logo

HAUSA

Ziyarar Xi Jinping a Anhui ta jaddada akidar shugabannin kasar na bautawa al'umma

2020-08-26 14:46:22 CRI

Kasancewar a bana kasar Sin ke kammala wa'adin da ta tsara na gina al'umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkanin fannoni, da kuma shirinta na yaki da talauci, shugabanninta a matakai daban daban na kara azama wajen sanya ido, da tabbatar da kammalar wannan manufa cikin nasara. Karkashin wannan manufa ne kuma, shugaban kasar Xi Jinping ke ci gaba da ziyartar yankunan kasar daban daban, ciki hadda wurare da ake yaki da ambaliyar ruwa, inda ya jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da kokarin tsame daukacin al'ummun kasar daga kangin talauci, duk da kalubalen cutar COVID-19 da aka fuskanta a baya-bayan nan.

Ziyarar Xi Jinping a Anhui ta jaddada akidar shugabannin kasar na bautawa al'umma

Sassan da ziyarar ta wannan karo ta shafa, sun hada da kogin Huaihe, inda shugaban ya duba yanayin kogin, ya kuma ziyarci ganuwar ruwa ta Wangjiaba, domin duba tasirinta ga kogin na Huaihe, da kuma matakan kandagarkin ambaliyar ruwa, da ayyukan jin kai da ake aiwatarwa a mazauna al'ummar dake makwaftaka da wannan kogi, tun bayan fara fuskantar bala'in ambaliyar a farkon shekarar nan ta bana.

Baya ga wannan, shugaba Xi ya ziyarci kamfanin hada jakunkuna na Hongliang dake garin Wangjiaba, don ganin yanayin farfadowar ayyuka bayan shan fama da cutar numfashi ta COVID-19. A zangon karshe na wannan ziyara, shugaba Xi jinping ya isa Xitianpo Zhuang Tai na kauyen Limin dake garin Caoji. Ya kuma ziyarci filayen noman yankin, domin kara fahimtar halin da gonaki ke ciki. A kauyen Xidanpo na gundumar Funan, dake birnin Fuyang, shugaban ya gana da al'ummun da ke zaune daura da filayen noma. Ko shakka babu, muhimman abubuwan lura game da wannan ziyara ta shugaban kasar Sin, sun hada da yadda har kullum mahukuntan kasar ke kokarin sauke nauyin dake wuyansu, na lura da cimma nasarar dukkanin wasu manufofi da aka tsara aiwatarwa domin ci gaban al'umma. Kaza lika batun mayar da bukatun jama'a sama da komai, da tabbatar da al'umma na rayuwa cikin yanayi mai kyau ginshiki ne na wannan akida. Har ila yau batun kare muhalli, da tabbatar da samar da muhalli mai nagarta ga al'umma, ya zama wani muhimmin aiki da shugabancin kasar ta Sin ke dora muhimmanci a kansa, wanda ya dace dukkanin sassan kasa da kasa su yi aiki tare don tabbatar da nasararsa a ko ina.

Ziyarar Xi Jinping a Anhui ta jaddada akidar shugabannin kasar na bautawa al'umma

Alal hakika, abun ban sha'awa ne ganin yadda shugabanni irin na babbar kasa kamar Sin, ke iya ware lokacin cikin tarin hidimomin dake gabansu, domin cudanya da al'ummun dake rayuwa a matakin farko wato na kauyuka, da yankuna mafiya fama da talauci.

Ko shakka babu, aiki tukuru da shugabannin kasar Sin ke yi na sauke nauyin dake wuyansu a dukkanin fannoni ta hanyar gudanar da ayyuka na zahiri, na kara nuni ga akidar shugabannin kasar na bautawa al'umma. (Ibrahim, Saminu/Sanusi Chen)