logo

HAUSA

Xi ya gana da Guterres ta kafar bidiyo

2020-09-24 10:31:32 cri

A yammacin jiya Laraba shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da babban sakataren MDD Antonio Guterres ta kafar bidiyo, inda ya jaddada cewa, kasarsa za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka domin goyon bayan aikin majalisar, ya kuma yi nuni da cewa, ya dace kasa da kasa su kara karfafa cudanyar dake tsakaninsu, ta yadda za a gina kyakkyawar makomar bil Adama.

Yayin ganawar da ya yi da babban sakataren MDD Guterres, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, "Ina farin ciki matuka da ganawa da Mr. Guterres, shekarar bana tana da ma'ana ta musamman ga MDD, a don haka bangarori daban daban suka shirya ayyuka a jere, domin murnar cika shekaru 75 da kafuwarta, kamata ya yi kasashen duniya su yi amfani da wannan dama, domin sake nanata muhimmancin goyon bayan ra'ayin cudanyar bangarori daban daban, tare kuma da sake nanata alkawarin da suka yi kan martaba ka'idojin majalisar. Tun bayan kafuwar majalisar, ta fuskanci wahalhalu da dama a cikin wadannan shekaru 75, amma ta samu babban sakamako wajen shimfida zaman lafiya a fadin duniya, a nata bangare, kasar Sin a matsayinta na zaunanniyar mambar kwamitin sulhun majalisar, za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka domin goyon bayan rawar da majalisar take takawa a cikin harkokin kasa da kasa, za kuma ta ci gaba da goyon bayan ayyukan majalisar baki daya."

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, yanzu annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a fadin duniya, a don haka, ya zama wajibi kasashen duniya su kara kokari domin ganin bayanta cikin hanzari. Kasar Sin tana son raba fasahohinta na yaki da annobar ga sauran kasashe, kuma za ta ci gaba da samar da goyon baya da tallafi ga kasashen da suke da bukata, kana za ta ci gaba da goyon bayan rawar da majalisar take takawa, musamman ma rawar da hukumar kiwon lafiyar duniya take takawa yayin da ake kokarin dakile annobar, ban da haka, kasar Sin ta yi alkawari cewa, za ta samar da allurar rigakafin cutar ga daukacin kasashen duniya, bayan da ta yi nasarar kammala aikin samar da allurar, musamman ga kasashe masu tasowa.

Shugaba Xi ya nuna cewa, duk da cewa, an gamu da sabbin matsaloli bayan barkewar annobar, amma dukkansu suna shafar zaman lafiya da samun ci gaba, shi ya sa ya kamata kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya, ya kara ba da muhimmanci kan wadannan batutuwa, saboda ba zai yiyu al'ummun kasashen duniya, su goyi bayan ra'ayin bangaranci da nuna fin karfi ba.

Xi ya jaddada cewa, ya dace a rage tasirin da annobar ta haifar ga tattalin arzikin duniya da rayuwar al'ummun kasa da kasa, akwai bukatar kasashen duniya, su tattara albarkatu da karfinsu waje guda, domin taimakawa kasashe masu tasowa a bangaren rage gibin dake tsakanin masu wadata da matalauta.

Xi ya kara da cewa, ya zama dole a samu ci gaba mai dorewa, abu mafi muhimmanci shi ne a daidaita huldar dake tsakanin bil Adam da hallitu, kasar Sin, ba ma kawai tana kokarin kyautata wayewar kan hallitu masu rai da marasa rai ba, har ma tana sauke nauyin dakile matsalar sauyin yanayi dake bisa wuyanta, ta yadda za a kiyaye duniyarmu, inda daukacin bil Adam suke rayuwa, kana tana kokarin gina "hanyar siliki" ba tare da gurbata muhalli ba tare da sauran kasashe daban daban.

Xi ya kuma bayyana cewa, yanzu haka an gamu da matsala a tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa, sakamakon barkewar annobar COVID-19, a don haka ya dace bangarori daban daban su yi la'akari domin kyautata tsarin dake karkashin jagorancin MDD, kasar Sin ba ta son yin adawa kan tunani, da raba kai ko kuma nuna fin karfi, muradunmu shi ne kara kyautata rayuwar al'ummun kasar da yawansu ya kai miliyan 1400, tare kuma da taka rawa wajen ci gaban bil Adam, amma kasar Sin ba za ta amince wasu su lalata ikon mulki da kimar al'ummu da moriyar ci gabanta ba, tabbas za ta kiyaye hakki da moriyarta da kuma adalcin duniya baki daya.

Hakazalika, Xi ya jaddada cewa, abu mafi muhimmanci shi ne, a kara karfafa cudanyar dake tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a gina kyakkyawar makomar bil Adam.

A nasa bangare, babban sakataren MDD Guterres ya bayyana cewa, yanzu ana fama da yaduwar cutar COVID-19 da matsalar sauyin yanayi da wasu rikice-rikice da kalubale, a don haka, ana bukatar ra'ayin cudanyar bangarori daban daban da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa da kuma MDD mai karfi, kuma ya nuna godiya ga kasar Sin saboda har kullum tana goyon bayan ra'ayin gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban da kuma aikin majalisar, kana majalisar tana fatan za ta kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a nan gaba.(Jamila)