logo

HAUSA

Ilimi gishirin rayuwa

2020-09-29 14:51:13 CRI

Ilimi gishirin rayuwa

 

A yunkurinta na tallafawa da kokarin raya al'umma mai makoma iri guda, da kuma rike matsayinta na babbar kasar, a jiya Litinin, kasar Sin ta lashi takobin ci gaba da taimakawa raya harkar ilimi a kasar Sudan ta kudu, inda ta ce za ta zuba kimanin dala miliyan 20 a mataki na biyu na hadin gwiwar da tun dama can suka kulla da kasar a bangaren ilimi, domin taimakawa yara da kasar mafi kankantar shekaru a duniya, wajen bunkasa harkar samar da ilimi. kasar Sudan ta kudu ta kasance cikin mawuyacin hali tun bayan da ta samu 'yancin kai, inda rikice-rikice suka addabeta. Lamarin da ya haifar da rashin tsaro da kayayyakin more rayuwa da na biyan muhimman bukatun al'umma da gudun hijira da rashin ilimi da sauran wasu muhimman batutuwa. Baya ga haka, akwai matsaloli na rashin arziki a kasar. A cewar bankin duniya, sama da rabin al'ummar kasar na rayuwa cikin talauci. Kuma gwamnatin kasar ba ta da isassun kudin bada tallafi, sannan gazawarta na samar da kudin gudanar da ayyukan illimi a kasar, ya sa makarantu su yi tsadar da wasu iyalai ba za su iya biya ba. Kasar na fuskantar tarin matsaloli, don haka, taimaka mata ta kowacce fuska abu ne da za ta yi maraba da shi ainun. Muddun ana son ganin kawo karshen matsalar da kasar ke fuskanta, dole, a fara daga tushe. Taimakawa wajen inganta ilimin yara a kasar zai bude wani sabon babi ga kasar, domin zai samar da sabuwar zuri'a mai cike da ilimi da basira da kuma dabara, wanda zai kai kasar ga samun ci gaba da kuma magance kaso mai yawa na tarin matsalolinta Hakika, kasar Sin ta yi amfani da irin kaifin basirarta da kyakkyawan manufarta a danganrtakarta da Sudan ta kudu, wanda ya shafi bunkasa kwarewar malamai da kuma tallafawa harkokin samun ilimi. Haka zalika, taimakon nata, zai ba yara daga matalautan iyali damar samun ilimi gishirin rayuwa.  

Ilimi gishirin rayuwa

 

Ko a kashin farko na shirin da ta gabatar a wannan fanni, kasar Sin ta samar da litattafan karantu sama da miliyan 3 ga yaran kasar a shekarar 2018, inda tuni wannan yunkuri ya sauya tsarin bada ilimi a kasar, ta yadda ya kara mayar da hankali kan fahimtar da dalibai abun da ake koyarwa maimakon yadda a baya ya mayar da hankali kan malamai.

Wannan mataki ba abu ne da za a ga alfanun shi yau ko gobe ba, amma abu ne da zai sauya tunani da kasar baki daya a nan gaba.

Yara manyan gobe! Kamar yadda jakadan kasar Sin a kasar ya bayyana, yara su ne makomar kowacce kasa. Don haka, tallafa musu da ilmantar da su, ginshikin mataki ne na neman ci gaba da samar da gagarumin sauyi mai inganci da dorewa. (Faeza Mustapha)