Harkokin wasanni na farfadowa sannu a hankali a kasar Sin
2020-10-12 13:39:44 CRI
Ga dukkanin alamu harkokin wasannin motsa jiki a kasar Sin na fardadowa sannu a hankali, yayin da dukkanin harkokin da ke da nasaba da hidimomin wasanni ke kara samun tagomashi. Hakan a ganin masu ruwa da tsaki a fannin, na da nasaba ne da halin da kasar ta Sin ke ciki game da yaki da cutar COVID-19, da ma tabbacin da aka samu game da tsaron lafiyar al'umma, yayin da rayuwar jama'ar kasar ke kara farfadowa. Kungiyoyin kwallon kafa ajin kwararru sun fara fafatawa A baya bayan nan, kungiyoyin kwallon kafa da masu sha'awar wasan a Sin, sun shiga wani yanayi na nishadi, duba da cewa, tuni aka fara buga wasannin ajin kwararru na kasar ta Sin ko CSL a takaice, bayan kusan rabin shekara da aka dakatar da su, saboda bullar cutar COVID-19. Duk da cewa an fara taka leda a lokacin zafi na bana a makare, a hannu guda 'yan kwallon kafa na cike da karsashi. Zagaye na farko, akwai kungiyoyi 16 a Dalian, da Suzhou da ake buga wasanni. Bayan wasanni 8, an ci kwallaye an kuma fafata wasanni, yanzu dai ana iya cewa, 'yan wasa da 'yan kallo suna cike da nishadi. Alkaluman CSL sun nuna cewa, yawan 'yan kallo da suka kalli wasan kungiyar Evergrande da Shanghai shenhua a birnin Guangzhou, da karawar Zall FC ta Wuhan da kungiyar Yellow Sea ta Qingdao FC, sun kai miliyan 30, a wasannin farko da kungiyoyin suka buga bayan bude gasar CSL. Masu sha'awar wasan kallo da dama dai na bayyana farin ciki da komowar wasanni, inda da yawa ke cewa, ganin kungiyoyin su na wasa ta kafar talabijin, na sa su jin cewa rayuwa ta fara komowa yadda aka saba. A matsayin hukumar dake shirya wasannin ajin kwararru a Sin, bude wasannin hukumar CSL muhimmin mataki ne na farfado da wasanni a cikin kasar. Bullar cutar COVID-19 ya sa an dakatar da wasanni a tsawon lokaci. Amma yanzu, sakamakon sake dawowa ayyukan yau da kullum, da ayyukan masana'antu, hukumar CSL, wadda ke jagorantar wasanni ajin kwararru a Sin, ta cimma nasarar sake bude gasanni, ta baiwa 'yan wasa, da masu horaswa, da sauran masu ruwa da tsaki a fannin komawa bakin ayyukan su, a gabar da kuma su ma 'yan wasa, suka kara farfado da fatan su, kana masu daukar nauyi, da sauran masu ba da gudummawa a fannin wasannin ke taka rawar gani a fannin dawo da wasanni. Masharhanta na cewa, sake bude wasanni cikin nasara a kasar Sin, ya shaida ikon kasar na tabbatar da nasarar dakile annoba. A nata bangaren, hukumar CSL ta tsara gudanar da wasannin kakar bana cikin nasara, ta hanyar tabbatar da aiwatar da matakan yaki da annoba, ciki hadda buga wasa ba 'yan kallo, da rufe wuraren da ka iya haifar da cunkoso, da gudanar da gwajin COVID-19 duk mako, da sauran matakan da za su rika daukewa kungiyoyin kwallon kafar kasar kewa. A ranar 26 ga watan Yulin shekarar nan ne, daruruwan 'yan kallo, ciki hadda jami'an lafiya, da malamai, suka shiga filin wasan Qingdao, bayan an tantance su, don kallon wasan da hukumar kwallon kwando ta CBA ta kasar Sin ta shirya. Yayin da ake ci gaba da buga wasanni, ana sa ran karin 'yan kallo za su sayi tikiti don kallon wasanni. Bisa tanajin da babbar hukumar shirya wasanni ta kasar Sin ta yi, dukkanin 'yan kallo da suke da sakamakon gwajin cutar COVID-19 na tsakanin sa'oi 48, kuma ba su yi cudanya da mutane ba, suna iya shiga kallon wasanni kai tsaye, kana za a rika ba da tazara tsakanin kujerun kwallon wasa, ta yadda yawan 'yan kallon ba za su haura kaso 50 bisa dari na daukacin 'yan kallo dale cikin filin wasan ba. A wannan yanayi ne kuma, ake sa ran sake jin amon shewar 'yan kallo a filayen wasa. Sake farfadowar wasanni na ingiza karsashin masu ruwa da tsaki a fannin Tuni aka fara buga wasannin kwallon kafa da kwallon kwando, da wasan kwallon raga na Volleyball, wadanda su ne wasanni 3 mafiya karbuwa a nan kasar Sin. A ranar 20 ga watan Agusta da ya gabata ne aka bude gasar kwallon Volleyball ajin Maza, wadda ake bugawa tare da 'yan kallo, da kuma wasu wasannin ba 'yan kallo. Ana farfado da karin wasanni masu tara 'yan wasa da yawa Yanzu haka ana kara farfado da karin wasanni masu tara 'yan wasa da yawa, wasannin da ke kara samun tagomashi matuka a nan kasar Sin. Sakamakon hakan ne ma babbar hukumar shirya wasanni ta kasar Sin ta fitar da wani tsarin aiki, mai kunshe da dabarun kimiyya, da kudurorin sake komowa wasanni, da sauran ayyukan dake yayata manufar komawa bakin aiki, da sarrafa hajoji masu nasaba da wasanni, an kuma dauki matakan fara bude harkokin wasanni a wuraren da suke da karancin matsaloli, ta yadda komai zai tafi yadda ake fata bisa tanadin da aka yi domin cimma nasarar hakan. Sakamakon wannan annoba, karin mutane sun fahimci muhimmancin aiwatar da harkokin wasanni tare da tsarin kula da lafiya. A farko farkon bullar wannan annoba, tsarin motsa jiki a gidaje ya zama muhimmiyar hanya da Sinawa ke bi wajen inganta kiwon lafiya, da kuma kyautata halin zukata. A yanzu kuwa, matakan kandagarki da shawo kan annoba, sun ba da damar budewa ga wurare, da cibiyoyin motsa jiki a dukkanin sassan kasar. Yanzu haka dai wasanni da masu sha'awar su, sun fara ban kwana da motsa jiki a gida, filayen wasanni yanzu haka sun fara cika da masu dariya da nishadi, da gumin masu motsa jiki. Domin bunkasa wasanni da agazawa kamfanonin dake taka rawar gani a fannin wasanni, ta yadda za su haye wahalhalu, kananan hukumomi sun bullo da manufofi da ka'idojin daidaita al'amura. Bayan dakushe wannan annoba a birnin Beijing, ana sa ran cibiyoyin wasanni kaso 50 bisa dari za su sake budewa. Domin cimma wannan nasara, mahukuntan birnin Beijing na tsara dabarun inganta harkokin motsa jiki ta hanyar shirya bukukuwan wasanni, ciki hadda na sayar da kayayyakin wasanni ta yanar gizo, masu kunshe da farashi mai rahusa, da wasannin yanar gizo na kyauta, da ayyukan yayata saye da sayarwar kayayyakin wasanni, da dawowa da karfin gwiwar masu sayayya. Yanzu haka dai birnin Tianjin ya kaddamar da wani shiri mai taken "Ka motsa jiki, na samar da rahusa "wanda ke da nufin ba da garabasa a harkokin motsa jiki, ta yadda masu sha'awar wasanni za su iya zuwa dakuna da cibiyoyin motsa jikin bisa farashi mai rahusa. A lokaci guda kuma, domin taimakawa kamfanonin kayan wasanni, ta yadda za su haye lokuta na wahalhalu, birnin Tianjin ya kuma tsara wani shiri, wanda zai baiwa cibiyoyin hada hadar kudi damar yin ido da ido da kamfanonin harkokin wasanni har 52. Kawo yanzu dai, irin wadannan kamfanoni 8 sun samu rance kudade daga cibiyoyin, wanda ya kai kudin Sin yuan miliyan 28.3, kudaden da za su yi amfani da su wajen rage masu radadin wahalhalu da suka fada sakamakon bullar cutar COVID-19. A daya bangaren shi ma birnin Chengdu, ya fitar da jadawalin gudanar da wasanni, mai kunshe da filayen wasanni na birane, da zaurukan motsa jiki, wadanda suka shafi wasanni 8, wato kwallon kafa, da kwallon kwando, da wasan raga na volleyball, da kwallon tebur, da badminton, da wasan tennis, da ninkaya da kwallon masu larurar ido wato "goalball", baya ga wasu wasannin rukunoni 49 da ake yi a jami'oi. An ce mazauna Chengdu na iya samun bayanai game da wurin gudanar da wasannin kai tsaye ta wayar salular su, don zabar wurin motsa jiki mafi kusa da su. Sauke nauyi dake wuyan dukkanin sassa ne hanyar dakile COVID-19 Bullar cutar COVID-19 ya jefa harkokin wasannin duniya cikin yanayi na mashasshara. Gasar Olympics ta birnin Tokyo da gasar kwallon kafa ta zakarun turai, dukkanin su an dage gudanar da su daga lokacin su na ainihi, kaza lika an soke wasanni kasa da kasa da dama da a baya aka shirya gudanarwa. To sai dai kuma a daya hannun, kwazon 'yan wasa daga dukkanin sassan duniya, na yayatawa, da komawa gudanar da wasanni cike da kwarin gwiwa bai ja baya ba. A fannin kwallon kafa, gasar Premier League, da Serie A, da La Liga da Bundesliga, duk sun kai matakin karshe na kakar su. A bangaren kwallon kwando ta hukumar NBA ma an kammala wasannin ta, cikin watan Agusta da ya gabata, bayan karkasa wasannin zuwa zango zango. Kasancewar sa bangare na gogewar da Sin ta samu a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, farfado da harkokin wasanni, da sake bude su a sassan kasar, ya kara karfafa gwiwar masu shiga wasannin na cikin gida, baya ga gudummawa da hakan ya bayar wajen yaki da annoba a fannin wasanni da hakan ya bayar a matakin kasa da kasa. Dan wasan kasar Belgium Fileni, wanda ke taka leda a kungiyar Shandong Luneng, ya ciwa kungiyar sa kwallaye 3 cikin mintuna 8 da take wasa, a wasan farko na bude gasar CSL na kakar bana. Masu sharhi a duniyar kwallon kafa, sun yi fashin baki game da kwazon dan wasa Fellaini, tun daga harbuwar sa da cutar COVID-19, zuwa ga farfadowar sa a cikin kasar Sin, zuwa komawar sa taka leda har ya kai ga cin kwallaye 3 a wasa daya. Yanzu haka dai ana ganin karsashin dawowar kwallon kafa, kuma fannin wannan wasa na kiyaye muhimmin bangare, wato kandagarki da taka tsantsan wajen tsaron lafiya. A baya, babbar hukumar wasanni ta Sin ta ba da umarni, bisa tushen cewa ba wata gasa ta kasa da kasa da za a gudanar bana a cikin kasar, in banda muhimman wasanni, kamar gwajin gasar Olympics ta binrin Beijing dake tafe a hunturun shekarar 2022. Bugu da kari, hukumomin ATP da WTA, sun shelanta soke dukkanin gasannin su a Sin na wannan shekara, ciki hadda gasar tennis ta "China Open", da "Shanghai Masters" da gasar karshen shekara ta "WTA" ta bana.
Da yake tsokaci game da hakan, shugaban hukumar ATP Andrea Gordentz, ya ce "Muna martaba hukuncin da kasar Sin ta yanke don gane da wasanni, bisa halin da aka shiga na bazuwar wannan annoba,". Ya ce wannan ce hanya mafi dacewa, ta bayyana matsayar da kasar ta dauka.