Tsokacin Ambasada Bakori kan alakar Sin da Najeriya da bikin ranar kafuwar kasashen biyu
2020-09-29 14:58:29 CRI
A wannan mako, wakilinmu Ahmad Inuwa Fagam, ya zanta da jakada na biyu na Najeriya a kasar Sin Ambasada Bakori Aliyu Usman wanda ya shafe kusan shekaru goma yana aikin jakadanci a kasar Sin, ya tabo muhimman batutuwa dake shafar huldar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Sin, da irin nasarorin da aka samu a cikin shekaru kusan 49 tun bayan kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu, kana yayi tsokaci kan cika shekuru 60 da samun 'yancin kan Najeriya, da kuma shekaru 71, da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin.(Murtala Zhang)