logo

HAUSA

Kamfanonin Sin sun taka rawar gani a shirin yaki da fatarar kasar

2020-10-05 16:26:24 CRI

Kamfanonin Sin sun taka rawar gani a shirin yaki da fatarar kasar

Masu hikimar magana na cewa "daga na gaba ake gane zurfin ruwa". Kuma a wani kaulin "barewa ba za ta yi gudu dan ya yi sassarfa ba". Manufar gwamnatin Sin na kokarin kawar da talauci da samar da guraben ayyukan dogaro da kai kana da kyautata zaman rayuwar al'ummar Sinawa da nufin samar da wata al'umma mai matsakaiciyar wadata yana samun tagomashi da goyon baya daga dukkan fannonin kasar. Sama da kamfanonin Sin 100,000 suka taimakawa shirin kawar da talauci da mahukuntan kasar ke cigaba da kokarin aiwatarwa.

Ya zuwa watan Yunin bana, kimanin kamfanoni masu zaman kansu 109,500 ne suka shiga ayyukan shirin yaki da fatara a kauyukan da suka fi fama da talauci a kasar Sin, babban jami'in hukumar kula da dukkan kamfanoni da masana'antun kasar Sin ACFIC, ya bayyana hakan. Wadannan kamfanonin masu zaman kansu sun taimakawa kauyuka kimanin 127,100, wanda ya kunshi kauyuka 68,900 da aka yiwa rejista a matsayin wadanda suka fi fama da talauci, Fan Youshan, mataimakin shugaban hukumar ACFIC, ya bayyana hakan a yayin wani muhimmin taro da aka gudanar a kwanakin baya a shiyyar kudu maso yammacin lardin Guizhou na kasar.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, wadannan kamfanoni masu zaman kansu sun samar da kusan kudin Sin Yuan biliyan 91.6 kwatankwacin dala biliyan 13.4 na jarin kamfanoni da aka zuba a yankunan da suke fama da talauci a shekarun da suka gabata, inda aka samu karin Yuan biliyan 15.2 na ayyukan kyautata walwalar jama'a. Kamfanonin sun taimaka wajen samar da guraben ayyukan yi 799,000, kana sun horar da mutane 1.16, sannan yawan mutane masu fama da talaucin da suka yi rejista ya kai miliyan 15.64. Hukumar ta ACFIC za ta jagoranci kamfanoni masu zaman kansu domin samar da karin kudade wanda zai amfani kauyuka sama da 1,100 da har yanzu ba su fita daga kangin fatara ba, don taimakawa shirin gwamnatin kasar Sin na yaki da talauci.

Ko shakka babu, wannan wani labari ne mai faranta rai duba da yadda kamfanonin kasar ke tallafawa dukkan manufofin gwamnatin Sin a kokarinta na kyautata zaman rayuwar al'ummar kasar. 'Yan magana na cewa "gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah" da fatan kamfanonin kasashen masu tasowa musamman na Afrika za su dauki izini daga takwarorinsu na kasar Sin. (Ahmad Fagam)