logo

HAUSA

Matakan kasar Sin na kara raya jihar Tibet

2020-09-02 16:51:06 CRI

A kwanakin baya ne, kwamitin koli na JKS, ya shirya wani taron karawa juna sani kan batun bunkasa jihar Tibet. A yayin wannan taro, inda aka jaddada muhimmancin aiwatar da cikakkun manufofin jam'iyyar JKS mai mulkin kasar kan sha'anin shugabancin jahar Tibet a sabon zamanin da muke ciki.

Matakan kasar Sin na kara raya jihar Tibet

Taron wanda babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kasar ta Sin Xi Jinping ya jagoranta, ya kuma bukaci a kara himma don tabbatar da tsaron kasa, da tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali, da inganta zaman rayuwar al'umma, da samar da ingantaccen yanayi, da samar da kyakkyawan tsarin tsaron kan iyakokin kasar da nufin tabbatar da tsaro.

Muddin ana son cimma wannan buri, da ma sauran muhimman manufofin da aka tsara kan jihar ta Tibet, tilas ne a yi kokarin gina sabon tsarin gurguzu a jihar a kokarin da ake na dunkulewar jihar, da samun ci gaba, da bunkasa al'adu, da samar da zaman lafiya da kayata yankunanta.

Matakan kasar Sin na kara raya jihar Tibet

Yanzu haka, gwamnatin kasar Sin ta yi nasarar gina layin dogo zuwa jihar da a baya ke da wahalar shiga, musamman ga masu sha'awar yawon bude ido. Masu fashin baki na cewa, inganta shugabancin jihar bisa tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, zai kara bunkasa jihar, matakin da zai kara taka rawa wajen dunkulewar kasar Sin baki daya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)