logo

HAUSA

Fa'iza Mustapha: Ina jinjinawa yadda al'ummar Sin ke taimakawa gwamnatin Sin wajen yaki da talauci

2020-10-05 15:04:12 CRI

A cikin shirinmu na makon jiya, mun gabatar muku da wata hirar da ke tsakanin Kande Gao da Fa'iza Mustapha kan yadda suka ziyarci lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin domin gano wata fasahar gargajiyar kasar Sin mai tarihin fiye da shekaru 1400, wato fasahar amfani da kakin zuma wajen zane-zane a kan yadi sa'an nan a rina shi, wadda mata 'yan kabilar Miao ke rike da ita kuma sun yi amfani da ita wajen samun abin dogoro da kai. A cikin shirinmu na yau, mu ci gaba da hirar.