logo

HAUSA

Shin ko yawancin jama'ar Amurka suna rayuwa cikin nishadi saboda suna rayuwa a kasa mafi girma a duniya?

2020-10-04 14:57:51 CRI

Shin ko yawancin jama'ar Amurka suna rayuwa cikin nishadi saboda suna rayuwa a kasa mafi girma a duniya?

Mene ne matsayin kasar Amurka a duniya? Game da wannan batu, babu shakka ana iya cewa Amurka kasa ce mafi girma da wadata a duniya, to ko jama'arta suna da wadata iri daya? Bari mu ga gaskiyar abin da ke faruwa a cikin al'ummar Amurka. Mai ba da rahoto kan tsananin talauci da hakkin bil Adama Philip Alston ya rubuta wani rahoto a watan Mayu na shekarar 2018 dangane da ziyarar da ya kai Amurka, inda ya nuna cewa, Amurka ta zama kasa mafi fama da matsalar gibi tsakanin masu kudi da talakawa a kasashen yamma, a cewarsa kimanin Amurkawa miliyan 40 suna cikin kangin talauci, daga cikinsu miliyan 18.5 na fama da talauci mafi tsanani, inda miliyan 5 suke rayuwa kamar wadanda ke zaune a matalautan kasashe masu tasowa. Tun bullar cutar COVID-19 a shekarar 2020, gwamnatin Amurka ta gaza daukar matakan da suka dace, abin da ya tsananta halin da kasar ke ciki a halin yanzu, abin da ya kara gibin dake tsakanin masu kudi da talakawa, har ya jefa wasu Amurkawa ciki matukar mawuyancin hali.

Shaida ta farko: Kudin shiga tsakanin masu kudi da talakawa ya bambanta matuka. Cibiyar nazari ta Pew dake Amurka ta fitar da alkaluma a ran 12 ga watan Yuni na shekarar 2018 cewa, tun shekarun 1970, ginbin dake tsakanin masu kudi da talakawa ke karawu. Hukumar kasuwancin kasar Amurka ta fitar da kididdiga cewa, a watan Mayu na 2019, ma'aunin alkaluman ci gaban kasar ya kai 0.482 wanda ya haura ma'aunin duniya wato 0.4. Ban da wannan kuma, kudin shiga na talakawa da yawansu ya kai 50% na al'ummar Amurkawa a shekarar 2014 ya yi daidai da na shekarar 1980 wato bai karu ba ko kadan, amma a wani bangare kuma, masu kudi da yawansu ya kai 1% na al'ummar ya ninka sau 3. Hukumar kidayar jama'a ta Amurka ta ba da kididdiga cewa, yawan matalauta ya kai miliyan 38.1 da,kimanin kashi 11.8% na al'ummar Amurkawa. Shaida ta biyu: Yawan gibin dake tsakanin wadannan mutane ya haifar da karuwar matsalolin da suke shafar kare hakkin bil-Adama a kasar. Kimanin rabin iyalan Amurka ba su iya rayuwa yadda ya kamata. Jaridar "USA TODAY" ta Amurka ta ba da labari a ran 19 ga watan Disamba na shekarar 2018 cewa, yawan kudin shigar mutane fiye da miliyan 5 bai kai dala dubu 15 ba, mizanin talauci. Abin da ya sa wadannan mutane suke rayuwa cikin halin rashin tabbas balle samun jiyya mai kyau, inda wasu ma ke kwana a kan tituna. Yara da suke fama da talauci ba su iya shiga makaranta, kuma mata masu yara da basu da mazaje suna cikin mawuyancin hali. Shaida ta uku: Da wuya a magance wadannan dalilan da suka haifar da wannan gibi. Saboda manufofin gwamnatin Amurka a fannin tattalin arziki da al'umma da kuma al'adu, sun yi biris da hakkin jama'a. Alal misali, yin takara maras iyaka a kasuwar hada-hadar kudade ta rage guraben aikin yi, kana wadanda ba su samun kudi shiga sosai, suna fama da matsalar wurin kwana saboda karuwar farashin gidaje a mataki-mataki. Kana jama'a ba sa samun jiyyar da ta dace, saboda kudin jiyya mai tsada. Haka kuma masu karancin kudin shiga ba su iya shiga makaranta saboda karuwar kudin makaranta. Ban da wannan kuma, gwamnatin Amurka ba ta da niyyar canja wannan halin da ake ciki, saboda ta hankalinta ya karkata ne kawai wajen kare hakkin masu kudi kawai. Sannan ta yi watsi da da yiwa tsarin inshorar jiyya gyaran fuska. Amurka tana daya daga cikin wasu kasashe da ba su samarwa dukkan jama'arta inshorar jiyya. An iya cewa, gwamnatin Amurka, tana kare muradun masu kudi ne kawai.

Babu shakka Amurka kasa ce mafi girma da wadata a duniya, amma shin ko yawancin jama'arta suna rayuwa cikin nishadi? (Amina Xu)