logo

HAUSA

CAF za ta shirya zabukan shugabannin ta a watan Maris na 2021

2020-09-17 17:57:55 CRI

CAF za ta shirya zabukan shugabannin ta a watan Maris na 2021


Hukumar kwallon kafar Afirka ta CAF, za ta shirya zabukan shugabannin ta a watan Maris na shekarar 2021 dake tafe, a birnin Rabat fadar mulkin kasar Morocco. Kwamitin kolin hukumar ne ya bayyana hakan, a yayin taron sa na baya bayan nan. Kaza lika kwamitin kolin ya ce, za a gabatar da jerin sunayen 'yan takarar jagorancin hukumar ga kasashe mambobin ta, a ranar 11 ga wayan Janairun shekarar mai zuwa. Ana hasashen cewa, mai yiwuwa shugaban hukumar na yanzu Ahmad Ahmad dan shekaru 61 a duniya, zai nemi tazarce na karin shekaru 4 a karo na biyu. A shekarar 2016 ne dai Ahmad ya kada tsohon shugaban hukumar ta CAF Issa Hayatou, yayin zaben da ya gabata, bayan Issa Hayatou ya shafe shekaru 29 yana jagorancin hukumar. Yayin zaben jagororin hukumar ta CAF, za a zabi shugaba, da mambobin hukumar zartaswar hukumar kamar yadda dokokin ta suka tanada.

Neymar ya warke daga COVID-19

Dan wasan gaban kungiyar Paris Saint-Germain ta kasar Faransa Neymar, ya bayyana cewa, ya warke daga cutar COVID-19 da ya kamu da ita, yana kuma matukar farin ciki da komawa atisaye, bayan fita daga wurin da ya killace kan sa. Dan wasan mai shekaru 28, na cikin 'yan wasa 7 da a baya bayan nan aka tabbatar sun harbu da wannan cuta a PSG. Sauran sun hada da Kylian Mbappe, da Mauro Icardi, da Angel Di Maria, da Leandro Paredes, da Keylor Navas da kuma Marquinhos. Neymar dan asalin kasar Brazil, ya wallafa sakon nuna farin cikin sa a shafinsa na Twitter, yana mai cewa "Na fita daga COVID". Rashin fitowar Neymar a wasan da PSG ta buga da kungiyar Lens a karshen makon jiya ya raunana karfin PSGn, inda Lens ta doke ta da ci daya mai ban haushi, duk kuwa da cewa a wannan shekara ne, kungiyar ta Lens ta samu damar farko ta fara buga gasar ajin kwararru ta zakarun kwallon kafar kasar ta Faransa. Rashin wadannan 'yan wasa da suka sha fama da cutar COVID-19 da PSG ta yi, ya tilasa kocin kungiyar Thomas Tuchel sanya kananan 'yan wasan sa, irin su Kays Ruiz-Atil mai shekaru 18 da haihuwa, da Arnaud Kalimuendo, da mai tsaron raga Marcin Bulka mai shekaru dan shekaru 20. Kaza lika PSGn ta bayyana sake dawo da dan wasan ta Alessandro Florenzi, karkashin kwangilar shekara daya daga kulaf din Roma na kasar Italiya, kungiyar ta kuma ce tana da madadin sa, lokacin da kwangilar sa za ta kare a karshen kakar wasa ta badi. 'Yan wasan PSG karkashin kocin su Tuchel, suna da jan aiki a wasannin su na makon nan, inda aka tsara karawar su da kungiyar Marseille, wadda a kakar da aka gama ta zamo ta biyu, sai kuma wasan su da Metz a "Parc des Princes" a ranar Laraba.

Kungiyar Black Starlets ta Ghana ta gayyaci 'yan wasa 40 zuwa sansanin ta

Hukumar kwallon kafar Ghana, ta ce an gayyaci matasan 'yan wasan kwallon kafar kasar masu buga gasannin kasa da shekaru 17 har su 40, karkashin tawagar kungiyar kasar ta "Black Starlets". 'Yan wasan za su shiga sansanin ba da horo tun daga ran 15 ga watan Satumbar nan, don fara atisayen tinkarar manyan wasannin kasa da kasa dake tafe. Hukumar ta GFA ta kara da cewa, dukkanin jami'an dake tallafawa 'yan wasa wajen samun horo, da sauran ma'aikata dake samar da hidimomi masu muhimmanci ga 'yan wasan, za su yi gwajin cutar COVID-19 da zarar sun isa sansanin horon. Da yake karin haske kan hakan, shugaban GFA ya ce shugaban Ghana Nana Addo Akufo-Addo, ya ba da umarnin baiwa matasan 'yan kwallon kasar maza da mata, masu buga gasannin kasa da shekaru 17 da 20 damar komawa sansanin horo, don tunkarar wasannin kasa da kasa dake tafe. To sai dai kuma, sakamakon gwajin da aka yiwa 'yan wasan, ya nuna cewa 7 daga cikin su na dauke da cutar COVID-19, an kuma tabbatar da harbuwar su, 'yan kwanaki kadan bayan isar su sansanin.

A halin yanzu dai, ana ci gaba da aiwatar da umarnin shugaban kasar ta Ghana, game da dakatar da harkokin wasanni, don dakile yaduwar COVID-19, duk da cewa yawan yaduwar cutar ya yi matukar raguwa a kasar dake yammacin Afirka.