logo

HAUSA

An yi taron tattaunawa kan zamani bayan cutar COVID-19

2020-09-29 13:44:05 cri


An kaddamar da taron tattaunawa bisa jigon "Odar kasashen duniya da kuma yadda za a daidaita harkokin kasa da kasa bayan cutar COVID-19", jiya Litinin a daki mai launin shudi dake nan Beijing, inda wakilin gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya halarci bikin kaddamar da taron, har ma ya gabatar da wani jawabi. Kwararru kusan dari 1 wadanda suka fito daga kasar Sin da kasashen Amurka da Burtaniya da Japan da wasu kungiyoyin kasa da kasa, sun halarci taron.

An yi taron tattaunawa kan zamani bayan cutar COVID-19

A cikin jawabi nasa, Mr. Wang Yi ya nuna cewa, yanzu duk duniya na cikin wani muhimmin lokaci bayan Yakin Duniya na 2. Ya ce ina duniya za ta nufa bayan cutar COVID-19? Ya kamata kowace kasa ta mai da hankali kan wannan batu, domin kaucewa yin kuskure.

Sannan Wang Yi ya bayyana matsayin da kasar Sin take dauka a gaban sauye-sauyen da duk duniya ke fuskanta, inda ya jaddada cewa, ya kamata neman samun ci gaba cikin lumana ya zama babban jigo ga dukkan kasashen duniya. Ya kamata adalci ya zama babbar darajar da kowace kasa za ta mutunta. Sannan neman samun ci gaba cikin hadin kai ya zama daidaitaciyar hanyar da ya kamata kowace kasa ta bi. Daga karshe dai, kara bude kofa da hadin gwiwa, makoma ce da ta kamaci kowace kasa a nan gaba. Wang Yi yana mai cewa, "A kan batun tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa, manyan kasashe suna da nauyi na musamman, bai kamata su illata moriyar sauran kasashen duniya domin kawai neman tabbatar da tsaronsu ba, bai kamata su kwace ikon neman ci gaba na sauran kasashen duniya ba ta hanyar mulkin danniya. Kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa kan matsayin neman samun ci gaba cikin lumana, sannan za ta hada kan sauran kasashen duniya wajen dakile wasu hujjoji irin su 'sanya moriyar wata kasa a gaban ta sauran kasashe', da 'samun riba ga bangare daya kadai, ta yadda tilas ne daya bangaren ya yi hassara'."

A cikin jawabinsa, Mr. Ban Ki-moon, tsohon babban sakataren MDD ya nuna cewa, a 'yan shekarun baya, wasu kasashe su kan nuna shakku kan kokarin bunkasa duk duniya bai daya da kungiyoyin kasa da kasa, lamarin ya haddasa wasu matsaloli ga aikin dakile cutar da sauye-sauyen yanayin duniya. Har ma wasu kasashe masu arziki sun sanya moriyarsu a gaban moriyar daukacin bil Adama. Mr. Ban Ki-moon ya bayyana cewa, "A lokacin da muke fuskantar annobar, ya kamata MDD ta shaida muhimmancinta, wato a wannan muhimmin lokaci, ya kamata a dakile wannan rikicin da duk duniya ke fuskanta bisa karfin gamayyar kasa da kasa. Ya kamata ta kasance wata kungiyar kasa da kasa mafi girma, inda kusan dukkan kasashen duniya ke zaman mambobinta, ya kamata mu nemi sassa daban daban da su tsaya kan ra'ayin kasancewar bangarori da dama. A waje daya, ya kamata mu nemi sassan da su kara hadin gwiwa domin warware wasu muhimman matsalolin da suke shafar duk duniya baki daya."

Da yake jawabi, Fukuda Yasuo, tsohon firaministan kasar Japan ya bayyana cewa, kafa tabbataciyyar dangantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Amurka yana da muhimmanci matuka ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankin Asiya, har ma da duk duniya. Mr. Fukuda Yasuo yana mai cewa, "A 'yan shekarun baya, manufofin da kasar Amurka ta dauka kan batutuwan da ke shafar MDD, da matsalar sauye-sauyen yanayin duniya, da yin cinikayya cikin 'yanci, da tabbatar da dimokuradiyya a cikin gida da dai makamantansu, sun sa ana shakkar, ko kasar Amurka tana sabawa burin da ta tsara a da. Lamarin ya lallata tasirin kasar Amurka a cikin al'ummar kasashen duniya. Shugaba Xi Jinping na kasar Sin yana fatan kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, kuma kasarsa ba za ta kawo barzana ga sauran kasashen duniya ba. Ba za ta yi mulkin danniya a duk duniya ba har abada, wannan muhimmin sakamako ne na manufofin diflomasiyya da kasar Sin take aiwatarwa." (Sanusi Chen)