logo

HAUSA

Hukumomin MDD da aikin noma ya shafa sun yi murnar ranar hadin gwiwar kasashe masu tasowa

2020-09-18 14:30:16 cri



A ranar 16 ga wata, kungiyar abinci da aikin gona karkashin MDD da hedkwatarsa a birnin Roma, tare da asusun raya ayyukan gona na kasa da kasa da ma Hukumar kula da abinci ta duniya sun shirya taro ta yanar gizo, don taya murnar ranar hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Mahalarta taron sun bayyana cewa, cutar numfashi ta Covid-19 da ta yadu a kusan ko ina a duniya ta haifar da munanan illoli ga tsarin samar da abinci a duniya, musamman ma kasashe masu karamin karfi, don haka, hukumomin da aikin noma ya shafa za su yi kokarin ingiza hadin gwiwar kasashe masu tasowa, don taimakawa kasashen da abin ya shafa wajen inganta tsarin samar da abinci. Ranar hadin gwiwar kasashe masu tasowa rana ce da MDD ta ware a shekarar 2003 don inganta musayar dabarun samun ci gaban kasa a tsakanin kasashe masu tasowa, domin tattauna sabbin hanyoyin hadin gwiwa. Taron da wasu hukumomi uku da aikin gona ya shafa suka gudanar a ranar 16 ga wata ya mayar da hankali musamman kan tattauna batun yin amfani da hadin gwiwar kasashe masu tasowa da kuma hadin gwiwar bangarori uku-uku, a kokarin tallafawa kasashe masu karamin karfi da kuma manoma masu karancin kudaden shiga wajen tinkarar illolin da annobar Covid-19 ta haifar ga tsarin ayyukan gona da samar da abinci. Mataimakin babban darektan asusun raya ayyukan gona na kasa da kasa, Mr. Wu Guoqi ya bayyana cewa, "Bikin murnar ranar hadin gwiwar kasashe masu tasowa da aka shirya a wannan shekara tana da ma'ana ta musamman, a daidai lokacin da annobar Covid-19 ke shafar kasashen duniya, musamman ma masu fama da talauci da kuma manoma. An kiyasta cewa, ya zuwa karshen bana, yawan al'ummar dake fama da rashin lafiya a sanadiyyar rashin samun abinci mai gina jiki zai karu daga miliyan 83 zuwa miliyan 132, a yayin da kasashe masu karamin karfi za su shiga matsi sosai ta fuskar samar da abinci. A daidai wannan lokaci kuma, ya kamata kungiyar abinci da aikin gona ta MDD da asusun raya ayyukan gona na kasa da kasa su yi kokarin tabbatar da ganin hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasuwar kasashen da kuma shiyyoyinsu." Sai kuma mataimakiyar babban darektan kungiyar abinci da aikin gona ta MDD, Beth Bechdol ta yi nuni da cewa, hadin gwiwar kasashe masu tasowa zai iya saukaka illolin da annonar ke haddasawa ga tsarin ayyukan gona daga wasu fannoni uku, ciki har da yin shawarwari a cikin shiyya ko kuma tsakanin shiyyoyi dangane da manufofi, da musayar dabaru da kuma inganta fasahohin sadarwa na zamani. Ta ce, "Za mu gano tare da raba sabbin dabarun tinkarar annobar ta fannin noma abinci, musamman ma dabarun da kasashe masu tasowa suka samar. Kasashe da yankunan al'umma da dama sun tsara sabbin dabaru da dama a yayin da suke gudanar da aikin tinkarar annobar, misali a kasar Sin, sabbin fasahohin da ake amfani da su sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da aikin samar da abinci ya gudana yadda ya kamata, inda a birnin Beijing da ma jihar Guangxi ta kasar, aka dauki dabarun sayar da ganyayen lambu tare da tura su ba tare da haduwa da juna a tsakanin al'umma ba." Kasar Sin kasancewarta tana kokarin inganta hadin gwiwar kasashe masu tasowa, wadda kuma ta dade tana tallafawa da kuma sa hannun hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta fannoni daban daban a karkashin tsarin MDD. A shekarar 2009, kasar Sin tare da kungiyar abinci da aikin gona ta MDD sun fara aiwatar da shirin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Sai kuma a shekarar 2018, bisa goyon bayan da kasar Sin ta nuna, asusun raya ayyukan gona na kasa da kasa ya kafa tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa da na hadin gwiwar bangarori uku-uku, don tallafawa kasashe masu tasowa su zuba jari da yin kirkire-kirkire da musayar fasahohi ta fannin ayyukan gona. A game da wannan, mataimakiyar babban darektan kungiyar abinci da aikin gona ta MDD, Beth Bechdol ta bayyana cewa, "Kasancewarta abokiyar hadin gwiwarmu mafi muhimmanci ta fannin hadin gwiwar kasashe masu tasowa, kasar Sin ta samar da dalar Amurka miliyan 80 wajen aiwatar da shirin hadin gwiwar kasashe masu tasowa karkashin kasar Sin da kungiyarmu. Ya zuwa yanzu, shirin ya amfanawa manoma sama da dubu 70 a fadin duniya kai tsaye, baya ga haka, masanan kasar Sin sun kuma samar da fasahohi sama da 450 ga abokan hadin gwiwarsu." (Lubabatu)