logo

HAUSA

Wasu yara 'yan firamare dake wani karamin gari na fatan shiga a dama da su a fannin kwallon kafa

2020-08-21 09:31:27 CRI

Wasu yara 'yan firamare dake wani karamin gari na fatan shiga a dama da su a fannin kwallon kafa

Wasu 'yan makarantar firamare dake garin Wuguanyi, wani karamin gari dake gundumar Liuba a lardin Shaanxi, da suka hada da maza 48 da wasu mata, sun shiga horon kusan wata guda, domin samun kwarewa wajen buga kwallon kafa yayin hutun su na lokacin zafi. 'yan makarantar sun rika gudanar da horo karo biyu a kullum, da kuma gasa tsakanin rukunonin su da yammacin ko wace rana. Fatan yaran dai shi ne samun gurbin karatu a jami'oi masu nasaba da kwallon kafa, yayin da wasun su ma ke burin a zabe su, don shiga tawagar kwallon kafar kasar su, kamar dai 'yan uwan su Sinawa da suka yi fice a wannan harka a matakin karatun jami'a daga Liuba, wato 'yan wasa Shi Xiaomin da Zou Mengyao.

Mafarkin zama 'yan wasan kasa da kasa

Tawagar mata 'yan kasa da shekaru 16 ta kwallon kafar kasar Sin, ta doke takwararta ta kasar Australia da ci biyu da daya, a wasan neman matsayi na 3 na gasar shekarar 2019, wadda hukumar kwallon kafar nahiyar Asiya ta AFC ke shiryawa. 'yan wasan Sin Shi da Zou ne suka ciwa kasar su kwallaye daidaya, matakin da ya jefa magoya bayan kungiyar cikin matukar farin ciki. Da yake tsokaci kan wannan nasara da tawagar ta Sin ta samu, mataimakin shugaban makarantar midil ta garin Liuba Zhang Suyang, ya ce 'yar wasa Shi, ta taba shaida masa cewa za ta ci wa tawagar ta kwallo a wannan gasa ta hukumar AFC. Ya ce dalibar na fatan hakan ya zama wata tsaraba ga malaman ta, da ma 'yan uwan ta dake garin su wato Liuba. Ga shi kuwa ta cika wannan alkawari na ta. A shekaru 1990, shi kan sa Zhang ya baiwa tawagar matasa ta Shaanxi gudummawa, amma bai ci gaba zuwa babbar kungiyar kwallon kafar ba. Maimakon haka, Zhang ya kammala karatu a kwaleji, ya kuma zabi zama malamin makaranta, inda yake aiki a makarantar midil ta Jiangwozi dake garin Liuba. A lokacin da hukumar wasanni ta lardin Shanxi ta bukaci garin Liuba ya bunkasa gasar wasan kwallon kafa ajin mata a shekarar 2008, sai Zhang wanda ke koyarwa a makarantar midil ta Liuba ya yanke kudurin kafa kungiyar kwallon kafar mata a makarantar. Ya nemi gudummawar daukar nauyin 'yan wasa daga karamar gundumar mai yawan al'umma kusan 40,000, ya kuma yi hadin gwiwa da yayan sa Zhang Suchun, dake makarantar firamare ta garin Huoshaodian. Karkashin wannan tsari ne kuma Shi da Zou suka fara horas da yara masu buga kwallo, har zuwa lokacin cikar burin su na samarwa tawagar su nasara.

Sabuwar damar rayuwa

Tang Xuesi, wanda ke aikin horas da 'yan wasa a makarantar firamare ta garin Wuguanyi, zai shiga jami'ar Northwest ta kasar Sin cikin watan Satumba, karkashin tallafin karatu na wasan kwallon kafa. A cewar mataimakin darakta a hukumar raya wasanni da Ilimi ta garin Liuba Chen Jun, yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, idan an kwatanta garin Liuba da sauran garuruwan gabashi da yammacin Sin masu makwaftaka da teku, za a ga cewa gari Liuba bai kai su ci gaba ba. Amma kuma tsarin garin na kwallon kafa yana da inganci, ta yadda yake baiwa yara damar cin jarabawar su ta shiga kwaleji, har su kai ga matakin sama na jami'a. Jami'in ya kara da cewa, domin hade ayyukan karatu da na wasa da yaran ke gudanarwa a kullum, makarantar midil ta Liuba, ta tattara dukkanin yara 'yan wasan kwallon kafa masu kwarewa a aji guda. Ko wane ajin 'yan kwallo na da yara kimanin 30 maza da mata. Dan wasa Tang, ya shiga irin wadannan ajujuwa shekaru 6 da suka gabata, inda kuma ya ci wa Liuba kwallaye, tare da daga kofunan gasanni da dama, har ta kai ya samu gurbin karatu a jami'ar Northwest ta kasar Sin. Game da hakan, Chen ya bayyana cewa, tsarin Liuba na bunkasa wasan kwallon kafa an rada masa suna "Salon 1352 ". Daya ta farkon sunan, na nufin za a ci gaba da buga wasan kwallo a dukkanin ajujuwan makarantar midil dake Liuba. Uku kuma na nufin yunkurin gano yara masu hazaka cikin dukkanin makarantu 3 na firamare. Biyar kuma na nufin malamin koyar da wasannin motsa jiki zai kwashe kaso 50 bisa dari na lokutan da ba na karatu ba, wajen horas da yaran dabarun kwallon kafa. Kana lamba 2 ta karshe na nufin za a rika gudanar da harkokin wasanni guda biyu a makarantun renon yara dake Liuba, a wani mataki na gina sha'awar yara ga wasan na kwallo.

Zakulo arziki ta hanyar mayar da hankali ga kwallon kafa

Shekaru 10 da suka gabata, kauyen Yingpan na cikin wurare mafiya talauci tsakanin kauyukan dake Liuba. Wata mata dake zaune a kauyen mai suna Luo Caiqin, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, mazauna wurin 50 cikin jimillar mutum 350 na aiki ne a wasu wurare dake wajen kauyen, kuma a shekara guda, iyalin ta na samun kudin shiga da bai wuce kudin Sin yuan 20,000 ba, wato kwatankwacin dalar Amurka 2,800 ta hanyar sayar da abubuwan hadi magungunan gargajiya. A shekarar 2017, aka kafa cibiyar horas da kwallon kafa a Yingpan. Ana iya ganin filin kwallon kafa cikakke a tsakiyar tsaunin Qinling, kuma a kewayen tsaunukan dake yankin, akwai filayen kwallon kafa 4, da kuma ginin dakunan kwana dake iya daukar mutane kusan 900. An yi amfani da wannan wuri, yayin gasar kwallon kafa ta matasa ta bana da ta gudana a Shaanxi, inda dubban 'yan kallo da 'yan wasa suka ganewa idanun su, gasar da aka yi, da ma yanayin wannan gari na Yingpan. Bayan la'akari da shawarwarin matasa, Luo ta sauya tsarin kayayyakin dake cikin kantin ta. Ta ce "Abun ban mamaki. Mafi yawan abubuwan dake ciki kantin nawa biskit din Oreos ne!" Ta ce "A bara na san wasu 'yan garin mu da suka samu kusan yuan 130,000, kwatankwacin dalar Amurka 18,700 cikin watanni 2 kacal saboda zuwan wasanni wannan yanki. Ta hanyar karbar bakuncin gasannin kwallon kafa, Liuba ya samu kudin shiga har yuan miliyan 10, wato kimanin dalar Amurka miliyan 1.44 tsakanin watan Yuni zuwa Satumbar shekarar 2019. Chen ya ce, kudaden shigar da aka samu daga harkar wasan kwallon kafa, za su taimakawa yankin a fannin raya wasan kwallo a makarantun dake gundumar. Ya ce cibiyar Yingpan za ta samar da karin filayen wasa 4 nan da shekarar 2021, wanda hakan ke nuna cewa, gundumar za ta samar da isassun kayan horo da ake bukata domin gudanar da gasanni da dama bisa mizanin kasa da kasa. Kaza lika a cewar jami'in, fatan su shi ne mayar da cibiyar ta Yingpan, zama wurin samar da horon kwallon kafa na yammacin kasar Sin, da ma wasannin zamiya da sauran su.

Daga nan sai ya yi fatan ganin kwallo kafa ta taimakawa Liuba, wajen janyo hankulan sassan kasuwanni a nan gaba.