logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD: Sabon tsarin raya kasar Sin zai samar da dama ga duniya

2020-09-30 12:00:27 cri


Tun farkon shekarar bana, sau da dama shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada a wurare daban daban cewa, ya dace a yi kokarin kafa sabon tsarin raya kasa, inda za a kara karfafa cudanyar tattalin arziki a cikin kasar, tare kuma da kara karfafa cudanyar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya.

Kwanan baya wakilin kasar Sin a ESCAP, wato hukumar kula da tattalin arziki da zaman takewar al'ummar kasashen Asiya da tekun Pasific ta MDD. Mr. Ke Yousheng, ya zanta da wakilinmu na CMG, inda ya bayyana cewa, sabon tsarin raya kasar Sin, zabi ne mai dacewa da kasar Sin ta yi a halin da ake ciki yanzu, wanda zai kawo sabuwar damar ci gaba ga sauran kasashen duniya.

Wakilin kasar Sin a hukumar kula da tattalin arziki da zaman takewar al'ummar kasashen Asiya da tekun Pasific ta MDD Ke Yousheng yana ganin cewa, dalilin da ya sa kasar Sin ta tsai da kudurin kafa sabon tsarin raya kasa ta hanyar kara karfafa cudanyar tattalin arziki a cikin kasar, da kuma kara karfafa cudanyar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, na da nasaba da bangarori biyu.

Da farko, kasar Sin ta tsai da kudurin ne bisa bukatun ci gaban tattalin arzikin babbar kasa, duba da cewa an lura, manyan kasashen duniya mafiya saurin ci gaban tattalin arziki, sun taba tsara irin wannan salon raya tattalin arzikin kasashensu, salon da ya dace da bukatun kasar Sin a halin yanzu.

Na biyu kuwa, kuduri ne na matakin da kasar Sin ta dauka a kan lokacin domin dakile tasirin sauye-sauyen muhallin duniya, yana mai cewa, "A halin yanzu, yanayin duniya yana fuskantar manyan sauye-sauye, inda kasashen duniya suka shiga halin tangal tangal, ake kuma fama da ra'ayin ba da kariyar cinikayya da bangaranci, da rashin amincewa da cudanyar tattalin arziki a fadin duniya. Duk wadannan suna lalata tsarin cinikayyar duniya. A karkashin irin wannan yanayi, idan aka sanya kokarin kafa sabon tsarin raya kasa, wanda ke mai da hankali ga biyan bukatun gida a kasar Sin, to hakan zai kyautata fiffikonmu na kasuwa da sana'a, da kwararru da fasahohi, da jari da sauransu. Haka kuma zai biya manyan bukatu a sabon zamani."

Game da yadda za a kara karfafa cudanyar tattalin arziki a cikin gida, da kuma yadda za a daidaita huldar dake tsakanin cudanyar cikin gida da cudanya tsakanin kasar da sauran kasashe, Ke Yousheng ya bayyana cewa, ya dace a gudanar da ayyukan ta hanyar kara cudanya. Misali yayin da ake kokarin kara cudanya a cikin gida, ya kamata a kara mai da hankali kan kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, tare kuma da kara zurfafa kwaskwarima, yana mai cewa, "Yanzu haka ana gudanar da sabon zagaye na juyin juya halin kimiyya da fasaha a kasar Sin. Haka kuma, ana gudanar da kwaskwari a fannin sana'oi a kasar, amma wasu kasashe suna kara gallazawa fasahohin kasarmu, domin hana ci gabanmu. A don haka abu ne mai muhimmanci mu hanzarta daga matsayinmu na kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha. Dole ne mu yi kokarin cimma burinmu na raya kasa ta hanyar kirkire-kirkire, kana mu kafa sabon tsarin raya kasa. Hakan na nufin akwai bukata a yi gyare-gyare ga tsohon tsarin raya kasa, ta hanyar kara habaka rawar da kasuwa take takawa."

Ke Yousheng ya kara da cewa, mai yiwuwa ne wasu sun dauka cewa, kara karfafa cudanyar tattalin arziki a cikin kasar, yana nufin kasar Sin za ta rufe kofarta ga sauran kasashen duniya. Amma ba haka ba ne, kasar Sin za ta kara karfafa cudanyar tattalin arziki a cikin gida ne, da kuma tsakaninta da sauran kasashen duniya ba tare da rufa rufa ba.

Hakikanin abubuwan da suka faru a tarihi sun sake shaida cewa, bude kofa ya kawo ci gaba, kuma rufe kofa ya haifar da koma baya. Kasar Sin tana ba da gudumowa ga ci gaban duniya, yayin da take kokarin raya kan ta, Ke Yousheng yana mai cewa, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tana taka babbar rawa a ci gaban tattalin arzikin duniya, inda gudummawarta ta kai kaso 30 bisa dari, kuma karuwar tattalin arzikinta tana sahun gaba a duniya, za ta kuma kasance kasuwar sayayya mafi girma a duniya. Ana iya cewa, cudanyar tattalin arzikin dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya tana kara habaka, kuma ci gaban kasar Sin zai samar da dama ga sauran kasashe. Kana ba zai yiwu kasar Sin ta rufe kofarta ba, a maimakon haka, za ta kara bude kofarta ne ga sassan ketare."

Hakika sabon tsarin raya tattalin arzikin kasar Sin, ya riga ya jawo hankalin al'ummun kasa da kasa, Ke Yousheng ya ce, bisa matsayinsa na wakilin kasar Sin a MDD, wasu manyan jami'an kasashe sukan tambaye shi kan wannan batun, kuma suna sa ran cewa, sabon tsarin raya tattalin arzikin kasar Sin zai ingiza hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik. Haka kuma zai taimaka wajen farfadowar tattalin arzikin duniya, wanda ke fama da matsala sakamakon tasirin annobar COVID-19. (Jamila)