logo

HAUSA

Tsarin motsawa da yaki da annoba da matasan Sinawa suke yi

2020-09-01 08:42:23 CRI

Tsarin motsawa da yaki da annoba da matasan Sinawa suke yi

Yayin da ake ci gaba da yaki da annobar cutar COVID-19, ya zama dole dalibai su kasance a gida, amma da yawa daga birane dake kasar Sin sun fara komawa gudanar da ajujuwan su ta yanar gizo, wanda hakan ka iya haifar da rauni ga lafiyar idanun dalibai, Wannan yanayi na "ZAMA" tsawon lokaci a gida, na iya sanyawa jiki ya yi rauni. Don haka, wajibi ne a ci gaba da motsa jiki sosai. A daya bangaren kuma, yayin da a baya ake ware lokacin motsa jiki wato sa'a guda a makaranta, yanzu ma lokacin da ake zaune a gida akwai bukatar ware lokaci sama da hakan domin motsa jiki.

To sai dai kuma dabarun karfafa gwiwar dalibai su rika motsa jiki shi ne abun lura. Wannan ita ce matsalar, duba da cewa, a hannu guda, karsashin dalibai da daman a motsa jiki ba shi da yawa, kuma a gida, tsarin sa ido don ganin suna motsa jiki ba shi da karfi, da yawa daga dalibai za su yi zaman dirshan, ga kuma matsalar karancin kayan motsa jikin, a daya ahannun kuma, malamai ba su da zarafin aiwatar da matakan lura da wannan fanni. A halin yanzu, da yawa daga malamai na amfani ne da tsarin auna lokaci, hakan ko shakka ba bu yana da fa'ida, amma idan kuma idan lokaci ya yi tsawo, dalabai za su gaji da tsarin, ga shi kuma zai yi wuya ma a iya auna ainihin tasirin motsa jiki a irin wannan yanayi. Ko da kuwa malamin aji ya bukaci dalibai su dora bidiyon motsa jiki da suka yi ta yanar gizo, abu ne mai wuya a iya magance yanayin rashin sha'awar motsa jikin daga bangaren dalibai. Hutun lokacin sanyi na bana ya yi matukar tsawo sama da kima. Dalibai sun kashe lokaci mai yawa suna tare da wayoyin su na salula da kwamfutocin su. Don haka dai, ya wajaba dalibai su rika motsa jiki sosai, in ba haka ba, wasu daga cikin su za su yi kiba, ta yadda zai musu wuya su iya yin gudu bayan kawo karshen wannan annoba. Akwai dai makarantu da dama, da kuma malamai masu yawa dake bullo da na su dabarun zaburar da dalibai su shiga motsa jiki sosai, amma wata hanya mai inganci ta yin hakan ita ce hada gasanni ta yanar gizo don samun sakamako mai armashi. Wani bidiyon mutane masu shiga irin wannan tsari su 40,000 ya shaida tasirin hakan.

Tsarin motsawa da yaki da annoba da matasan Sinawa suke yi

Dalilin da ya sa wannan tsari ke da tasiri wajen zaburar da daliban shi ne, ana yin wasannin ne kai tsaye ta yanar gizo, kana bisa sanya ido na malamin aji, akwai cudanya da juna tsakanin daliban da malaman su, ta yadda banbancin dake tsakanin irin wannan wasa da wanda ake yi a zahiri ba shi da yawa. Kaza lika ana iya fitar da zakarun wasa, yayin da sauran dalibai ke da damar kallon yadda wasan ke gudana. Dalibai sun fi jin dadi idan sun shiga an yi da su, kuma shigar malamai wasannin motsa jikin na kara musu kuzari yadda ya kamata.

Irin wadannan nau'oin wasanni na hadaka, ba lallai sai an gudanar da su karkashin tsarin makarantu ba, wato dai za su iya gudana karkashin tsari na ajujuwa, muddin dai hakan zai ba da dama ga dalibai su shiga a yi da su cikin nishadi da tsaro, kuma za su gudana ta hanya mai sauki da za a iya samu. Kana akwai batun yanayin tafiyar da su, wato yadda dalibai za su so shiga, su kuma iya gudanar da wasannin a gida. Dalibai masu karatu a cikin kasa da kuma na waje, sun shaida cewa kananan yara da matasa dake motsa jiki a kalla tsawon sa'a guda a kullum na samun kyakkyawan yanayin lafiyar jiki. Kaza lika masana a fannin ilimi da dama na ba da shawarar cewa, "Zama a gida", na sawa a kasa mayar da hankali ga batun koyon ilimi, don haka dabara a nan ita cewa zaburar da zukatan dalibai, ta hanyar shigar su wasanni, wanda ke motsa zukatansu, matakin da ko shakka ba bu ke da matukar tasiri. Rayuwa na danganta da wasanni, kuma zama a gida kawai ba ya hana wasanni gudana. Ga shi kuma yanayin gudanar da wasanni ta kafofin sadarwa na ba da damar rage wahalhalun shirya wasan, da rage lokacin gudanarwa. Akwai shirye shirye da dama irin su "Healthy Qinghai", da "fitness and anti-epidemic", da "home aerobics"...wadanda suka ja hankali matuka. Wadannan shirye shirye da suke wakana yayin da ake yaki da COVID-19 sun kasance abubuwan tattaunawa a fannin wasanni a lardin Qinghai. Ya zuwa yanzu, akwai kusan mutane 10,000 da suka shiga wadannan shirye shirye inda aka kalli bidiyo da aka dora game da su sau sama da miliyan 10. Rukunonin gudanar da wasanni ta gida da dabarun motsa jiki a gida sun zama ruwan dare tsakanin al'ummun Qinghai a wannan lokaci da ake yaki da COVID-19. A yanzu haka akwai dubban rukunonin wasanni da masu horasawa dake jagorantar wannan fanni ta hanyoyin kimiyya. A kowace safiya, Li Yuming na farawa ne da yin wanka, sannan ya dan ji kida a cikin dakin kwanan sa, sai kuma ya dauki bidiyon wasu 'yan bidiyo na motsa jiki da yake yi da kan sa, sannan ya shiga tattaunawar da ake yi game da shirin "Healthy Qinghai", shirin motsa jiki da yaki da wannan annoba, yana kuma raba batutuwan da sauran mutane ta kafar sada zumunta ta Douyin. A matsayin sa na mai horaswa a fannin wasanni ta dandalin zumunta, Li Yuming yana samar da bidiyon ayyukan motsa jiki da ya gudanar da kan sa a yayin atisaye da dama da hukumar wasanni ta lardin Qinghai ke daukar nauyi. Da yake tsokaci game da hakan, Li Yuming ya ce "A matsayi na na mai ba da horo a dandalin sadarwa, ina da wasu manyan hanyoyin ba da horon motsa jiki a gida". "Game da tsarin motsa jiki na hukumar wasannin lardin Qinghai kuwa, na bude wani fejin yanar gizo, na horas da mutane yayin da ake fama da wannan annoba, ya zuwa yanzu na fitar da bidiyo sama da 10 na motsa jiki a gida, da ma wasu bayanai na karantawa 10 da wadanda suka samu alamun yabo sama da 30,000, wanda hakan ya sa na ji matukar gamsuwa. Tun daga 10 ga watan Fabarairu, lokacin da hukumar wasanni ta Qinghai ta fitar da shirin yayata manufar "Motsa jiki ta kasa yayin yaki da annobar COVID-19 ", kungiyoyin wasanni, da kulaflikan wasanni, da kwararru a fannin da ma masu ba da horo a fannin wasanni na dukkanin matakai dake wannan lardi na Qinghai, sun shiga wannan aiki, kuma kusan masu horaswa a fannin wasanni ta yanar gizo 1,000 sun rungumi wannan aiki. Darakta mai lura da harkokin wasannin jama'a da dama na hukumar wasannin Qinghai Guo Quancai, ya bayyana cewa, shirin samar da horon motsa jiki ta yanar gizo a gida, ya taka muhimmiyar rawa wajen yayata wasanni masu hada da gasa. Baya ga damar raya wasanni ta hanyoyin komiyya ga masu sha'awa a Qinghai, a hannu guda hakan ya samar da dama ta yaki da wannan annoba ta COVID-19 da ake fama da ita. Tsakanin masu shiga a dama da su a wasannin na kasa baki daya zuwa masu samun alfanun motsa jiki an samu maku kallon bidiyon har sama da mutum miliyan 10 Kamar dai sauran masu ba da horo ta yanar gizo daga gida, a kullum Zhang Chunxiu tana dora bidiyon aikin ta na motsa jiki a gida mai taken "Al'ummar Qinghai mai cike da koshin lafiya, motsawa da yaki da annoba " a kan shafin manhajar Douyin. Amma banbanci da na sauran shi ne Zhang tana koyar da motsa jikin kuma tana koya ita ma. Yayin zantawa da manema labarai, Zhang Chunxiu ta ce "A matsayi na na mai sha'awarar motsa jiki, a baya na kan yi wasannin motsa jikin a waje kamar tafiyar kasa, gudu da raye rayen dandali. Amma lokacin da wannan annoba ta barke ba na iya fita waje, don haka na kan karanta darussa a yanar gizo na kuma shiga a dama da ni. Ban taba zaton akwai kwararru da dama a wannan fanni dake koyarwa haka ba".Ta ce "Yanzu haka na fi maida hankali ga bidiyon da masu ba da hoto na cibiyar motsa jiki ta Xining ke dorawa a yanar gizo. Ina koyo na rika maimaitawa bayan sun dora na su bidiyon a kullum, wanda hakan ya taimaka min matuka. Game da hakan, Mr. Guo ya ce "Ya zuwa yanzu, yawan bidiyon da aka dora a yanar gizo bisa taken "Al'ummar Qinghai mai cike da koshin lafiya, motsawa da yaki da annoba" sun kusa 1,000, kuma yawan mutanen da suka kalle su yah aura miliyan 10, wanda hakan ke nuni ga sha'awar al'umma game da shiga a dama da su. Ya ce za mu ci gaba da zaburar da mutane ta yadda za su shiga harkokin motsa jiki ta hanyoyin kimiyya, da nishadi da hanyoyi masu sauki na koyo, za mu rika gudanar da gasanni iri-iri na jama'a da dama ta yanar gizo, ta yadda jama'a za su kara gane dabarun kimiyya na motsa jiki da samun kariyar garkuwar jiki da karin lafiya. Rahotanni na cewa, gangamin yayata shirin "Al'ummar Qinghai mai cike da koshin lafiya, motsawa da yaki da annoba" ta yanar gizo an kawo karshe a ranar 8 ga watan Maris, mutane da dama wadanda suke da sha'awa sun bi ta manhajar douyin su rika binciko darussa masu nasaba da shirin domin ci gaba da amfana da shi. Bayan kammalar shirin, an zabi bidiyo mafiya samun yabo don ba su shidar martabawa ta motsa jiki, da kayan sakawa da kyaututtuka na yabo.

A gabar da ake yaki da annobar COVID-19, akwai wani karfi da ake cewa Wasanni. Mu shiga a dama da mu, mu yi himma tare don samun karfin jiki da kuzarin yakar wannan annoba.