logo

HAUSA

Bai dace kasashen da "suka gaza" su zamo malaman kare hakkin bil Adama ba

2020-10-08 20:06:18 CRI

Bai dace kasashen da "suka gaza" su zamo malaman kare hakkin bil Adama ba

 

A baya bayan nan, mahukuntan kasar Sin, sun yi watsi da karairayin da wasu kasashen yamma ke ci gaba da yadawa, game da batun kare hakkin bil Adama a jihar Xinjiang da yankin Hong Kong. Hakan na zuwa ne, a gabar da kasar ta Sin ke sake jaddada matsayin ta, na kin amincewa wata kasa daban, ta zame mata mai ba da umarni game da kare hakkin bil Adama, musamman ma kasashen da su kan su, ba sa iya tabuka wani abun azo a gani game da kare hakkin kananan kabilu, ko rukumomin al'ummun da ba su da rinjaye. A baya bayan nan, Amurka da kawayen ta, na kan gaba wajen zargin kasar Sin da tauye hakkokin bil Adama a Xinjiang da yankin Hong Kong, duk kuwa da cewa ita kan ta Amurkan na fama da alhakin rashin kyautata tsarin kare rayuka, da hakkokin sassan mutane marasa rinjaye dake kasar. Ko a Alhamis din nan, rahotanni sun tabbatar da cewa, kotu ta bayar da belin korarren dan sanda farar fatan nan mai suna Derek Chauvin, wanda a watan Mayu, lokacin yana aikin dan sanda a Minneapolis, ya shake wani matashi bakar fata mai suna George Floyd da gwiwar kafar sa, lamarin da ya kai ga rasuwar Floyd.

Bai dace kasashen da "suka gaza" su zamo malaman kare hakkin bil Adama ba

 

Masharhanta da dama na kallon irin wadannan matakai, a matsayin gazawa da rashin ingancin tsarin kare rayukan al'umma a Amurka, duba da yadda ta kasa magance matsaloli masu nasaba da bakin haure, da harkokin jin kai, da na nuna wariyar launin fata. Amma duk da haka, mahukuntan ta, na kawar da kai daga halin da kasar su ke ciki, inda suke mayar da hankali ga sauran kasashe, suna furta kalamai masu hadari, wadanda ba za su haifar da komai ba sai raba kawunan al'umma, da kokarin shafawa wasu kasashe kashin kaji.

Abun tambaya ma a nan shi ne, shin ta yaya irin wadannan kasashe za su zamo masu rajin kare hakkin bil Adama, bayan mummunan tarihi da suka kafa na gazawa a fannin?

Ko shakka ba bu, abu mafi dacewa shi ne Amurka da kawayen ta, su maida hankali ga kashe wutar dake gaban su, su rungumi zaman lafiya da lumana a fannin siyasa da tattalin arziki, tare da kauracewa shiga sharo ba shanu, game da harkokin cikin gidan sauran kasashen duniya, wanda hakan ne kadai zai baiwa kasar damar cimma kudurorin ciyar da al'ummun ta gaba yadda ya kamata. (Saminu)