logo

HAUSA

Owodunni Maryam: A hada hannu don bar wa zuriya ta gaba wata kyakkyawar duniya

2020-08-17 16:06:42 CRI

Owodunni Maryam: A hada hannu don bar wa zuriya ta gaba wata kyakkyawar duniya

Masu sauraro, abin da kuka saurara dazu wata waka ce da wata 'yar Najeriya ta rubuta kuma ta karanta. Taken wakar kuwa shi ne "Wanda ya zo ba zata", Owodunni Maryam, wata daliba 'yar Najeriya da ke karatu a nan kasar Sin ita ce da ta rubuta domin bayyana aniyar yaki da cutar COVID-19.

Owodunni Maryam daga birnin Lagos, yanzu tana karatun digiri na biyu a fannin falsafa a jami'ar Suzhou da ke gabashin kasar Sin. Yayin da take hira da wakiliyarmu Fa'iza Mustapah, ta bayyana cewa, ta karanta harshen Sinanaci a digiri na farko a Jami'ar Lagos, wadda ta kasance daya daga cikin 'yan ajin farko da suka karanci Sinanci a jami'ar Nijeriya a shekarar 2013. Ta kwashe shekaru 2 a Nijeriya, sannan ta taho nan kasar Sin ta yi wasu shekaru biyu. Sun fara zuwa kasar Sin ne a shekarar 2015, sai kuma bara da ta zo karatun digiri na 2. Kamar yadda aka sani, a lokacin bikin bazara na bana wato a karshen watan Janairu, cutar COVID-19 ta fara bulla a kasar Sin. Yayin da tabo batun yanayin da ake ciki yanzu, Owodunni ta bayyana cewa, an samu ingantuwar al'amura sosai, idan aka kwatanta da 'yan watannin da suka wuce. Kusan dukkan harkoki sun koma kamar yadda suke. A kwanan nan ma, wasu jami'o'i sun fara barin dalibai suna shiga cikin makaranta, idan aka kwatanta da lokacin da aka kulle a baya. Lokacin da ta waiwayi yanayin fama da cutar a baya, Owodunni ta ce, "Cutar ta barke ne a lokacin bikin bazara. ko ina ya kasance a rufe, mutane ba sa iya tafiye–tafiye, kamfanoni da harkokin kasuwanci sun tsaya, makarantu sun koma karatu ta intanet, don a rage mu'amala tsakanin mutane. Amma a yanzu abubuwa sun sauya. Idan ba wuri mai yawan mutane ba, ba ka bukatar sanya makarin baki da hanci. A baya abinci ma sai dai ka saya, ka tafi da shi gidanka. Duk wanda yake kasar Sin ya san Sinawa sun fi son sayen abinci, amma lokacin da annobar ta barke, kusan kowa ya tuna tsohuwar fasaharsa ta girki." Masu sauraro, kamar yadda muka bayyana muku a farkon shirinmu na yau, Owodunni ta taba rubuta wata waka a lokacin da annobar ta yi tsanani. Owodunni ta bayyana cewa, idan ta tuna yadda ma'aikatan jinya da masu aikin sa kai suka dukufa wajen yaki da cutar COVID-19 ba tare da tsoron komai ba, har sai ta yi hawaye. Kaunar da kasar Sin cike take da ita ta burge ta kwarai da gaske. "Annobar ta barke ba zato ba tsammani. Kuma ta zo a lokaci mafi hada-hada a shekara. A lokacin jama'a na cike da tsoro da fargaba da rashin sahihan bayanai, abin da ya haddasa yada jita-jita, lamarin da ya sanya tsoro a zukatan mutane. Dokar kulle da aka sanya a lokacin, ta haifar da fargaba domin ba kowa ne ba yake son takurawa ba. Wannan shi ne ya sa ni rubuta wakar, inda na bayyana ainihin abun da ke wakana da karfafa gwiwar mutane. kuma na jaddada bukatar hadin kai, domin ta hadin kai ne kawai za mu iya fuskantar wannan kalubale." Owodunni ta kuma furta cewa, a matsayinta na daliba mai koyon ilmin falsafa, ta kan yi nazari da ma kwatanta matakan da Sin da kasashen yammacin duniya suka dauka wajen tinkarar cutar COVID-19 da ma sakamakon da suka samu. Sa'an nan za ta yi tunani kan abin ya jawo bambanci sosai a tsakaninsu. Owodunni ta ce, " A ganina, matakan kasar Sin su ne mafi dacewa duba da yadda abubuwa suka kasance. Duk da cewa ba kowa ne zai yi na'am da su ba, idan dai za mu fadi gaskiya, abun da ya kamata ke nan. A ganina sauran kasashe ma na iyakar kokarinsu, kuma wasu ma sun koyi matakan na kasar Sin, amma kuma an fi ganin sakamako mafi kyau a kasar Sin, saboda irin tsarin gwamnatinta, wanda ke samun goyon baya ainun ba tare da adawa ba. Al'ummomin kasashe da dama na son 'yanci sosai, wanda a wasu lokutan ke kaiwa ga keta dokoki. Amma saboda tsarin gwamnatin kasar Sin, ba a samu matsala ba wajen samun hadin kan al'umma. Sannan tsarin gwamnatin na bada damar daukar matakai cikin sauki ba tare da matsala ba. Kuma a wannan lokaci, abun da ake bukata ke nan duba da yanayin gaggawa da ake ciki. Wannan ya taimakawa kasar Sin shawo kan matsalar cikin sauri."

Game da hadin gwiwar Sin da Afrika wajen yaki da cutar, Owodunni tana ganin cewa, a farkon barkewar cutar a Sin, galibin kasashen Afrika da sauran na duniya, sun kasance da kasar Sin tare da taimaka mata, kuma da yanayin ya sauya, ita ma kasar Sin ta taimaka musu. Haka ake bukata a duniya.

"Kamar yadda na rubuta a wakar, 'duk da cewa ana fuskantar kalubale, mun hada kai don mu yi galaba'. Haka zalika, wani baitin na cewa, 'mu al'umma ce dake hade da juna, cikin kwale-kwale daya muke tafiya, don haka za mu yi nasara a wannan yaki'. A ganina, hadin kai da goyon bayan juna ake bukata. Kuma shi ne abun da hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika ke nunawa." Ya zuwa yanzu dai, Owodunni ta shafe shekaru uku tana kasar Sin. A matsayinta na mace, kullum ta kan kwatanta mata Sinawa da na Najeriya, da tunani kan yadda suke iya koyi da juna. A ganinta, suna da kamanceceniya. Kamar yadda suke da kokari da jajircewa da kuma tarbiyyar yara. Bambancin da kawai take gani shi ne, yadda suke tafiyar da mazajensu, wanda ke da nasaba da bambancin yanayin al'adu da tarihi da dabi'u. Game da abun da za su iya koya daga juna, Owodunni ta furta cewa, "A ganina, kasar Sin kasa ce da ta fi mu samun ci gaba. Matan Nijeriya za su iya koyon sabbin abubuwan zamani daga matan kasar Sin. yanzu a kasar Sin, kan mata ya waye sosai, a Najeriya ma akwai matan da suka waye, amma ba su bai kai na kasar Sin ba. kuma Matan Sinawa na iya koyi da matan Nijeriya kan yadda martaba al'adunsu. Amma dai wannan ra'ayina ne. Akwai fannoni da dama da za su iya koyi da juna. Sannan mata da 'yan Nijeriya sun fi sakewa da baki, amma a nan suna dan taka tsantsa da farko, kafin daga baya su sake da kai." Owodunni tana sa ran ganin ci gaban matan Najeriya cikin shekaru masu zuwa. Ta yi tsokacin cewa, ana iya cewa matan Nijeriya suna kokari a dukkan fannonin rayuwa, yayin da suke kula da gida da tarbiyyar yara. Don haka ta yi imanin idan matan suka kara samun Ilimi, ba karatun boko ba kadai, kamar sanin 'yancinsu, babu inda ba za su kai ba. Tana ganin cikin shekaru masu zuwa, matan Nijeriya za su kara samun ci gaba

A yayin zantawa da wakiliyarmu, Owodunni, ta sha ta ambaton batun hadin kai da goyon bayan juna. Duniya baki daya ba Sin da Afrika ba kadai, na bukatar hadin kai. A ganinta, duk abun da ke faruwa ko za su faru nan gaba, sai an hada kai kafin a iya shawo kansu. Amma ba wai yau ka ji an ce wasu kasashe ba sa ga maciji ba, gobe a ce waccan kasa da waccan ba sa jituwa. Kuma gaskiya ba a bukatar wani yunkurin neman iko da fifiko. Akwai bukatar a hada kai don shawo kan kalubale. A cewarta, babu wanda ya san cutar COVID-19 za ta zo, amma ga ta nan, kuma ba a san gobe ba, don haka ya kamata mu mayar da hankali wajen gyara alakarmu yayin da muke raya duniya.

"Yanzu duniyar ta dunkule wajen guda saboda ci gaba, kuma da a cikin shekaru 20 da suka wuce annobar ta barke, da ba za ta yi saurin yaduwa haka ba. amma yanzu abubuwa sun sauya, tafiyar da za a shafe watanni ana yi, yanzu cikin kwanaki za a yi. Tun da duniya ta dunkule, ya kamata mu hada hannu. In ba haka ba, me za mu barwa zuri'a ta gaba masu tasowa? A ganina wannan shi ne abun da ya kamata mu yi."(Kande Gao)