logo

HAUSA

Xi ya gabatar da jawabi yayin taron kolin cika shekaru 75 na kafuwar MDD

2020-09-22 11:30:30 cri

Xi ya gabatar da jawabi yayin taron kolin cika shekaru 75 na kafuwar MDD

A jiya Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a yayin taron kolin da aka shirya domin cika shekaru 75 da kafa MDD, inda ya jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu, ya kamata MDD ta kara mai da hankali kan tabbatar da adalci yayin da take gudanar da harkokinta bisa doka, ta hanyar ingiza hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, kana ya sake nanata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban daban, kuma za ta kara yin kokari kan gyare-gyare da gina tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa, ta yadda za a ingiza gina kyakkyawar makomar bil Adam.  

A cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 75 da suka gabata, al'ummun kasa da kasa sun yi namijin kokari, inda suka yi nasarar yaki da tafarkin murdiya, nasarar da suka samu nasara ce ta adalci. A bisa irin wannan yanayi wato bayan da al'ummun kasa da kasa suka sha wahalhalun yake-yaken duniya har sau biyu, shi ne aka kafa MDD, yanzu haka an bude sabon shafin zaman lafiya da bunkasuwa a fadin duniya bayan kokarin da aka yi a cikin shekaru 75 da suka gabata, shugaba Xi yana mai cewa, "Tarihin MDD na tsawon shekaru 75, tarihin ci gaban zaman takewar al'ummun kasa da kasa ne, inda yanayin kasa da kasa ya fuskanci manyan sauye-sauye, kuma manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban daban ta kara samun karbuwa a tsakanin al'ummun kasa da kasa, kana MDD tana cike da kuzari, duk da cewa ta gamu da kalubaloli daban daban, inda al'ummun kasa da kasa da yawansu ya kai sama da biliyan 7 suna sa ran za su cimma burin jin dadin rayuwa karkashin jagorancin MDD."

Shugaba Xi ya jaddada cewa, yanzu duniyarmu tana fama da manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru 100 da suka gabata, yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta kawo jarrabawa mai tsanani ga daukacin duniya, bil Adam sun shiga sabon zamani na cudanya da juna, a don haka kasashen duniya suna da moriya da kuma makoma daya, a don haka, ya dace su dakile kalubale da barazana dake gabansu tare. To a sabon yanayin da ake ciki yanzu, kamata ya yi a yi la'akari wai wace irin MDD ake bukata? Ta yaya MDD take takawa rawarta yayin da ake kokarin dakile yaduwar annobar COVID-19?

Kan wannan batun, shugaba Xi ya gabatar da shawarwari hudu, na farko, a kiyaye adalci, a cewarsa: "Ya dace kasashen duniya ko manya ko kanana su nuna biyayya ga juna, kuma su yi zaman tare cikin daidaito, saboda hakan shi ne bukatun ci gaban zamani,da ka'ida mafi muhimmanci ta muradun MDD, kuma kamata ya yi mu gina duniyarmu tare ta hanyar yin tattaunawa, a kiyaye tsaron duniya ta hanyar hada kai, a raba sakamakon ci gaban da aka samu domin gina kyakkyawar makomar bil Adam tare. Kana ya kamata a kara mai da hankali kan rawar da kasashe masu tasowa za su taka a cikin harkokin MDD, domin nuna fata da moriya na yawancin kasashen duniya."

Na biyu, a tafiyar da harkokin MDD bisa doka, ka'idojin MDD, ka'idoji ne masu muhimmanci da ake bi yayin da ake daidaita huldar kasa da kasa, kana su ne tushen tabbatar da zaman lafiyar tsarin kasa da kasa, ya zama wajibi a tsaya tsayin daka domin kiyaye wadannan ka'idojin.

Na uku, ingiza hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, hakika ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa shi ne burin farko na kafuwar MDD, kana ita ce babbar ka'idar majalisar, a don haka, ya dace a gudanar da shawarwari a maimakon hargitsi, kuma a yi tattaunawa a maimakon matsa lamba, kana a yi kokari domin samun ci gaba tare a maimakon lalata moriyar juna, a karshe a hada moriyar kasa da moriyar duniya, ta yadda za a gina babban iyalin duniya mai zaman jituwa.

Na hudu, ya dace a dauki matakai a kan lokaci, shugaba Xi ya bayyana cewa, idan ana son aiwatar da manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban daban, kamata ya yi a dauki matakai a kan lokaci, yanzu haka MDD tana dukufa kan aikin tabbatar da tsaro da ci gaba da kuma kiyaye hakkin bil Adam, da kiwon lafiyar jama'a, musamman ma wajen cimma muradun samun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin ita ce kasa ta farko adda ta sa hannu kan ka'idojin MDD, kana kasa mai tasowa daya kacal dake cikin zaunannun mambobin kwamitin sulhun MDD, yana mai cewa, "Har kullum kasar Sin tana nacewa kan manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban daban, tana kuma nuna kwazo da himma kan gyare-gyare da gina tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa, haka kuma tana kokarin kiyaye tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorancin MDD, tare kuma da goyon bayan rawar da MDD ke takawa a cikin harkokin kasa da kasa."(Jamila)