logo

HAUSA

Jawabin shugaba Xi na ci gaba da jan hankalin masana

2020-09-24 14:27:22 cri

Jawabin shugaba Xi na ci gaba da jan hankalin masana

A jiya Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin jawabi, yayin muhawarar babban taron MDD karo na 75, inda ya nanata cewa, ganin yadda annobar COVID-19 ke ci gaba da bazuwa a duniya, ya dace kasashen duniya su maida moriya, gami da rayuwar mutane a gaban komai, da karfafa hadin gwiwar dukkanin sassa, da zama tsintsiya madaurinki daya.

Game da hakan, mun zanta da Dr. Sheriff Ghali Ibrahim, masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja dake Najeriya, wanda ya yi mana fashin baki game da muhimman batutuwa da shugaban na Sin ya tabo cikin jawabin nasa, ciki hadda batun muhimmancin hadin gwiwar dukkanin kasashen duniya a fannin ci gaba, musamman yayin da ake tunkarar kalubaloli. Da ma burin kasar Sin na ba da gudumawa ga aikin shawo kan cutar COVID-19, da tasirin MDD a fannonin wanzar da ci gaba. (Maryam Yang)