logo

HAUSA

Yariniyar dake kokarin cimma burinta na zama malama

2020-09-07 19:38:04 CRI

 

 

Xiao Qiu, yariniya ce da ta fito daga wani karamin kauye dake gundumar Jianchang ta birnin Huludao na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin. A yayin da ta kai shekaru 12, ta gamu da wata nakasa a habanta Da farko dai ta fara jin ciwon hakori ne, amma saboda iyalinta na fama da talauci, don haka ba su da kudi da za su yi mata jinya, sai ta yi amfani da hakoranta na bangare daya a yayin da take cin abinci, a sakamakon haka, ba da dadewa ba fuskarta ta kumbura, kunci da habarta duk suke murde, hakan ya sa fuskarta ta canja kama, sannu a hankali matsalar ta kara tsananta, ta yadda hakan ya mata tasiri sosai wajen cin abinci da ma yin magana a yau da kullum.

A shekarar 2013, wato a yayin da Xiao Qiu ke yin karatu a makarantar midil, mahaifiyarta ta mutu sakamakon ciwon sankara, bayan shekaru uku kuma, mahaifinta shi ma ya mutu a wani hadarin mota. Ko shakka babu, halin da Xiao Qiu take ya kara tsananta, amma duk da haka, tana cike da fatan na gari kan makomar zaman rayuwarta a nan gaba. A shekarar 2016, Xiao Qiu ta ci jarrabawar shiga wata kwalejin koyar da malamai, daga baya kuma ta kammala karatunta a makarantar da maki mai kyau. A yayin da take karatu da kuma yin aikin gwaji, Xiao Qiu ta kara imaninta na zama malama.

 

 

"A yayin da nake yin mu'ammala da yara a lokacin da nake yin aikin gwaji, na gano cewa, yara suna da kirki, ina jin farin ciki yayin da nake tare da su, hakan ya sa na kara fatan da nake da shi na zama malama." Amma, bayan ta kammala karatu, ta yi ta gamu da matsaloli a kokarin cimma wannan buri nata, sakamakon matsalar fuskarta. Bisa ka'ida, bai dace ba wanda ya kamu da cutar nakasar fuska ya yi aikin koyarwa, don haka, Xiao Qiu ba ta ci jarrabawar zama malama ba, a don haka, ba za ta samu aikin koyarwa ba. "Na ci jarrabawar da ake rubutawa ta zama malama, amma ba a yi nasara a intabiyu ba saboda yanayin fuska ta, na sha yin wannan jarrabawar, amma duk ban yi nasara ba."

 

A yayin da take fuskantar wadannan matsalolin, Xiao Qiu ba ta yi watsi da burinta na zama malama ba, kuma ta yi ta kokarin cimma burinta ta hanyar da take so, kamar kafa ajin samar da horo kyauta a kauyensu, don taimakawa yaran dake zaune a kauyen wajen samun horo a fannin karatu.

"Bayan yaran sun tashi daga makaranta ko kuma yayin da suke hutu, za su iya zuwa ajin, idan akwai abubuwan da ba su iya ba game da aikin gida, ko kuma ba su fahimta ba a yayin da ake koyar da su, sai na nuna musu."

Irin wannan aiki da Xiao Qiu ta ke yi, ya sanya mazauna kauyen kara tausaya mata, har ma sun tattara kudi yuan dubu biyar don taimaka mata wajen samun jinya. Amma, aikin da za a yi wa Xiao Qiu, yana bukatar fasaha mai inganci sosai, kuma akwai babban hadari, yawancin likitoci ba su da tabbas kan nasarar wannan aiki ko da an yi, ban da wannan kuma, ana bukatar kudade masu yawa domin samun jinya.

 

 

A yayin da wani mai aikin sa kai da ya shahara a nan kasar Sin, Guo Mingyi ya ji labarin Xiao Qiu, sai ya tsaida kudurin taimaka mata. Bayan ya fahimci cewa, za a iya gyara fuskar Xiao Qiu ta hanyar yi mata tiyata, nan da nan ya tattauna da wani babban asibiti da ya kware a wannan fanni, kana kuma ya biya dukkan kudaden da ake bukata na wannan aiki

A karshen watan Yuni na bana, aka yiwa Xiao Qiu aiki a fuskarta, kuma a farkon watan Agusta, Xiao Qiu ta yi nasara, aikin ya yi kyau, har ma aka sallame ta daga asibiti.

"A da, ina jin tsoro wasu su ga fuska ta, idan ina tafiya, kullum kai na a sunkuye, amma yanzu kaina a sama idan ina tafiya. Ina farin ciki sosai."

 

 

A watan Yuni, Guo Mingyi da kungiyarta ta aikin sa kai sun isa makarantar sakandare ta biyu na birnin Naqu na birnin Lhasa na jihar Tibet ta kasar Sin, don ba da tallafin kudi ga dalibai masu fama da talauci dake makarantar, inda ya kuma bayyana labarin Xiao Qiu. Shugabannin makarantar sun bayyana fatansu na ganin Xiao Qiu don ta ba da horo ga dalibai masu fama da talauci guda 50 a lokacin hutu. Yanzu, Xiao Qiu ta shirya rubuta jarrabawar samun iznin zama malama, domin cimma burinta na zama malama.

"Ban taba tunanin halin da nake ciki zai kyautatu kamar haka ba, ina godiya sosai da taimakon da kawu Guo da kungiyarsa suka ba ni, sun sauya rayuwa ta."

Yariniyar dake kokarin cimma burinta na zama malama

 

Xiao Qiu ta gaya mana cewa, ta ki amsa gayyatar da wasu makarantun a manyan birane kamar su Beijing, Shanghai da dai sauransu suka yi mata, na daukar ta aiki a makarantun, ta ce, za ta yi aikin koyarwa a kauye, domin taimakawa yara da dama, fita daga yankuna masu tsaunuka, ta fi so ta koyar da yara kyauta a yankuna masu fama da talauci, don yada irin kaunar da aka nuna mata ga yaran dake irin wadannan wuraren."