logo

HAUSA

Kasar Sin tana kokarin kara taka rawarta a yaki da cutar COVID-19 a duniya

2020-10-11 20:03:38 CRI

Kasar Sin tana kokarin kara taka rawarta a yaki da cutar COVID-19 a duniya

A ranar 8 ga watan Oktoba, kasar Sin ta sanya hannu kan yarjejeniya tare da gamayyar hadin gwiwar kasa da kasa don samar da alluran rigakafi da ba da kariya, wato GAVI a takaice, inda ta shiga cikin "shirin gudanarwa na alluran rigakafin cutar COVID-19". Wannan wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka don tabbatar da manufar kafa al'umma ta bai daya a fannin kiwon lafiyar dan Adam a duniya, da kuma cika alkawarinta na inganta alluran rigakafin a matsayin kayan amfanin jama'ar duniya baki daya. Hakan kuma zata ba da gudummawarta wajen hadin kan duniya a yaki da annobar tare da kare rayuka da lafiyar mutane a duk duniya. A halin yanzu, annobar numfashi ta COVID-19 na ci gaba da yaduwa a duniya, kuma alluran rigakafi suna da mahimmiyar rawa ga cimma nasarar yaki da annobar. Domin inganta alluran rigakafi don taimakawa bil Adama wajen kawo karshen cutar tun da wuri, kasar Sin tana kara yin kokari ba tare da jinkiri ba a fannonin nazari, da samarwa, da rarrabawa da kuma inganta hadin gwiwar kasa da kasa kan alluran rigakafin. Tabbatar da cewa kasashe masu tasowa suna iya samun damammaki iri daya na samun alluran rigakafi mai dacewa, da inganci da kuma amfani, shi ne muhimmin batu da kasar Sin ke mayar da hankali a kai a ko da yaushe. Kasar Sin ta sha yin alkawalin cewa, bayan ta kammala ayyukan nazari da amfani da alluran rigakafin cutar COVID-19, to alluran rigakafin za su zama kayayyakin amfanin jama'a na duniya baki daya, kasar za ta taka rawarta don ganin an samu wadatar alluran a kasashe masu tasowa. Hakan na nuna aniyar kasar da ra'ayinta na hada kai tare da kasashen duniya wajen yakar annobar. Yanzu dai, alluran rigakafi da yawa da kasar Sin ke nazari suna matsayin gaba a duniya, kuma kasar na cike da isasshen karfin samarwa. Bisa wannan halin da ake ciki, kasar Sin ta tsaida kudurin shiga cikin wannan "Shirin gudanarwa" ne da nufin inganta rarraba alluran rigakafi cikin adalci da tabbatar da samar da alluran rigakafin ga kasashe masu tasowa, matakin da ya nuna matsayinta na wata babbar kasar dake daukar nauyin dake bisa wuyanta.

Kasar Sin tana kokarin kara taka rawarta a yaki da cutar COVID-19 a duniya

Yaki da cutar COVID-19, aikin bai daya ne na duk duniya, idan akwai wata kasa da ba ta shawo kan cutar ba, to da wuya duniya ta zauna lafiya. Amma, har yanzu wasu 'yan siyasar Amurka suna namijin kokari don siyasantar da alluran rigakafi, da kin samar da alluran rigakafi ga mutane a matsayinsu na kayayyakin jama'a, wadanda suka illata ayyukan yaki da annobar a duniya. Hukumar lafiya ta duniya ta taba bayyana cewa, yanzu wani ra'ayin samar da allurar rigakafi domin bukatun kashin kai na wasu kasashe ya soma bullowa a duniya, kuma akwai yiwuwar kara farashin alluran rigakafin, sai dai kasashen duniya su karfafa hadin gwiwa za a iya magance matsalar samar da alluran.

A karkashin irin wannan yanayi, kasar Sin ta dauki matakin shiga cikin "shirin aiwatarwa", hakan zai haifar da karin kwarin gwiwa ga gamayyar kasa da kasa don tsayawa kan ra'ayin bangarori da dama, da inganta hadin kai wajen yaki da annobar, da kuma nuna adawa da ra'ayin samar da alluran rigakafi domin bukatun kashin kai na wasu kasashe kawai. Mun yi imanin cewa, ta hanyar hadin gwiwar kasar Sin da sauran wasu bangarorin da ke cikin "shirin aiwatarwa", tabbas ne 'yan Adam za su shawo kan annobar tun da wuri, kuma za a samu makoma mai kyau a nan gaba. (Bilkisu Xin)