logo

HAUSA

Duniya ta yaba tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin kan yaki da fatara

2020-09-21 18:21:45 CRI

Duniya ta yaba tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin kan yaki da fatara

Masu hikimar magana na cewa labarin zuciya a tambayi fuska. A karo da dama, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sha nanata aniyar mayar da rayukan jama'a da kyautata rayuwarsu a gaban komai. Kuma wannan shi ne hakikanin ma'anar shugabanci wato sadaukar da kai, da hidimtawa al'ummar kasa. Kamar yadda shugaban ya sha furtawa cikin kalamansa cewa dukkan mambobin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin burinsu shi ne kokarin sauke nauyin dake bisa wuyan jam'iyyar ta JKS, wato bautawa kasa da jama'ar kasa. Wani abin ban sha'awa shi ne, hasashen masanan kasa da kasa ya nuna cewa, kasar Sin za ta iya cimma nasarar kawar da kangin fatara a tsakanin al'ummarta ya zuwa karshen wannan shekarar da muke ciki duk da kalubalolin annobar COVID-19 da duniyar ke fuskanta. Wani kwararren masani na cibiyar nazarin siyasar kasa da kasa dake birnin Havana na kasar Cuba, Eduardo Regalado, ya yi tsokaci kan manufar gwamnatin Sin na yaki da fatara, inda ya ce, cikin wasu 'yan gwamman shekaru da suka gabata kasar Sin ta yi aiki tukuru wajen tsame mutane kusan miliyan 800 daga kangin talauci, wanda hakan wata alama ce dake nuna karfin hali da jajurcewar da kasar ke da shi wajen tinkarar kalubalolin duniya. Masanin na kasar Cuba ya ce, kasar Sin ta baiwa duniya gudunmawa wajen rage kaifin talauci da kashi 70 bisa 100 a kokarin cimma muradun MDD na samar da dawwaumamman ci gaban duniya nan da shekarar 2030. Ko shakka babu, wannan samakon da kasar Sin ta cimma na yaki da talauci ya tabbata ne bisa jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda ita ce jigon nasarorin da gwamnatin Sin da ma al'ummar Sinawa suka samu. Koda yake, ba wai Regalado ne kadai ke da wannan ra'ayi ba, ko a karshen wannan mako, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi jawabi game da babbar gudunmmawar da kasar Sin ke bayarwa wajen shawo kan kalubalolin duniya da kuma nasarorin da kasar ta samu a yaki da fatara. Har ma Guterres ya bayyana kasar Sin a matsayin "Jigon hadin gwiwar bangarori daban daban," jami'in MDD ya ce, Sin tana ci gaba da taka muhimmiyar rawa a harkokin shiyya, da al'amurran kasa da kasa, ya kara da cewa, hadin gwiwar kut-da-kut da MDD ke yi da kasar Sin ya kara fadada zuwa bangarorin wanzar da zaman lafiya da tsaro a dukkan sassan duniya, wanda ya hada da nahiyar Asiya, Afrika, da yankin gabas ta tsakiya. A bayyane take karara, idan muka yi la'akari da rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin kasa da kasa musamman batun rajin tabbatar da hadin gwiwar bangarori daban daban, da kokarin tafiyar da al'amurran tattalin arzikin duniya a bisa tsarin moriyar dukkan bangarori, da nuna adawa da ra'ayin kashin kai, da kalubalantar ra'ayin kariyar ciniki da makamantansu, za mu iya cewa, tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin yana samun yabo daga dukkan fannoni. (Ahmad Fagam)