logo

HAUSA

Dora laifi kan wasu, ba zai warware matsaloli ba

2020-09-25 20:05:40 CRI

A kwanan baya, an kaddamar da babban taron MDD na bana, inda shugabannin kasashen duniya, ciki har da shugaban kasar Amurka Donald Trump, suka bayar da jawabai daya bayan daya.

Dora laifi kan wasu, ba zai warware matsaloli ba

A cikin jawabansu, sauran shugabannin suna fatan za a kara yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, domin dakile wasu matsaloli masu tsanani da ke kasancewa a gabansu tare, amma a nasa bangare, shugaban kasar Amurka ya ci gaba da sanya moriyar kasarsa a gaban ta saura, har ma ba tare da jin kunya ba, da kansa ya yaba da sakamakon dakile annobar COVID-19 da gwamnatinsa ta samu, duk da cewa ya zuwa yanzu, yawan wadanda suka harbu da cutar ya wuce miliyan 7, sannan yawan mutanen da suka mutu sakamakon harbuwa da cutar ya wuce dubu dari 2 a kasarsa.

Lallai wannan dan siyasa bai san mene ne abin kunya ko kadan ba. Bugu da kari, a yayin taron, ya sake zargin kasar Sin da kungiyar WHO ba dalili bare hujja. Sanin kowa ne, bayan da aka tabbatar da bullar cutar COVID-19 a kasar Sin a farkon bana, ba tare da bata kowane lokaci ba, hukumar kasar Sin ta sanar wa wakilin sashen WHO dake nan kasar Sin, har ma ta samar wa takwararta ta kasar Amurka kai tsaye nan da nan. Sabo da haka, a watan Janairu da Faburairu, shugaban kasar Amurka mai ci, ya taba yabawa da kwararan matakan dakile cutar da gwamnatin kasar Sin ta dauka. Bisa kwararan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka, tare da goyon bayan al'ummar Sinawa, cikin watanni uku kawai, kasar Sin ta cimma nasarar shawo kan cutar a cikin gida. Sakamakon nasarar da ta samu, tattalin arzikinta ma ya samu farfadowa cikin sauri. Game da dalilin da ya sa kasar Sin ta cimma nasarar shawo kan cutar, kafofin watsa labaru na kasashe da dama sun wallafa sharhohinsu, inda suka yaba da matakan da kasar Sin ta dauka. Alal misali, a kwanan baya, jaridun Newsweek ta Amurka, da "Bangkok Post" ta kasar Thailand sun ce nasarar da Sin ta cimma a wannan fanni na da nasaba da sahihan matakai, kuma masu tsauri da gwamnatin kasar ta aiwatar, baya ga amincewar da al'ummun kasar suka nuna ga gwamnatinsu, tare da managarcin jagoranci da JKS ke bayarwa.

Dora laifi kan wasu, ba zai warware matsaloli ba

Bugu da kari, a lokacin da kasar Sin take kokarin shawo kan cutar, ba ta taba zargin kowa ba, balle dora wa wani laifi, sai dai ta mai da hankalinta kawai wajen dakile cutar. Amma duk da cewa wannan shugaban kasar Amurka ya san wannan cuta tana illata rayukan dan Adam a farkon bana, amma ya zabi boye wannan bayani, maimakon sanar wa al'ummun Amurka kamar yadda ya kamata, domin moriyar radin kansa ta yunkurin sake cin babban zaben da za a yi a watan Nuwamban bana.

Sakamakon haka, a kullum shi da gwamnatinsa su kan dora wa kasar Sin, da kungiyar WHO laifin gaza shawo kan cutar maimakon daukar wajibabbun matakan dakile cutar da ya kamata ya dauka. Dadin dadawa, ya mai da hankali kan yadda zai iya hana bunkasar kamfanonin kasar Sin masu fasahohin zamani.

A don haka, kamar yadda Mr. Zhang Jun, wakilin kasar Sin a MDD ya fadi, ya kamata kasar Amurka ta fahimci cewa, gazawarta na tunkarar annobar, laifinta ne. Ya kamata Amurka ta fahimci cewa, zargin wasu kan wannan annoba, ba zai sa ta magance matsalolinta ba. Kowace kasa tana da nata matsalar da ma hanyar ci gabanta. A don haka, ya kamata kowace kasa ta warware matsalolinta ta hanyar da ta dace da ita. Dora laifi kan wasu, ko shirga karya, da zamba, ko sata, babu matsalolin da za su iya warwarewa, sai ma kara fadawa hanyar da ba ta dace ba. (Sanusi Chen)