logo

HAUSA

Kamfanonin Sin suna kokarin kyautata rayuwar al'ummun Afirka yayin kandagarkin COVID-19

2020-08-14 13:42:24 cri

 

Kamfanonin Sin suna kokarin kyautata rayuwar al'ummun Afirka yayin kandagarkin COVID-19

A halin da ake ciki yanzu, gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen Afirka ya zarta miliyan 1 da dubu 50, irin wannan yanayi mai tsanani da ake ciki ne, ya sa kamfanonin kasar Sin dake gudanar da harkokinsu a nahiyar suke kokari matuka domin tabbatar da ganin sun gudanar da ayyukansu karkashin shawarar ziri daya da hanya daya yadda ya kamata, lamarin da ya nuna wa al'ummun kasa da kasa saurin aikin kasar Sin.

Kamfanonin Sin suna kokarin kyautata rayuwar al'ummun Afirka yayin kandagarkin COVID-19

A ranar 7 ga watan Agusta, agogon kenya, an yi nasarar kammala aikin nutsar da dogon karfe a babbar tashar ruwa ta hakar mai ta hukumar kula da harkokin tashoshin kasar Kenya da kamfanin CCCC wato kamfanin gina kayayyakin sufuri na kasar Sin yake ginawa a tashar ruwa ta birnin Mombasa na kasar ta Kenya, tsayin babbar tashar ya kai mita 770, gaba daya an jibge kayayyakin turakan jirgin ruwa guda 12, da kayan saukar jirgin ruwa guda 4 da dandalin adana da saukar da kayayyaki guda 2 da kuma wani babban dandali na daban. Bayan kammala tashar ruwa, za ta biya bukatun shigi da fici na kayayyakin mai na kasar, haka kuma za ta taka babbar rawa kan ci gaban tattalin arzikin kasar ta Kenya, kana za ta taimaka wa kasar wajen cimma muradunta nan da shekarar 2030, hakazalika, za ta ingiza bunkasuwar Kenya da sauran kasashen dake gabashin nahiyar ta Afirka baki daya.

A gabar tekun Guinea dake yammacin Afirka, a kwanakin baya ne, aka kammala aikin gina tashar ruwa da za a rika sauke manyan kwantenonin kayayyaki a tashar ruwa ta Tema ta kasar Ghana daga duk fannoni, wato an kammala aikin ne kwanaki 50 kafin lokacin da aka tsara, a baya ana kiran kasar ta Ghana da sunan "gabar teku ta zinari", inda take da gabar teku mai tsayin kilomita 562, tashar ruwa ta Tema, ita ce tashar ruwa mafi girma a kasar, inda ake jigilar kaso 80 na kayayyakin shigi da fici na kasar, yanzu haka bisa bunkasuwar tattalin arzikin kasar da kuma kara karfafa cudanyar tattalin arzikin dake tsakanin kasashen yammacin Afirka, tashar ruwan Tema ba ta biyan sabbin bakatu, a don haka an tsai da kudurin gina wata sabuwar tashar ruwa da za a rika sauke manyan kwantenonin zuba kayayyaki bisa shawarar ziri daya da hanya daya, sabuwar tashar ruwar za ta kasance tashar ruwa ta zamani dake sahun gaba a duniya,kana za ta zama babbar cibiyar jigilar kayayyaki kan teku a yankin yammacin Afirka.

Kamfanonin Sin suna kokarin kyautata rayuwar al'ummun Afirka yayin kandagarkin COVID-19

A cikin 'yan kwanakin nan, mazauna kauyen Xifenbu na jihar Cabinda ta kasar Angola suna farin ciki kwarai, saboda suna iya dibar ruwa kai tsaye daga famfon da kamfanoin kasar Sin ya gina a cikin kauyen, a ranar da famfon ya fara aiki a hukumance, mazauna kauyen sama da 100 sun taru a wurin domin diban ruwan famfo mai tsabta

Cikin dogon lokaci, mazauna kauyen da yawansu ya kai sama da 2000 suna sa ran za su sha ruwa mai tsabta, amma daga zuriya zuwa zuriya, suna dibar ruwa ne daga wani kogin dake da nisan kilomita daya, kana ruwan kogin ba shi da tsabta, domin canja yanayin da suke ciki, gwamnatin Angola ta yi hadin gwiwa da kamfanin CRCEG na kasar Sin wato kamfanin gina layin dogo na kasar Sin domin gina tsarin samar da ruwa a jihar, abun farin ciki shi ne, kwanan baya, an cimma burin shigar da bututun ruwa samfurin DN90 a cikin gidajen mazauna jihar Cabinda ta kasar, bayan kammala aikin, ko wace rana adadin ruwan famfon da ake samarwa zai kai cubic mita dubu 50, inda yankunan gidaje kaso 92 bisa dari a jihar za su amfana da gangunan ruwan famfon, wato al'ummun kasar da yawansu ya kai dubu 600 za su mori aikin.

Kamfanonin Sin suna kokarin kyautata rayuwar al'ummun Afirka yayin kandagarkin COVID-19

Hakika abu ne mai wahala a gudanar da aikin gina tsarin samar da ruwan famfo a jihar, saboda karancin kayayyaki a wurin, haka kuma ma'aikatan kamfanin kasar Sin sun gamu da matsaloli daban daban, alal misali zafin yanayi da yawan ruwan sama da kamuwar cutar malariya da sauransu, a bisa wannan yanayin, kamfanin ya kara kyautata shirin aiki har sau goma, domin gudanar da aikin lami lafiya kuma cikin sauri. Kana abun bakin ciki shi ne kafin a kammala aikin, annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta fara barkewa a nahiyar Afirka, gwamnatin Angola ta sanar da cewa, kasar ta shiga yanayin gaggawa, sakamakon haka, ma'aikata sun ragu, har an daina jigilar kayayyakin aikin da ake bukata, reshen kamfanin kasar Sin dake Angola ya kara tura ma'aikatan fasaha zuwa wurin aiki, domin dawowa bakin aikin cikin gaggawa, yanzu haka an yi hasashen cewa, al'ummun kasar sama da dubu 600 za su fara amfana da famfo nan da karshen shekarar bana.(Jamila)