An kaddamar da taron baje kolin tarihin bikin fim na kasa da kasa na birnin Beijing
2020-08-24 14:12:46 cri
A ranar Asabar da ta gabata, an kaddamar da wani taron baje kolin nasarorin da aka cimma cikin shekaru 10 bayan kaddamar da bikin baje kolin fina-finai na kasa da kasa na birnin Beijing na kasar Sin.
A safiyar ranar Asabar, bisa agogon birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, an bude wani taron baje koli don tunawa cika shekaru 10 ta kafuwar bikin bajekokin fina-finai na kasa da kasa na Beijing, bikin da ya gudana a wani dakin adana abubuwa masu nasaba da fim na kasar Sin.
Yayin wannan biki, an nuna yadda aka yi kokarin raya harkar bikin fim na Beijing cikin shekaru 10 da suka wuce, don kyautata dandalin musayar ra'ayi tsakani masu daukar fim na kasar Sin da na kasashen waje, da kara bunkasa ciniki, da hadin gwiwa, da musayar al'adu a wannan fanni. Chen Ling, ita ce shugabar dakin adana kayayyaki masu nasaba da fim na kasar Sin, ta gaya mana cewa,
"Wannan shi ne karon farko da muka tsara irin wannan taron baje koli don nuna yadda aka yi kokarin raya bikin fim din cikin shekaru 10 da suka wuce. Ta wannan hanya, za mu nazarci irin fasahohin da aka samu a baya, ta yadda a gaba, za mu gudanar da ayyuka da kyau."
A yayin wannan taron baje koli, an nuna wasu fannoni da aka samu nasarori wajen rayar harkar bikin fim na Beijing, da suka hada da taurarin wasan kwaikwayon, da fina-finan da aka nuna, da kyaututtukan da aka bayar, da makamantansu. Sa'an nan a lokaci guda, ana gudanar da baje kolin ne a shafin yanar gizo ta Internet, inda jama'a masu sha'awar kallon baje kolin za su iya yin amfani da na'urar kwamfuta ko kuma wayar salula, don kallon yadda ake gudanar da bikin baje kolin. A cewar Madam Chen Ling, wannan dabara wani yanayi ne na musamman ga taron baje kolin na wannan karo. Ta ce,
"Muna kokarin hada bikin da ake yi cikin dakinmu na nuna kayayyaki, da wani biki ta intanet. Za kuma a iya kallon abubuwan da aka nuna ta wata fasaha da ke kira VR. Ta wannan hanya muna fatan jama'a za su iya kallon abubuwan da muka nuna a ko da yaushe, ta yadda za mu samu wani bikin fim, da za a rika kallo a duk lokacin da ake bukata."
Bayanai na nuna cewa, taron bajekolin da ke gudana a dakin nuna kayayyaki masu nasaba da aikin daukar fim na kasar Sin, zai ci gaba har zuwa watan Nuwamban bana. A hannu guda kuma, za a dauki wani lokaci ana gudanar da taron baje kolin da ake yi ta shafin yanar gizo. Shi dai wannan biki na musamman ya riga ya janyo hankali masu kallo da yawa, inda wata mace daga cikinsu ta gaya mana cewa,
"Gaskiya bikin ya burge ni sosai, da ma ban zaci za a yi baje kolin kayayyaki da fina-finai da yawa kamar haka ba. Don haka na karu sosai. Na san a lokaci daya ana gudanar da wasu ayyuka da bukukuwa kan shafin yanar gizo ta Internet. To, zan ci gaba da mai da hankali kan lamarin, sa'an nan zan gaya ma abokai na domin su ma su zo su kashe kwarkwatan idonsu."
A nasa bangare, wani saurayi ya gaya mana cewa, "Da ma a cikin iyalina, akwai wanda ke yin wani aiki mai nasaba da daukar fim, don haka yau na zo don kara koyon wani abu dangane da aikin. Burina shi ne, kara kyautata tsarin bikin baje kolin fina-finan kasa da kasa na birnin Beijing, sa'an nan za a samu damar kara habaka tsarin bikin, don ya zama biki mai girma."
Sauran fasahohin zamani da aka yi amfani da su wajen tsara wannan taron baje koli sun hada da wani babban allon telabijin mai lankwasa, sa'an nan fadinsa ya kai muraba'in mita 1800. Girmansa da tsarinsa na lankwasa sun sa masu kallo ke ji tamkar suna cikin fim din da aka nuna. (Bello Wang)