logo

HAUSA

Kudan zuma da ke samar da arzikii

2020-09-18 15:17:07 CRI



Yankin Miyun na birnin Beijing, yanki ne mai matukar ni'ima, da ya shahara da wani babban wurin adana ruwa da ke samar da ruwan sha ga mazauna birnin na Beijing. Baya ga haka, ana kuma yi wa yankin Miyun da kirarin garin kudajen zuma, a sakamakon yadda ake yawan kiwon kudan zuma a wurin. Bayanai na cewa, tun zamanin da, mazauna yankin suna da al'adar kiwon kudan zuma, har ma sarakunan gargajiya na wancan lokaci na son shan zumar da aka samar a wurin.

Bisa ga ni'imar yanayin yankin, an fara dukufa a kan bunkasa aikin kiwon kudan zuma a yankin a cikin 'yan shekarun da suka gabata a sakamakon yawan nau'o'in tsirrai sama da dubu da ke iya samar da zuba a wurin, kuma malama Liu Fengping na daya daga masu kiwon kudan zuma a wurin.

Yanzu shekaru kimanin bakwai ke nan da Malama Liu Fengping ta fara sana'ar kiwon kudan zuma, ta ce, kafin wannan, ta dogara ne ga noman masara da 'ya'yan itatuwa, sai dai rayuwa na da wahala a sakamakon dan kudi kadan da bai taka kara ya karya ba da take samu a aikin noman. Amma abubuwa sun inganta, bayan da ta shiga kungiyar hadin kan manoma masu kiwon kudan zuma, ta ce, "Ai, gaskiya sun fid da mu daga kangin talauci, bayan da muka samu kanmu a cikin wannan kungiya, bayan da su malam Guo Xiaoli suka sa mu aikin kiwon kudan zuma. A baya, gaskiya ni da iyalai na mun fuskanci talauci sosai, kuma rayuwata ta inganta sosai har na fara jin dadi bayan da na kama aikin kiwon kudan zuma."

 

Malam Guo Xiaoli da malama Liu Fengping ta ambata, shi ne babban darektan kungiyar hadin kan masu kiwon kudan zuma ta Baoyuling, da ke yankin Miyun na birnin Beijing. Malama Liu Fengping ta ce, bayan da malam Guo Xiaoli ya zo wajensu, ganin yadda suke fama da talauci, sai ya bukace su da su kama aikin kiwon kudan zuma. Ta ce, kafin wannan, tana samun yuan kimanin dubu 20 zuwa dubu 30, kwatan kwacin dalar Amurka dubu 3000 zuwa 4000 a kowace shekara, a noman masara da 'ya'yan itatuwa, amma yanzu kudin da take samu ya ninka sau daya.

A zantawarmu da malam Guo Xiaoli, babban darektan kungiyar hadin kan masu kiwon kudan zuma ta Baoyuling da ke yankin Miyun na birnin Beijing, ya ce, kawo yanzu, akwai manoma 400 da suka shiga kungiyarsa, kuma daga cikinsu, kimanin 80 ne suka kasance masu fama da talauci. Ya ce, "Muna iyakacin kokarin tallafawa masu fama da talauci, kuma babu wani abin damuwa a gare su, abin da ake bukata kawai shi ne su samar da kwadago. Misali, gwamnati na samar musu kudajen zuma da na'urorin kiwonsu kyauta. Baya ga haka, kungiyarmu na samar musu fasahohi, sai su bi yadda muka koya musu, da lokacin dibar zuma ya yi, sai su diba su ba mu, sa'an nan mu biya su kudin zumar. Ban da haka, mu kan kuma biya su ribar da muka ci a karshen shekara bayan sayar da zumar, sabo da mu ba kamfani ba ne, muna raba kaso 60% na ribar da muka ci ga ma'aikatanmu masu kiwon kudan zuma."

Malam Guo Xiaoli ya ce, da farkon fari, wasu manoma na damuwa kan cewa, aikin noma ne suke yi a baya, kuma ba su san yadda za su yi aikin kiwon kudan zuma ba. A game da wannan, ya musu alkawari. Ya ce, "Tun farko mun yi musu alkawarin cewa, ba sai sun damu game da fasahohin kiwon ba. Za mu gayyato masana don su horar da su. Sabo da ni ma ban iya wannan aikin ba, shi yasa muka gayyaci wadanda suka kware, kuma suka dade suna wannan aiki daga sassa daban daban na kasar, don su koya mana. Ban da wannan, mun kuma cimma yarjejeniya tare da sashen nazarin kudajen zuma na cibiyar nazarin kimiyyar noma ta kasar Sin, ta yadda idan akwai matsalolin da muka kasa daidaitawa, su za su turo mana masana don su taimaka wajen warware irin wadannan matsalolin."

Don haka, hankalin manoma ya kwanta. Malama Liu Fengping ta ce, "A ganina, akwai wanda ke mana jagora, sun kawo mana kudajen zuma, sun sa mana wannan aiki, tabbas za su taimaka mana, to, ra'ayina ke nan, shi ya sa ban damu ba ko kadan, na mai da hankali ne kawai a kan aikin kiwon kudan zuma. Idan malamai sun zo suna koya mana, ina saurara sosai, in bi yadda suka koya mana. Ban iya rubutu ba, Ina haddace abin da suka bayyana ne"

Baya ga koyar da manoma da ba su iya wannan aiki ba, horaswar da kungiyar ta samar, ta kuma taimaka ga inganta aikin kiwon kudan zuma. Malam Liu Jinguo, shi ma wani manomi ne da ya shiga kungiyar. Sai dai kafin shigarsa, ya dade yana kiwon kudan zuma, kakanninsa ma sun kasance masu kiwon kudan zuma. Ya ce, "Da farko, fasahohin gargajiya muke bi wajen kiwon kudan zuma, a maimakon fasahohi na kimiyya, matakin da ya sa yawan zumar da muke samu ba ta da yawa. Idan kuma kudajen zuma suka gamu da rashin lafiya, lalle mu ba mu san yadda za mu yi ba. Kungiyar hadin kan manoma masu kiwon kudan zuma tana samar mana kwasa-kwasai a kowace shekara, matakin da ya inganta aikinmu, baya ga kuma yawan zumar da muka samu ta karu."

Malam Liu Jinguo ya shiga kungiyar ce a shekarar 2016, a game da dalilin hakan ya bayyana cewa,"Sabo da mun amfana, kungiyar ta taimaka mana wajen sayar da zumar da muka fitar, kuma ga dalilin da ya sa muke kiwon kudan zuma shi ne, don mu sayar da zumar da muka fitar, amma a baya mu kanmu ba mu iya sayar da dukkan zumar, sabo da karancin hanyoyi na sayarwa."

Malam Liu Jinguo yana da 'ya'ya biyu, kuma daya daga cikinsu yana makaranta. Ya ce, sakamakon karuwar zumar da aka sayar, kudin shigarsa ma ya karu, lamarin da ya sa rayuwarsa ta saukaka. Ya ce, "Kudin da nake samu a kowace shekara ya karu daga yuan dubu 30 zuwa dubu 50, idan na kwatanta da lokacin da ban shiga kungiyar ba, sabo da haka kuma, rayuwata ma ta kyautata. A baya, na kan shiga matsi wajen biyan kudin makarantar yaro na, amma yanzu sauki ya samu sosai, a sakamakon yadda kungiyar ta taimaka wajen sayar da baki dayan zumar da na fitar."

Kawo yanzu, akwai magidanta kimanin 2072 da ke aikin kiwon kudan zuma a yankin Miyun, wadanda suke kiwon rukunonin kudajen zuma kimanin dubu 115, abin da ya sa yankin Miyun ya shahara a fadin kasar Sin wajen samar da zuma. Baya ga haka, aikin kiwon kudan zuma ya kuma taimaka ga bunkasa tattalin arzikin yankin, ko a bara, kudin da aka samu daga aikin samar da kayayyakin da suka shafi zuma ya kai kusan yuan miliyan 120, kwatankwacin dalar Amurka kimanin miliyan 18, tare da fitar da magidanta kimanin 362 daga kangin talauci. Malam Guo Xiaoli ya ce, gwamnatin yankin Miyun na ba da babban tallafi wajen bunkasa aikin kiwon kudan zuma a wurin, kuma kowace shekara ta kan ware kudin Sin yuan kimanin miliyan 20 ga ayyukan kiwon kudan zuma.

Ya ce, yana kuma kokarin bunkasa harkokin yawon shakatawa ta hanyar aikin kiwon kudan zuma. Ya kuma daddale yarjejeniya tare da kamfanonin samar da hidimomin yawon shakatawa, wadanda ke janyo masa baki masu yawon shakatawa daga sassa daban daban. Baya ga haka, yana kuma yunkurin kafa wani sansani na fadakar da 'yan makarantar midil, da na firamare a kan harkokin kiwon kudan zuma.

Kudajen zuma suna taka muhimmiya rawa wajen kiyaye yanayin muhallinmu, suna iya inganta tsirrai, a sa'i daya kuma, idam har yanayi ya inganta, kudajen zuma ma za su kara karuwa, wato bangarorin biyu sun kasance masu dogara ga juna.

Bisa binciken da aka gudanar, a sakamakon aikin kiwon kudan zuma, bishiyoyin yankin Miyun sun kara inganta, yanzu haka, bishiyoyi sun mamaye sama da kaso 73% na yankin Miyun. Yawan nau'o'in halittun da ke rayuwa a wurin ma ya karu.(Lubabatu)