logo

HAUSA

Jawabin Xi Jinping zai taimaka wajen gudanar da ayyuka bisa ra'ayin bangarori daban daban a duniya

2020-09-25 14:59:33 cri


Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a yayin taron kolin murnar cika shekaru 75 da kafuwar MDD da muhawarar babban taron MDD karo na 75, jawabin da ya jawo hankalin mutane daga bangarori daban daban na kasar Masar. Direktan hukumar kula da harkokin waje ta kasar Masar Ezzat Saad El-Sayed ya bayyana cewa, yayin da ake fuskantar kalubale kan kiyaye tsarin tafiyar da harkokin duniya a halin yanzu, jawabai guda biyu da shugaba Xi ya yi a taron MDD suna da babbar ma'ana.

A yayin zantawar da aka yi da shi, direkta El-Sayed ya bayyana cewa, a cikin jawaban biyu da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a tarukan na MDD, ya jaddada muhimmancin kiyaye ra'ayin cudanyar bangarori daban daban, ya kuma nuna yabo ga muhimmiyar rawar da MDD ta taka a cikin shekaru 75 da suka gabata a fannonin sa kaimi ga inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, da girmama juna, da kuma kin amincewa da ra'ayin bangare daya. Ya ce,

"Sin ta taka muhimmiyar rawa a kungiyoyin kasa da kasa ciki har da MDD. A matsayinta na kasa mai kujerar dindindin a kwamitin sulhun MDD, kasar Sin tana daukar nauyin tabbatar da zaman lafiyar duniya da nuna goyon baya ga ayyukan MDD. A cikin jawabai biyu na shugaba Xi Jinping, an jaddada tunanin samun bunkasuwa ta hanyar hadin gwiwa tare. A hakika, kasar Sin ta bukaci kasashen duniya da su mayar da hankali kan martaba ra'ayin cudanyar bangarori daban daban. Kiran da shugaba Xi Jinping ya yi na raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama ya bayyana tunanin Sin kan harkokin diplomasiyya, wanda ke da nasaba da shawarar 'ziri daya da hanya daya' ya kuma dace da burin bunkasuwa na MDD."

El-Sayed yana ganin cewa, ra'ayin cudanyar bangarori daban daban, shi ne tushen tsarin kasa da kasa. Ya ce, yayin da ake kokarin yaki da cutar COVID-19 da sauran manyan batutuwa a duniya a halin yanzu, ya zama tilas kasa da kasa su kara yin hadin gwiwa wajen tinkarar matsalolin tare. Ya kuma nuna goyon baya ga kiran da shugaba Xi ya yi a cikin jawabinsa wato sa kaimi ga raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, ya ce,

"Aiwatar da ayyuka bisa ra'ayin bangarori daban daban wani muhimmin bangare ne na jawabin shugaba Xi. Mu kasance zama tare a duniya guda, ya kamata a kiyaye duniya tare. Bisa jagorancin ra'ayin cudanyar bangarori daban daban, Sin ta gabatar da manufofi biyu wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama wato nuna daidaito kan siyasa, da samun moriyar juna kan tattalin arziki, da kafa tsarin kiyaye tsaro, da sa kaimi ga yin mu'amalar al'adu, da kiyaye muhallin hallitu, wadanda za su kawo moriya ga dukkan duniya baki daya."

Hakazalika, El-Sayed ya yi nuni da cewa, ana iya martaba ra'ayin cudanyar bangarori daban daban da Sin ta yi kira yayin da ake yin hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19 a duniya. Ya bayyana cewa, bayan da cutar COVID-19 ta barke a duniya baki daya, Sin ta yi kokarin taimakawa kasashen duniya don yaki da cutar. Bana shekaru 64 ke nan da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Masar, Sin na fatan za a zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da kiwon lafiya da sauransu, haka kuma kasashe, ba za su dakatar da yin hadin gwiwa ba a sakamakon cutar. Ya ce,

"A yayin da ake tinkarar cutar COVID-19, Sin ta kiyaye yin ciniki cikin 'yanci, hakan ya sassauta tasirin da cutar ta haifar kan tattalin arzikin kasa da kasa. Na yi imani cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Masar da Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya zai kawo moriya ga bangarorin biyu. Kasar Masar tana yin kokarin shiga tsarin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, da kasashen Larabawa da sauransu don daidaita matsalolin da take fuskanta a sakamakon cutar COVID-19 cikin hanzari." (Zainab)