logo

HAUSA

Al'ummun Sin da na tarayyar Najeriya na yiwa kasashen su kyakkyawan fatan kara samun ci gaba

2020-10-01 21:36:19 CRI

Al'ummun Sin da na tarayyar Najeriya na yiwa kasashen su kyakkyawan fatan kara samun ci gaba

A yau daya ga watan Oktoba ne al'ummun kasar Sin ke murnar cika shekaru 71 da kafuwar Jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ranar da ta yi daidai da ranar murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Al'ummun Sin da na tarayyar Najeriya na yiwa kasashen su kyakkyawan fatan kara samun ci gaba

A wannan gaba, shugabanni da al'ummun kasashen biyu, sun gudanar da bukukuwa na taya juna murnar wadannan muhimman raneku, wadanda ke tunasar da su irin gwagwarmayar da kasashen su suka sha, kafin kai wa ga inda suke a yanzu.

A bangaren kasar Sin, wannan lokaci ne na waiwaye adon tafiya, game da irin sadaukarwar da jagororin kasar na baya suka yi, wajen shatawa kasar kyakkyawar taswirar ci gaba, wadda a kan ta ne kasar ta kai ga samun babbar bunkasuwa cikin shekaru kalilan. A hannu guda kuma al'ummar Sinawa na amfani da wannan dama wajen jinjinawa 'yan mazan jiya, wadanda suka ba da gudummawa a fannonin raya kasa har kasar ta kai matsayin da take a halin yanzu. Wannan lokaci ya kasance na sake jaddada aniyar kishin kasa, da ci gaba da aiki bisa himma da kwazo, da zage damtse wajen habaka cudanyar kasa da kasa, ta yadda za a kai ga kafa duniya mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adama. Wadannan kudurori ne da ko shakka ba bu kasar Sin ke baiwa matukar muhimmanci.

Al'ummun Sin da na tarayyar Najeriya na yiwa kasashen su kyakkyawan fatan kara samun ci gaba

Masharhanta da dama na fatan ci gaban da kasar Sin ta samu a wadannan shekaru 71, za su dore zuwa matakai masu yawa a nan gaba, duba da tasirin da ci gaban kasar ke yi ga bunkasar tattalin arziki da zamantakewar duniya baki daya.

A bangaren Najeriya kuwa, baya ga cikar kasar shekaru 60 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka, al'ummar kasar na kallon shafe shekaru 21 da komawa mulkin dimokaradiyya bayan sojoji sun mulki kasar tsawon shekaru, a matsayin daya daga muhimman nasarori da kasar ta samu a baya baya nan. Ko da yake ana lasafta matsalolin cin hanci da rashawa, da rashin dorewar manufofin gwamnati a wasu fannoni, da tsadar rayuwa, da karyewar darajar man fetur a baya bayan, a matsayin matsaloli da ke addabar kasar, har wannan gaba da ake bikin cikar ta shekaru 60 da kasuwa, a hannu guda wasu 'yan kasar na bayyana kyakkyawan fatan su game da samun ci gaba mai armashi a shekaru masu zuwa.

Al'ummun Sin da na tarayyar Najeriya na yiwa kasashen su kyakkyawan fatan kara samun ci gaba

'Yan Najeriya na fatan ganin karin sauye sauye a fannoni da dama, ciki hadda fadada hanyoyin samun kudaden shigar kasar, baya ga wadanda ake samu daga cinikayyar albarkatun mai. Kaza lika suna fatan ganin mahukunta sun kara azama wajen inganta tsaro, da bunkasa noma, da kara kyautata tsarin kiwon lafiya, da ilimi da dai sauran su.

A karshe, ga duk wanda ke bibiyar matsayi, da yanayin alakar Sin da Najeriya, ya san cewa, kamar yadda suka yi tarayya wajen gudanar da wadannan bukukuwa muhimmai a rana guda, kasashen na kuma da kyakkyawar dangantakar abota mai armashi, wandda ke ba su damar cin gajiya daga juna. Fatan shi ne kasashen biyu, za su ci gaba da daga matsayin dangantakar su, ta yadda hakan zai fadada gajiyar da al'ummun su ke samu.

Kaza akwai fatan dangantakar Sin da Najeriya za ta kara yaukaka zumunta dake wanzuwa tsakanin su. Wato Sin a matsayin ta na babbar kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Asiya, da Najeriya dake ke matsayin Giwar nahiyar Afirka, ta yadda hakan zai zamo kyakkyawan misali na kawance tsakanin kasashe masu tasowa a duniya.(Saminu Alhassan)