logo

HAUSA

Hutun Tsakiyar Kaka ya haska nasarar kasar Sin ta yaki da COVID-19

2020-10-06 20:09:08 CRI

Yaki da cutar COVID-19 abu ne da ake ci gaba da yi a sassan duniya, kimanin watanni sama da 10 bayan sanar da bullar cutar karo na farko a hukumance. Sai dai labarin ya sha bamban a kasar Sin, ganin cewa, ta yi nasarar yakar cutar, wanda abu ne da yake a bayyane da kowa zai iya gani. A baya, ana ganin kamar kasar Sin na boye adadin wadanda suke kamuwa da cutar domin nuna cewa ta samu shawo kanta. Abun ba haka yake ba, saboda a zahiri kasar Sin ta samu gagarumar nasara a wannan fannin, duba da irin yadda al'ummarta suke gudanar da harkokinsu yayin hutun bikin kafuwar kasa da kuma na tsakiyar kaka na kalandar gargajiya ta kasar.  

Hutun Tsakiyar Kaka ya haska nasarar kasar Sin ta yaki da COVID-19

 

Ma'aikatar al'adu da kula da yawon bude idon ta kasar Sin, ta yi hasashen tafiye-tafiyen da za a yi a cikin kasar yayin hutun na bana, za su kai miliyan 550, yayin da kamfanin shirya tafiye-tafiye na C-trip na kasar Sin ya yi kiyasin tafiye-tafiye sama da miliyan 600. A bara, yawan tafiye-tafiyen da aka yi a makamancin lokacin, ya kai miliyan 782. Wato adadin na bana ya kai sama da kaso 70 na bara, ke nan bambanci kalilan aka samu a yawan tafiye-tafiyen da aka yi a bara lokacin da ba a samu barkewar cutar ba, da kuma bana da ake fama da ita, lamarin da ya zama shaida ga nasarar da kasar Sin ta samu wajen fatattakar cutar.

Kusan za a iya cewa nasarar ta zama abun mamaki, la'akari da cewa, irin wannan tafiye-tafiye a lokaci guda, abun ne da ba za a samu a galibin kasashen duniya ba, saboda yadda ake ta fafutukar ganin an shawo kan cutar COVID-19. Cikin karshen makon da ya gabata, yawan masu cutar a Amurka ya haura miliyan 7, yayin da galibin kasashen Turai ke fama da sake barkewar annobar. Ana iya cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu a kasar Sin. Domin managartan matakan da ta dauka, sun yi rawar gani wajen kai ta ga matakin da take a yanzu. Kasashen dake fafutuka da cutar yanzu haka, sun sha sukar kasar Sin dangane da tsauraran matakan da ta dauka na dakile cutar a waccan lokaci, sai dai a yanzu, ana amfana daga wadancan matakai. Wato sahihanci da kuma kwazon kasar ne ke kaita ga irin nasarorin da take samu. Abun takaici shi ne, maimakon sauran kasashe su nazarce ta don su yi koyi da ita, sai suke kokarin shafa mata bakin fenti ta hanyar suka da zarge-zarge marasa kan gado.  

Hutun Tsakiyar Kaka ya haska nasarar kasar Sin ta yaki da COVID-19

 

Bisa dukkan alamu, yaki da cutar COVID-19 ba shi ne abun da kasar Sin ta mayar da hankali kai a yanzu ba, domin tuni ta kammala da wannan babi inda ta nufi mataki na gaba wato, farfado da harkokin zamantakewa da na tattalin arziki da kare lafiyar al'umma. Duk da haka, wannan bai sa ta saukaka matakanta na kandagarki ba. Duk da nasarorin da ta samu, har yanzu ana tabbatar da kiyaye hanyoyin dakile cutar da samar da dabarun tunkararta idan bukata ta taso. An ce rigakafi ya fi magani! Yayin da ake tururuwar zuwa hutu da yawon shakatawa yayin hutun bikin na kasa da ya kasance mafi girma baya hutun bikin bazara da ya zo a lokacin da cutar ke ganiyar yaduwa, an dauki matakan ganin jama'a ba su shiga cikin hadarin kamuwa da cutar ba. Yayin da ake wannan hutu, dukkan sassa dake wurare daban-daban na kasar, sun kara daukar matakan kandagarki da hana yaduwar annobar COVID-19, inda aka tsaurara matakan tsaro a fannin sufuri, da hidimomi a wuraren cin abinci da yawon shakatawa da sauransu, don tabbatar da cewa, masu yawon shakatawa sun ji dadin ziyara.

Lallai kasar ta zama uwar da ta amsa sunanta wajen kula da 'ya'yanta. Yayin da ta ba su damar tafiye-tafiye da yawon bude ido a wannan lokaci, ta kuma dauki tsauraran matakai na ganin ba su shiga cikin hadari ba, duk da cewa tana sane ta shawo kan cutar, ba ta son barin wata kafa da za a sake komawa halin da aka shiga a baya. Matakin nata ya zama mai bada kwarin gwiwa ainun. Ko kafafen watsa labaran kasashen ketare da dama ma, sun yaba mata, inda suke ganin lallai yanayin na wannan hutu, ya bada tabbaci ga ikirarin kasar na fatattakar cutar. (Faeza Mustapha)