FIFA, CAF sun jajantawa hukumar kwallon kafar kasar Ghana game da rasuwar matasan 'yan wasan kasar 8
2020-10-12 13:43:59 CRI
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, da takwararta ta nahiyar Afirka CAF, sun mika sakon ta'aziyya da jaje ga hukumar kwallon kafar kasar Ghana ko GFA a takaice, sakamakon rasuwar matasan 'yan wasan kwallon kafar kasar su 8, wadanda hadarin mota ya ritsa da su. Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, ya aike da wasika ga hukumar ta GFA, wadda a cikin ta ya karfafa gwiwar hukumar ta kasar Ghana, da ma iyalai da 'yan uwan mamatan, da wadanda suka jikkata sakamakon aukuwar hadari. Ya ce "Hukumar FIFA da al'ummun duniya gaba daya, na jajantawa GFA, da kwamitin samarin kasar, da iyalai da 'yan uwan mamatan, da wadanda suka jikkata baki daya. Muna fatan masu raunuka za su samu sauki cikin hanzari". Ita ma hukumar CAF, ta aike da makamanciyar wannan wasika mai dauke da sa hannun shugabanta Ahmad Ahmad, wadda ke cewa hukumar ta kadu matuka da irin wannan babbar asara da aka yi, ta matasan 'yan wasa na nahiyar. Ahmad Ahmad ya ce "Na kadu, kuma na yi matukar bakin cikin rasuwar wadannan 'yan kwallo matasa su 8, wadanda suka mutu a hadarin mota ran Asabar din karshen mako. Ina mika ta'aziyya ta, a madadin mambobin kwamitin zartaswar hukumar CAF, yana kuma fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka". Ahmad ya kara da cewa "Na san wannan rashi zai bakanta ran mu, ina kuma son ku san cewa, daukacin iyalin kwallon kafa na nahiyar Afirka na tare cikin wannan hali mai tayar da hankali". Ratohanni sun tabbatar da rasuwar 'yan wasan kasar ta Ghana dake bugawa kasar kwallo a ajin matasa, lokacin da motar da suke ciki ta kwacewa direban su, ta kuma fada cikin kogin Offin dake yankin Ashanti na kasar ta Ghana. Hukumar kwallon kafar Ghana GFA, ta fara zaman makokin 'yan wasan ta matasa su 8 da suka rasu sakamakon hadarin mota. Wata sanarwa da hukumar ta GFA ta fitar, ta bayyana matukar jimamin rasuwar 'yan wasan su 8 sakamakon hadarin mota. Ratohanni sun ce 'yan wasan kasar ta Ghana dake bugawa kasar kwallo a ajin matasa, sun rasu lokacin da motar da suke ciki ta kwacewa direban su, wanda hakan ya sanya motar fadawa kogin Offin dake yankin Ashanti na kasar ta Ghana.
Rahoton 'yan sanda ya nuna cewa, 'yan wasan dake cikin motar na tsakanin shekaru 12 zuwa 15 ne, suna kuma kan hanyar su ta komawa gida bayan gudanar da wani horo. Baya ga wadanda suka rasu, da yawa sun yi raunuka an kuma garzaya da su asibiti.