A kullum kasar Sin na goyon bayan kasancewar bangarori daban-daban a lokacin da ake daidaita harkokin kasa da kasa
2020-09-23 17:36:54 CRI
A ranar Litinin 21 ga watan Satumban shekarar 2020 ne, aka shirya taron manyan jami'an MDD ta kafar bidiyo, yayin da majalisar ke bikin cika shekaru 75 da kafuwa.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping na daga cikin wadanda suka halarci taron da ma gabatar da muhimmin jawabi, inda ya bayyana cewa, wajibi ne MDD ta kasance mai nuna adalci, da martaba doka, da bunkasa cudanyar bangarori daban-daban, da mayar da hankali kan matakan da suka dace a dauka bayan ganin bayan annobar COVID-19.
Ya kuma nanata kudirin kasar Sin, na kasancewar bangarori daban-daban, da yin gyare-gyare, da bunkasa tsarin tafiyar da harkokin duniya, tare da alkawarin gina al'umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama. Jawabin na shugaba Xi ya samu yabo daga masana na ketare, inda suka bukaci kasashen duniya da su kara hada kai, don daukar matakan da suka dace na tunkarar barazana da kalubalen da duniya ke fuskanta.
Babban sakataren MDD, Antonio Guterres da babban darektan hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya, duk sun bayyana cewa, kalaman shugaba Xi game da kudirin kasarsa na nacewa ga cudanyar bangarori daban-daban kan harkokin kasa da kasa, wata alama ce da a fili dake nuna babbar rawar da tsarin MDD yake takawa, na kasancewa tare da goyon bayan kasashe mambobin majalisar, a wannan lokaci da duniya ke fama da wannan annoba.
Shi ma darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya, Charles Onunaiju, ya bayyana cewa, kasar Sin ta fito da wata taswira a zahiri dake bayyana bukatar gina al'umma ta bai daya, ta hanyar amfani da shawarar nan ta "Ziri daya da hanya daya", don kafa tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa ba tare da wata rufa-rufa ba, wanda kuma zai kunshi kowa da kowa. (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)