logo

HAUSA

Na'urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin ta kammala daidaitawa karo na biyu a falaki

2020-09-21 10:57:00 cri

Hukumar kula da harkokin zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar (CNSA), ta bayyana cewa, na'urar binciken duniyar Mars da kasar ta harba mai suna Tianwen-1, jiya Lahadi ta kammala daidaituwa karo na biyu a falaki.

A jiyan ne, da misalin karfe 11 na dare agogon birnin Beijing na kasar Sin, na'urar ta kammala wannan aiki, bayan da injunanta guda hudu masu karfin 120N suka yi aiki na tsawon dakika 20. Haka kuma an tabbatar da ingancin injunan yayin wannan aiki.

Ita dai wannan nau'ra, ta yi tafiyar kimanin kwanaki 60 a cikin falaki, kuma nisanta daga doron duniya, ya kai kimanin kilomita miliyan 19. Dukkan sassan na'urar suna aiki yadda ya kamata.(Ibrahim)