logo

HAUSA

"Ice ribbon" filin wasan zamiyar kankara na gasar Olympic mai zuwa dake birnin Beijing

2020-09-03 15:44:40 CRI

"Ice ribbon" filin wasan zamiyar kankara na gasar Olympic mai zuwa dake birnin Beijing


Zuwa tsakiyar lokacin zafi, ana iya hangen katafaren filin da aka tanada, musamman domin gasar Olympic na lokacin sanyi, wanda ake fatan gudanarwa a yammacin birnin Beijing. A wannan fili ne kuma aka gina zauren wasan kankara na "skating" wanda aka yiwa lakabi da "Ice ribbon" a turance, zauren dake daura da babban filin wasan nan mai suffar shekar tsuntsu, da na wasan ruwa dake wannan birnin, matakin da ya baiwa birnin Beijing wani matsayi na kasancewa na farko a duniya, dake da irin wadannan filaye na wasan Olympic na lokacin zafi da na sanyi. Shaidun gani da ido sun ce, ginin zauren wurin wasan zamiyar zuwa katangar sa, na dauke da sassan gilasai 3,360, wadanda suka samar da wasu zobba 22 da ake iya sarrafawa masu matukar ban sha'awa, wadanda kuma suka ba da suffar sawun waurin zamiya a kan kankara, alama mai ma'ana dake nuna karsashin saurin tafiya da 'yan wasan kankara ke yi. An dai sanyawa zauren sunan "ice ribbon", suna mai gamsarwa da zai dace da nishadantarwar da wasan ke bayarwa. A cikin filin wasan kuwa, ma'aikata na aikin shinfida kasan ramin kankara. Wuri ne da ake sa ran amfani da shi, wajen horas da 'yan wasan zamiyar kankara masu sauri a lokacin gasar ta Olympics. Bayan wucewar gasar ta lokacin sanyi kuma, zai zama sabon zauren wasanni na birnin Beijing dake da kankara da dusar kankara, mai alamta manufar kasar Sin ta raya wasannin motsa jiki, da amfana daga kayayyaki, da hidimomin da wasannin ke samarwa Babbar na'urar zamani da aka girke a zauren na " ice ribbon ", mai samar da kankara a ko da yaushe, don biyan bukatun masu shiga gasar dake tafe, ita ce makamin sirri ga nasarar manufar da aka sanya gaba, kamar dai yadda daraktan tsara aikin samar da filin, Ma Jin ya bayyanawa manema labarai. Ma Jin ya kara da cewa, na'urar za ta biya bukatu daban daban na nau'oin wasannin kankara da za a gudanar a filin. Jami'in ya kara da cewa, wannan na'ura, baya ga kankara da za ta rika samarwa bisa madaidaicin yanayi na fasaha ga masu fafatawa a gasar Olympic ta lokacin na sanyi, a hannu guda kuma, za ta rika amfani da zafin da take fitarwa wajen dumama iskar dake kewayen zauren, da kuma kyautata yanayin kankarar wurin, da samar da ruwan zafi da za a bukata a wurin, da ma sarrafa sauran na'urori masu fasahar zamani da za a yi amfani da su a filin. An ce idan ana cikakken amfani da na'urar yadda ya kamata, sashen ta na samar da sanyi kadai, zai iya tsumin karfin wutar lantarki da yawan ta ya kai sama da kilowat miliyan 2 a shekara guda. A cewar Song Jiafeng, mataimakin babban manajan hukumar gudanarwar kamfanin dake lura da wannan filin wasa na zamiyar kankara, wannan dabara ta kula da zauren kankarar yana da tsari mai dorewa, inda aka tsara zauren, ta yadda sassa daban daban za su amfana daga fasahohi mabanbanta da aka tanada, gwargwadon bukatar wasannin da za a rika yi a zauren. Song Jiafeng ya ce, a lokuta na gama gari, zauren na iya daukar bakuncin sama da mutane 2000 don wasan Hockey (Gora) na kankara, da masu wasan zamiya ta takalma, da ta alluna, da wasannin "curling (wasan kwallon kankara na hannu) da dai sauran su.

A daura da wannan zaure, akwai filin wasan ruwa, wanda aka yi amfani da shi yayin gasar lokacin zafi ta birnin Beijing a shekarar 2008. A can ne kuma, ake sa ran gudanar da gasar wannin "Curling", da "Curling na kan keken guragu a gasar 2022 mai zuwa, bayan yiwa filin kwaskwarima, don dacewa da bukatun wasannin lokacin sanyi.