logo

HAUSA

Kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha da kasar Sin ke yi ya inganta jin dadin dan Adam baki daya

2020-10-05 20:52:40 CRI

Kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha da kasar Sin ke yi ya inganta jin dadin dan Adam baki daya

 

"Mu muka fara wallafa bayanan gwajin asibiti a duniya, awoyi biyar gabanin kasar Amurka. Kuma mun wallafa bayanan gwaji na II a cikin mujallar Lancet a ranar 22 da 24 ga watan Yuli, ku san shi ne mafi sauri a duniya." A kwnakin baya ne Chen Wei, masaniyar kimiyya ta kasar Sin ta fito fili ta bayyana yayin gabatar da yadda ake samun ci gaban nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19. Kan wannan annobar da ta bullo ba zato ba tsamani, an sake gwada kwarewar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ta kasar Sin, wadda ta nuna ci gaban da kasar ta samu a fannin kimiyya da fasaha a lokacin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13. Jama'a sun gano cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta samu manyan nasarori a fannin: karon farko da na'urar bincike ta sauka a bayan wata, kuma layin dogo mai saurin tafiya na zamani na farko ya soma aiki, an kuma kaddamar da babban madubin hangen nesa na zamani mafi girma a duniya mai suna "Sky Eye", kana babban jirgin ruwan jaki da jiragen saman yaki ke sauka a kansa kirar kasar Sin ya soma tafiya a cikin ruwa, kuma tsarin jagorancin zirga-zirga ta hanyar tauraron dan Adam mai suna "Beidou" ya kammala aikin kafa tsarin sadarwa na duniya ... Ana iya cewa, karfin kimiyya da fasaha na kasar Sin yana kara inganta cikin sauri, kuma sannu a hankali kasar tana kan gaba a fannin kirkire-kirkire a duniya.  

Kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha da kasar Sin ke yi ya inganta jin dadin dan Adam baki daya

 

Dalilin da ya sa kasar Sin ta samu nasarori masu kayatarwa wajen kirkire kirkire a fannin kimiyya da fasaha shi ne, da farko shugabannin kasar Sin sun dage wajen daukar kirkire-kirkire a matsayin matakin farko na samun ci gaba, haka kuma kasar tana kara zuba jari a fannin aikin nazari da ci gaba, da kuma kyautata yanayin fannin. Ban da wannan kuma, yadda masanan kimiyya da fasaha suke nuna kishin kasa, kirkire-kirkire, nuna gaskiya, sadaukarwa, hadin kai, da ilimantar da mutane, shi ma ya zama muhimmin karfi na inganta ci gaban kimiyya da fasaha na kasar Sin.

Kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da kasar Sin ke yi ya kara karfin ingiza samu ci gaba mai inganci. Haka zalika, a yayin da kasar ke kokarin inganta karfinta na yin kirkire-kirkire da kanta, a sa'i daya kuma tana sa himma wajen shiga ayyukan yin kirkire-kirkire na duniya, da inganta mu'amala da hadin kai tsakanin kasa da kasa, ta yadda nasarorin da aka samu a fannin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na iya amfanar kasashe da mutane da dama. (Mai fassara: Bilkisu)