logo

HAUSA

Matsalar kabilanci da Amurka ke fuskanta ta tona aihinin halin da kasar ke ciki ta fannin kare hakkin bil Adam

2020-09-30 22:10:38 CRI

Matsalar kabilanci da Amurka ke fuskanta ta tona aihinin halin da kasar ke ciki ta fannin kare hakkin bil Adam

A gun taron majalisar kare hakkin bil Adam ta MDD da aka gudanar a karo na 45 a birnin Geneva na kasar Switzerland, matsalolin keta hakkin bil Adam da na nuna kabilanci da suka kunno kai a kasar Amurka a yayin da take kandagarkin annobar Covid-19 sun jawo hankalin sassa daban daban da ma nuna damuwarsu. A jawabin da wakilan kasashe da dama suka gabatar sun kalubalanci kasar ta Amurka da ta martaba gaskiyar lamuran da suka shafi hakkin bil Adam, sun kuma bayyana takaici dangane da yadda kasar take nuna fuskoki biyu a wannan fanni don cimma burinta na siyasa. Baya ga haka, sun bukace ta da ta duba matsalolin da ita kanta take fuskanta ta fannin kare hakkin bil Adam. A sa'i daya kuma, an yi ta yin zanga-zanga a sassa daban daban na kasar Amurka don nuna kyamar kabilanci da kuma yadda 'yan sanda ke amfani da karfin tuwo a yayin gudanar da aikinsu, lamuran da suka tona ainihin halin da kasar ke ciki ta fannin hakkin bil Adam.

Matsalar kabilanci da Amurka ke fuskanta ta tona aihinin halin da kasar ke ciki ta fannin kare hakkin bil Adam

Shin Amurka ba ta jin kunya a yayin da take nuna yatsa ga sauran kasashe? A duniyar nan, babu malaman kare hakkin bil Adam, kuma bai kamata a nuna fuskoki biyu ba ta fannin kare hakkin bil Adam. (Lubabatu)