logo

HAUSA

Gundumar Miyun Ta Beijing Na Kokarin Raya Sana'ar Kiwon Kudan Zuma

2020-09-01 21:15:15 cri

Gundumar Miyun Ta Beijing Na Kokarin Raya Sana'ar Kiwon Kudan Zuma

Gundumar Miyun ta birnin Beijing tana kara kokarin raya sana'ar kiwon kudan zuma bisa ga kyakkyawan muhallin halittu da ke akwai a wurin.

Ya zuwa yanzu akwai magidanta 2072 a Miyun dake kiwon kudan zuma da ke cikin rukunoni dubu 115. Gundumar ta zama abin misali wajen samar da zuma a kasar Sin, wadda ake kiranta "garin zuma na kasar Sin". A shekarun baya, manoman wurin sun kara samun kudin shiga saboda kiwon kudan zuma. Darajar kayayyakin zuma da aka sayar a shekarar bara a Miyun ta kai kudin Sin Yuan kusan miliyan 120 baki daya. Kana kuma, bunkasar sana'ar kiwon kudan zuma ta samar wa wasu manoma guraben aikin yi da kara samun kudin shiga, wadanda suka daina kiwon dabbobin gida da aikin gona don kiyaye muhalli a matarin ruwa na Miyun.

Har ila yau yadda kudan zuma suke baiwa shuka sinadarin da take bukata kai tsaye don ta yi 'ya'ya yana taimakawa sosai wajen kyautata muhalli da kuma kara albarkar amfanin gona. Nazarin da aka yi, ya nuna cewa, yadda kudan zuma suke baiwa shuka sinadarin da take bukata kai tsaye don ta yi 'ya'ya, ya kara yalwar tsirrai a gundumar ta Miyun, da kuma kara yawan dabbobi da tsire-tsire a kananan koguna 79 da ke kusa da matarin ruwa na Miyun. Ban da haka kuma, ayyukan kudan zuma sun kara ribar da ake samu daga wajen noman 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu a Miyun har fiye da Yuan miliyan 850. (Tasallah Yuan)