logo

HAUSA

Tattaunawarmu da Malam Ibrahim Aliyu a kan bikin Zhongqiu na Sinawa

2020-10-02 20:20:47 CRI



Bikin Zhongqiu na daya daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na Sinawa, wanda a kan yi shi a ranar 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiya na kasar Sin, wato ya fado a daidai tsakiyar yanayin kaka, shi ya sa ake kiranta bikin Zhongqiu, wato bikin tsakiyar yanayin kaka. Kuma a wannan shekara, ya fado daidai a jiya ranar 1 ga wata. A wannan rana, wata ya kan cika da'ira da kuma haske, kuma a lokacin da jama'a ke hango duniyar wata, su kan fara kewan iyalansu, shi ya sa Sinawa suna kuma daukar bikin a matsayin bikin haduwar iyali. Don haka, a yayin bikin, Sinawa a duk inda suke, in suna da dama su kan koma gida don haduwa da iyalai.

A yau muna tare da malam Ibrahim Aliyu da ya shafe wasu shekaru yana dalibta a nan kasar Sin, don ya shiga tattaunawarmu dangane da bikin. Sai a biyo mu cikin shirin, don jin karin haske.