logo

HAUSA

Yadda jihar Xinjiang take samun ci gaba

2020-10-08 14:31:07 CRI

Sanin kowa cewa, jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta, wani bangare ne na kasar Sin mai kunshe da kabilu daban-daban dake zaune cikin zaman lafiya da jituwa. Amma saboda rashin sani ko adawa ko jahiltar abubuwan dake faruwa saboda ba su taba zuwa yankin ba, suke yada jita-jita da ma karairayi game da yankin.

Don haka, bai kamata a rika fadin abin da ba su da masani akai, don kawai neman biyan bukatunsu na siyasa

Haka kuma, saboda wata manufa ta neman biyan bukata, a baya ma har gwamnatin kasar Amurka da magoya bayanta, su ka sanya hannu kan shirin dokar kare hakkin dan Adam ta Uygur na shekara ta 2020, inda ta shafa wa kasar Sin bakin fenti kan yanayin kare hakkin dan Adam da jihar Xinjiang ta kasar Sin ke ciki, da kuma manufofinta na tafiyar da harkokin jihar, lamarin da ya sanya al'ummar Sinawa da ma al'ummar kabilu daban daban na jihar kimanin miliyan 25 yin Allah wadai da nuna adawa da wannan mataki, haka ma al'ummar kasashen duniya masu nuna gaskiya da adalci sun soki matakin na Amurka.

Duk mai bibiyar abubuwan dake faruwa a jihar Xinjiang, ya san cewa, bisa managartan matakan da aka dade ana dauka a jihar, kan yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi a 'yan shekarun da suka gabata, ya sanya jihar ta shiga cikin sabon zamani na samun wadata da ci gaba. (Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)