logo

HAUSA

Lokacin hutu na bikin kasar Sin ya shaida karfin tattalin arzikin kasar

2020-10-09 20:49:58 CRI

Lokacin hutu na bikin kasar Sin ya shaida karfin tattalin arzikin kasar

 

Kullum lokacin hutu na bikin kafa kasa yana kasancewa taga, ta kallon yadda tattalin arzikin kasar yake. Yanzu ga jerin alkaluman da aka samu kan wannan dogon lokacin hutu na kwanaki 8 a bana, wadanda suka bayyana sha'awar Sinawa wajen sayayya: A tsakanin ranar 1 zuwa 8 ga wata, yawan kudin da manyan kamfanoni da aka sanya wa ido a kasar ya kai kimanin yuan tiriliyan 1.6, kuma yawan Sinawa masu bude ido dake yawon shakatawa a cikin kasar ya kai sau miliyan 637, kana yawan kudin da aka samu sakamakon yawon shakatawa a cikin gida ya kai kimanin biliyan 466.56, kuma jimilar kudin da aka samu sakamakon fina-finai a duk kasar ya kai kudin Sin yuan biliyan 3.952, kana yawan mutanen da suka kalli fina-finai ya kai kusan miliyan 100……Kamar yadda jaridar NewYork Times ta ce, yadda tattalin arzikin kasar Sin yake a lokacin hutu na bikin kasar ta Sin, "alama ce mafi bayyana cewa, Sin ta warke daga annobar COVID-19 a yanzu haka". A halin yanzu, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin yana sauyawa daga dogaro sosai kan zuba jari, da fitar da kayayyaki, zuwa kasashen waje, zuwa dogaro kan bukatun cikin gida. Karuwar sayayya ta Sinawa na kara bunkasuwa, musamman ci gaban tattalin arziki na yanar gizo wanda ya gaggauta wannan yunkurin, tare da ba da muhimmin tallafi ga farfadowar tattalin arzikin kasar.  

Lokacin hutu na bikin kasar Sin ya shaida karfin tattalin arzikin kasar

 

Tattalin arzikin duniya na yanzu, yana komawa baya sakamakon yaduwar annobar COVID-19,kuma ko shakka babu saurin farfadowar kasa mafi girma ta biyu a duniya, na taimakawa farfadowar tattalin arzikin duniya. Misali, kayayyakin cinikayya masu inganci da yawa da kasar Sin ke shigowa, zai kawo damar ci gaba ga kamfanoni na sauran kasashe.

Bisa hasashen da wasu hukumomin kasa da kasa, ciki har da Asusun Ba da Lamuni na Duniya da Bankin Duniya suka yi, ana sa ran kasar Sin za ta kasance babbar kasa daya tilo da za ta samu ci gaban tattalin arziki a bana. Bisa yanayin tattalin arzikin duniya mai cike da damuwa, tabbas ne kasar Sin za ta kara kwarin gwiwa ga duniya. (Mai fassara: Bilkisu)