logo

HAUSA

Xi Jinping: Ya kamata a gada ruhin yakin kin jinin harin Japanawa a sabon zamani don farfado da al'ummar Sinawa

2020-09-04 14:14:11 cri

Jiya Alhamis, kwamitin tsakiyar JKS, da majalisar gudanarwa, da ma kwamitin tsakiya mai kula da harkokin sojan kasar Sin, suka kira wani taro a babban dakin taron jama'a, na tunawa da cika shekaru 75 da samun nasarar yakin harin Japanawa, da ma yakin kin tafarkin murdiya.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron inda kuma ya gabatar da jawabi. Cikin jawabin sa, shugaba Xi ya jaddada cewa, an fitar da wani muhimmin ruhi yayin ake kokarin tinkarar harin Japan, abin da ya bayyanawa dukkanin duniya cewa, duk wani basine na kaunar kasa, zai sadaukar da ransu don kare kasar, duk da kalubaloli masu dimbin yawa da aka fuskanta.

Ya ce irin wannan ruhi, ya zama wadata mai muhimmanci ga al'ummar Sinawa, zai kuma karawa Sinawa kwarin gwiwa, da sanyawa musu kuzari wajen tinkarar duk wani kalubale da matsala, don samun farfadowar al'ummar Sinawa.

Zaunannun mambobin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS Li Keqiang, da Li Zhanshu, da Wang Yang sun halarci taron, inda Wang Huning ya jagoranci taron.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, an yi wannan gaggarumin biki ne don tunawa da cika shekaru 75, da samun nasarar yakin kin jinin harin Japanawa, da ma yakin kin tafarkin murdiya. A shekaru 75 da suka gabata, jama'ar kasar Sin sun hada kai da jama'ar duniya, don tinkarar 'yan mulkin danniya, sun kuma cimma nasara, kuma Sinawa sun kwashe shekaru 14 suna yin iyakacin kokarin tinkarar harin Japanawa ba tare da jin tsoro, ko ja da baya ba.

Wannan yaki dai ya kasance mafi tsawon lokaci, kuma mafi girma, kana mafi haifar da asara a zamanin baya bayan nan. Shi ne kuma karon farko da aka kwaci 'yancin kan al'umma a dukkanin fannoni a duniya. Matakin da ya zama wani sauyi ga al'ummar Sinawa, tun lokacin da ta wasu manyan kalubale suka dabaibaye kasar, suka kuma jefa su cikin mawuyacin hali.

Kaza lika muhimmin kashi ne daga cikin yakin kin tafarkin murdiya. Nasarar da Sinawa suka samu, da ma nasarar dukkanin Bil Adama baki daya, abubuwa ne da ba za a taba mantawa da su ba. Shugaba Xi ya ce:

"A madadin kwamitin tsakiyar JKS, da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da ma majalisar gudanarwa, da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, da kwamitin tsakiya mai kula da harkokin sojan kasa, ina matukar maraba, da girmamawa ga wadanda suka shiga wannan yaki, da ma Sinawa a gida da na ketare, wadanda suka bayar da babbar gudunmawa a wannan yaki. Kuma ina godiya ga taimakon da sauran gwamnatoci, da masu sada zumunta na kasa da kasa suka bayar. Ina kuma jajantawa, da nuna alhini ga wadanda suka sadaukar da rayukansu a wannan yaki."

Shugaba Xi ya nuna cewa, nasarar da Sinawa suka samu a wannan fanni, ta murkushe makarkashiyyar masu ra'ayin nuna karfin soja, don gudanar da mulkin mallaka a kasar Sin, da ma kiyaye ikon mulki da cikakken 'yancin kasar. Har ma ya sake tabbatar da matsayin Sin na wata babbar kasa a duniya. Kuma jama'ar duniya masu kaunar zaman lafiya, suna matukar girmama Sinawa. Kazalika, wannan nasara ta aza tubali ga al'ummar Sinawa, na neman samun 'yanci, da farfadowar al'umma.

Ban da wannan kuma, Xi ya jaddada cewa, Sin da Japan makwabta juna ne, kuma abokan juna. Don haka raya dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata a dogon lokaci, ya dace da muradun jama'ar kasashen biyu, da ma ba da tabbaci ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin shiyyar su, da ma dukkanin duniya baki daya.

Ya ce daidaita ra'ayi game da harin da Japan ta aiwatar, tushe ne mai muhimmanci na siyasa, don raya dangantakarsu yadda ya kamata. Muna tunawa da wannan yaki, don mun koyi darasi daga cikinsa, na kokarin shimfida zaman lafiya a nan gaba, ta yadda al'umomin kasashen biyu za su sada zumunta daga zuriya zuwa zuriya, da ma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya.

Haka zalika, Shugaba Xi ya jaddada cewa, a cikin wadannan shekaru 75 da suka gabata, Sin ta samu matukar sauyi dake jawo hankalin duniya. Ya ce Sin ta bullo da hanyar tsarin mulki na gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, da ma kokarin kawar da talauci da raya al'umma mai wadata, matakan da suke samar da makoma mai kyau wajen farfado da al'ummar Sinawa. Ya ce:

"Duk yunkurin da za a yi na jirkata tarihin JKS ba zai cimma nasara ba, kuma duk wani karfi dake neman murgude, da sauya hanyar da Sin take bi, da ma musanta nasarorin da Sinawa suka samu, zai ci karo da rashin yardarm Sinawa. Kuma ba wanda zai raba JKS da jama'arta, ba wanda zai tsoma baki cikin harkokin kasar Sin, ba wanda zai dakatar da bunkasuwar kasar Sin ko kadan. Babu wanda zai iya hana mu'ammalar Sinawa da sauran al'umomin ketare, da ma kokarinsu na neman samun zaman rayuwa mai wadata. Duk wadannan matakai ne da Sinawa ba za su amince da su ba."