logo

HAUSA

Hadin gwiwa tsakanin Sin da ASEAN ya kara kyautata huldarsu

2020-10-12 20:01:38 CRI

Hadin gwiwa tsakanin Sin da ASEAN ya kara kyautata huldarsu

Tun bayan da manzon musamman na shugaban kasar Indonesia da ministan harkokin wajen kasar Philipines suka ziyarci kasar Sin, a jiya mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya tashi zuwa kasashen Cambodia da Malaysia da Laos da kuma Thailand domin gudanar da ziyarar aiki, kana zai yada zango a kasar Singapore. Wannan shi ne karo na farko da sassan biyu wato kasar Sin da kungiyar tarayyar kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN suka ingiza cudanyar diplomasiyya tsakaninsu, tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, kokarin da suke yi zai taimaka wajen farfadowar tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'ummar kasashen dake yankin, haka kuma zai kara inganta karfin ci gaba cikin lumana a shiyya shiyya da kuma fadin duniya ta hanyar aiwatar da manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban.

An lura cewa, bayan aukuwar annobar COVID-19, nan take kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN sun hada kai domin dakile annobar tare, sun kuma samu sakamako a bayyane. Baya ga tawagogin likitoci da kasar Sin ta tura kasashen Cambodia da Philipines da Myama da Laos da Malaysia da sauransu, ta kuma hanzarta samar da tallafi ga Philipines da Myama yayin da suka gina cibiyoyin tantance kwayar cutar COVID-19, a sa'i daya kuma, kasar Sin ta yi alkawari cewa, za ta yi la'akari da bukatun allurar rigakafi na kasashen ASEAN, tare kuma da kara samar da bayanan da abin ya shafa da kuma kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu wajen yin nazari, da amfani da allurar rigakafi, duk wadannan sun nuna cewa, kasar Sin da ASEAN suna gina kyakkyawar makomarsu tare. Kana yayin da suke kokarin hana yaduwar cutar, sassan biyu suna yin kokari tare domin farfado da tattalin arzikin kasashensu, alkaluman da aka samar sun nuna cewa, gaba daya adadin cinikayyar da sassan biyu suka yi tsakanin watan Janairu zuwa watan Agustan bana, ya kai dalar Amurka biliyan 416.55, adadin da ya karu da kaso 3.8 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, haka kuma kungiyar ASEAN ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ta kasar Sin a karo na farko a tarihi. Amma a 'yan watannin da suka gabata, Amurka ta rika tura jiragen ruwan yaki da jiragen saman yaki zuwa tekun kudancin kasar Sin, har ma wasu 'yan siyasar kasar suna neman shafawa kasar Sin bakin fenti bisa fakewa da batun tekun kudancin kasar, makarkashiyarsu ita ce lalata huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen mambobin kungiyar ASEAN. A kwanakin baya, wasu kafofin watsa labaran kasashen yamma, sun watsa wasu rahotanni, wai Cambodia ta zabi kasar Sin a maimakon Amurka, kan wannan batun, firayin ministan kasar Samdech Hun Sen ya mayar da martani da kakkausar murya cewa, "Idan kasar Sin ba ta taimakawa kasar Cambodia gina kayayyakin more rayuwar al'umma ba, to wace kasa ce za ta taimake ta, wasu ne kawai suke zargin wasu, duk da cewa, su ma suna jin dadin wadannan kayayyakin more rayuwa."

A fili yake cewa, kasashen ASEAN sun riga sun gano makarkashiyar wadannan 'yan siyasa ta lalata zaman lafiya a yankin, don haka burinsu ba zai cika ba.(Jamila)