logo

HAUSA

Fa'iza Mustapha: Fasahar rina ta gargajiyar kabilar Miao ta burge ni

2020-09-28 13:40:59 CRI

A kwanakin baya, Kande Gao da Fa'iza Mustapha sun ziyarci lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin domin gano wata fasahar gargajiyar kasar Sin mai tarihin fiye da shekaru 1400, wato fasahar amfani da kakin zuma wajen zane-zane a kan yadi sa'an nan a rina shi, wadda mata 'yan kabilar Miao ke rike da ita kuma sun yi amfani da ita wajen samun abin dogoro da kai. A cikin shirinmu na yau, su biyu za su tattauna kan batun.