Bello Nasiru Abdullahi: Allah ya kara daukaka Najeriya da Sin
2020-10-06 14:35:18 CRI
Bello Nasiru Abdullahi, wani dalibi dan jihar Kano ne wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a fannin kimiyyar tattalin arzikin gona a jami'ar koyon ilimin aikin gona ta lardin Gansu na kasar Sin. A zantawarsa da Murtala Zhang, ya ce, duk da cewa bai dade da fara karatu da zama a kasar Sin ba, yadda mutanen Sin suke karbar baki da nuna musu karamci ya burge shi kwarai da gaske. Haka kuma ya kwatanta bambancin ayyukan noma a kasarsa Najeriya da kuma kasar Sin.
Haka kuma, ranar 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 60 da Najeriya ta samu 'yancin kai, yayin da ake cika shekaru 71 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, wato People's Republic of China a turance. Bello Nasiru Abdullahi ya yi wa kasashen biyu gami da jama'arsu fatan alheri.(Murtala Zhang)