logo

HAUSA

SAURA SHEKARA GUDA A BUDE GASAR JAMI'OI TA KASA DA KASA KARO NA 31

2020-09-01 08:48:09 CRI

Nan da kusan shekara guda ne ake fatan gudanar da bikin bude gasar wasannin jami'oi na duniya na lokacin zafi karo na 31. Bisa tsarin gasar wadda za ta gudana a birnin Chendu na lardin Sichuan, dalibai daga jami'oin duniya daban daban, za su hallara domin shiga wasanni daban daban na motsa jiki, tare da musayar al'adu na kasashe daban daban. Hukumar shirya gasar ta bayyana ranar 18 ga watan Agusta na shekarar 2021 a matsayin ranar bude wannan gasa, wadda a karon farko za ta gudana a yammacin kasar Sin. Birnin Chengdu ya gabatar da katunan gayyata guda 212, dauke da yaren Turanci da Sinanci, domin fara kidayar shekara gabanin bude gasar dake tafe. Birnin Chengdu na maraba da zuwan abokai daga dukkanin sassan duniya domin shiga wannan muhimmiyar gasa. Tuni kuma aka gabatar da manyan daraktocin bikin budewa da rufe wannan gasa a hukumance. Kaza lika an zabi babbar dabbar Panda mai suna Sesame dake cibiyar bincike da reno, da kyautata rayuwar dabbar Panda, a matsayin dabbar da za ta alamta wannan gasa. Cike da kuzari da kyan gani, tana hawa da sauka bishiyoyi, Sesame mai shekaru uku da haihuwa ta samu wannan karramawa ne a ranar 19 ga watan Agustan nan. An yi zanen wannan Panda wanda aka sanyawa suna "Rong Bao", wanda ke rike da fitilar wuta ta wannan gasa dauke da lamba "31" ta wuta, kuma idanun zanen, da kunnuwan sa, da jelar zanen duk na wuta ne. Sesame, na matsayi tsakanin yarinta da girma, wanda hakan ke daidai da lokacin kasancewar dan Adam matashi. Wannan Panda na cike da kuzari da jin karfin jiki, Wanda hakan ke baiwa wannan alama ta gasa wani karsashi na musamman, kamar yadda "Zhang Xiaohui, wani jami'i a ofishin gudanarwa na wannan cibiya ta birnin Chengdu. Mutane na matukar kaunar wannan babbar Panda. Sunan sa ya dace da kimar kasar Sin da manufarta, ta bunkasa al'adun Sin na Bashu. Yayin da wannan gasa karo na 31 ke karatowa, Sesame zai ci gaba da nunawa masu sha'awa kyawun sa ta kafar dandalin yanar gizo. Baya ga samar da alamar gasar, bikin budewa da rufe gasar jami'oin, za ta nunawa duniya tsarin birnin Chengdu da halayyar musamman ta birnin, wanda hakan shi ma ya ja hankali matuka. Da yammacin 18 ga watan Agustar nan, aka kaddamar da daraktocin bikin budewa da rufe wannan gasa dake tafe a hukumance. Jami'ai biyu masu kwarewa a fannin gudanar da bikin budewa da rufe gasanni ne aka dorawa wannan nauyi. Chen Weiya shi ne daraktan da zai jagoranci bikin bude gasar, kana Jia Ding, zai jagoranci bikin rufe gasar. Wani rahoto ya nuna cewa, za a yi amfani da na'urorin fasahar sadarwa ta zamani kamar fasahar 5G da makamantan su, da kyawawan al'adun Chengdu kamar tsuntsuwa mai daraja, da babbar dabbar Panda, da wasan kwaikwayo na birnin Sichuan, da abubuwa na al'adu masu nasaba da birnin, kamar Sanxingdui da Jiuzhaigou, da bukukuwa biyu na matasa masu salo na kasa da kasa, har da ma salon wasan Sin na Bashu wanda zai kayatar da masu kallo da sauraro. Wannan gasa na tattara 'yan wasan motsa jiki daga jami'oi daban daban. A cewar daraktan bikin bude gasar Mr. Chen, burin su shi ne haskawa duniya irin karsashi da matasa ke da shi, ta yadda sauran dalibai dake sassan duniya daban daban, za su ji banbancin birnin Chengdu, da ma Sin da sauran yankunan duniya. Ya ce "Fata na shi ne dukkanin wanda ya dandana yanayin wannan gasa a birnin mu, ba zai taba mantawa da yanayin wannan gasa ta Chengdu ba". Tuni dai aka kammala ginin sabbin filayen wasanni 13 a birnin. A ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2019, yayin taron kwamitin manyan jami'ai na hukumar shirya wasannin jami'oi na kasa da kasa a Krasnoyarsk, dake kasar Rasha, aka zabi birnin Chengdu a matsayin wurin da gasar ta shekara mai zuwa za ta gudana. Daga wancan lokaci zuwa lokacin bude gasar, wato kimanin shekaru biyu da rabi, ba bu isasshen lokaci mai yawa na gine gine, amma duk da haka a ganin mataimakin minista a kwamitin shirya wannan gasa Tang Chongmin, daukacin masu aikin gine ginen wuraren wasannin da za a gudanar sun san nauyin dake wuyan su na gaggauta kammala ayyukan su bisa tsari. A filin wasanni na Donganhu dake Chengdu, inda a nan ne za a gudanar da bikin bude gasar, an riga an kammala ayyuka, inda ake iya ganin fuskar filin mai launin azurfa cike da fasahohin zamani. Kaza lika domin karbar bakuncin wannan gasa karo na 31, birnin chengdu ya gina ko gyara wurare 49. A yanzu haka ma, dukkanin sabbin filayen wasannin 13 an kammala rufin su, inda ake fatan kammala sauran kananan ayyukan da suka rage nan da karshen watan Afirilun shekara mai zuwa. A hannu guda kuma, al'ummar Chengdu da ma can masu sha'awar wasanni da gasanni ne. Yayin gasar wasannin jami'an kashe gobara da aka gudanar a watan Agustan shekarar bara, Chengdu ya sake samun yabo game da ikon sa na daukar nauyin gasannin kasa da kasa. A nan gaba kuma, birnin zai ci gaba da fadada wuraren wasanni a Chengdu, yayin da birnin ke fatan ci gaba da karbar bakuncin manyan gasanin kasa da kasa irin su gasar jami'oin dake tafe, da kuma gasar kwallon tekur ta kasa da kasa a shekarar 2022, da kuma gasar kasashen duniya ta 2025. Burin birnin shi ne janyo gasanni, da bunkasa yankunan birnin, da fadada harkokin masana'antun sa, ta yadda hakan zai amfani al'umma. Birnin Chengdu ya riga ya shirya karbar bakuncin gasannin daban daban, wadanda za su iya ba da damar inganta rayuwar al'ummar sa. Ya zuwa watan Disambar shekarar bara, an gina hanyoyi na zamani na Tianfu masu tsawon kilomita 3,429, da kayayyakin wasa nau'oi daban daban da yawan su ya kai 1,224. An kuma ware hanyoyin tafiyar kafa da motsa jiki masu yawan gaske, da da'irar motsa jiki na mintuna 15, wanda hakan ke kara karfafa kwazon masu sha'awar motsa jiki dake birnin. Tuni dai aka fara sauya kwalliyar birnin Chengdu sakamakon wadannan wasanni. Ana dai ganin taken "Mafarkin Chengdu ya tabbata" a kusan ko ina kan titunan birnin. A cewar Zhong Bingshu, farfesa a cibiyar raya ilimin motsa jiki ta Capital dake birnin, Chengdu zai dauki nauyin wasanni da kuma inganta tsarin birnin, wanda hakan zai kara bunkasa lafiyar al'umma. Ana sa ran wakilan gwamnatin kasar Sin da za su shiga aikin tabbatar da nasarar gasar dake tafe zai kai mutum 500. Tuni aka tsara kauyen wannan gasar ta jami'oi a kusa da jami'ar Chengdu. Kauyen wannan gasar dai ya kai fadin sakwaya mita 800,000, ya kuma kunshi sassa 4: Sashen gidajen kwana, da na sufurin rukunonin kasashen waje. Kana bayan kammalar ginin sa, kauyen zai samar da wuraren kwana, da na cin abinci, da na sufuri da sauran matsugunnai na tawagogi, da yawan su ya kai sama da 10,000 daga sassan duniya daban daban. A cewar Zhang Jiewen, wadda ta lashe lambar zinari a gasar wasan Badminton ajin mata 'yan wasa biyu, a gasar Olympic ta Athens, a duk lokacin da ake gudanar da gasannin kasa da daka, idan 'yan wasa suka shiga wannan kauye, hakan na nufin sun shiga tsarin fara gasar, wato dai sun shirya fara fafatawa a gasar. Zhang ta ce kuzarin 'yan wasan dake shiga gasar jami'oi ya haura na 'yan wasan dake shiga gasar Olympic, wanda hakan ke nuni ga mataki na bunkasar rayuwar matasa na kasashe, da yankuna daban daban na duniya. Shi kuwa mataimakin shugaban kungiyoyin wasanni na jami'oin kasar Sin Xue Yanqing, kuma mataimakin babban shugaban kwamitin gasar ta badi a jami'ar Chengdu, ya ce ana sa ran yawan 'yan wasan motsa jiki na kasar Sin da za su shiga wannan gasa zai kai kusan mutum 500, adadin da zai haura na wadanda suka shiga makamanciyar wannan gasa da suka gabata a baya a kasashen ketare. A wannan lokaci, baya ga cewa 'yan wasan manyan jami'oi da dama da za su halarci gasar, a hannu guda kuma, za a samu dalibai daga kananan jami'oi da kungiyoyi masu tallafawa, da ma 'yan aikin sa kai, da masu raya al'adu da sauran su, wanda za su yi cudanya da abokai sa'oin su, da za su halarcin birnin daga dukkanin bangarorin duniya, wanda hakan zai kara bude tunanin su, ya kuma fadada kwarewar su. Xue Yanqing ya kara da cewa "burin mu shi ne wannan gasa ta taka rawar gani, wajen raya wasanni da bunkasa ci gaban dalibai a dukkanin fannoni. Ya ce "A bara, hukumar wasanni ta kasar Sin, ta ba da lambar yabo ga FISU. A nan gaba kuma, hukumar za ta kara azama wajen shiga harkokin wasanni na kasa da kasa.

A nasa tsokaci game da bikin zagayowar lokacin dakon gasar wasanni ta jami'oin ta 31, shugaban FISU Oleg Madichin, ya ce "Tasirin wasanni yana hade al'ummu daban daban su yi abota, tare da wanzar da zaman lafiya, kana yana baiwa mutane damar kara fahimtar juna, ta yadda za su kara samun lafiyar jiki da ta tunani. Kuma wannan shi ne babban tasirin gasar.