logo

HAUSA

Makircin Pompeo kan kasar Sin a yankin Turai bai yi nasara ba

2020-08-19 09:01:59 CRI

A kwanakin baya ne, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya kammala ziyarar aiki da ya kai kasashen Turai guda hudu da suka hada da kasar Czech, da Slovenia, da Austria da kuma Poland. Kamar yadda ya saba yi, a wannan karo, ya dukufa wajen yada "cutar siyasa" a wadannan kasashe, domin cin zarafin jam'iyya mai mulkin kasar Sin, da rura wutar farfado da yakin cacar baki.

Makircin Pompeo kan kasar Sin a yankin Turai bai yi nasara ba

Amma, bisa yadda kasar Amurka ta saba wajen kwashe moriyar kawayenta, yanzu, kasashen Turai ba su son zama masu goyon bayan manufar "Amurka da farko". Kuma, a wannan karon da Mike Pompeo ya kai ziyarar aiki a kasashensu, ko da yake, ya yi ta zargin kasar Sin bisa wasu dalilai marasa tushe, amma, kawayenta ba su yarda ba.

Haka kuma, a yayin ziyarar Pompeo ya zargi kamfanonin fasahar 5G na kasar Sin, cewar wai za su kawo barazana ga tsaron kasashensu, sai dai shugabannin wadannan kasashe ba su yarda da kalaman na Pompeo ba. Burinsu shi ne kafa tsarin bayanai mai inganci, a maimakon tsara manufar hana wani kamfani musamman na wata kasa. Sanin kowa ne cewa, kasar Sin da kasashen dake tsakiya gami da gabashin nahiyar Turai ba su taba yin sabanin siyasa ba cikin tarihi, kuma suna da moriyar iri daya a fannin hadin gwiwar albarkaru, da fasahohi, da kuma kasuwanni da sauransu.

Makircin Pompeo kan kasar Sin a yankin Turai bai yi nasara ba

A halin yanzu, da ake fama da matsalar koma bayan tattalin arziki da kariyar ciniki, babu wata kasa a yankin da za ta so katse huldar ciniki a tsakaninta da kasar Sin.

Yanzu haka kasashen dake tsakiya gami da gabashin nahiyar Turai sun cimma ra'ayi daya cewa, kasar Sin ita ce abokiyar da ta kawo musu damammaki a maimakon kalubaloli. Wasu 'yan siyasa kamar Mike Pompeo da sauransu ba za su cimma burinsu na dawo da wani salo na yakin cacar baki ba, kuma, ci gaba da yin karya kan wannan batu, zai sa su zama masu aikata mummunan laifi a tarihin duniya. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)