logo

HAUSA

Mahepali: 'Yar kabilar Kazakh wadda ke jagorantar bangaren tankunan yaki na bataliyar soja dake jihar Xinjiang

2020-08-13 09:15:00 CRI

 

Ita ce mace ta farko da ta fara tuka motoci masu sulke a wannan bangare. Ita ce babbar jami'a ta farko da ta jagoranci sashen kula da tankuna yaki na soja. Sunanta Mahepali, ta kuma yi aiki a sassa daban-daban har guda 6 tun bayan da ta shiga aikin soja a cikin shekaru 7 da suka wuce, wannan 'yar kabilar Kazakh ta iya sarrafa makamai iri-iri har guda 12, tana nuna kaunar aikinta da kuma kokarin cimma burin da ta sanya a gaba.

 

An haife Mahepali a shekarar 1991, ta kuma yi fama da lalurar kwayoyin cuta dake shiga magudanar jini a lokacin da take karama. Wannan ya sa aka sauya dukkan jinin dake jikinta. A yayin da take shekaru 8, ta warke daga wannan cuta, irin wahalar da ta sha ta sanya ta zama mai karfin hali.

Mahepali yana nufin furen da ba zai mutu ba dake zama a dutse bisa wani labarin gargajiyar 'yan kabilar Kazakh, wanda yake nuna karfin hali da jajurcewa. Kamar yadda ma'anar sunanta ta nuna, Mahepali tana namijin kokari don ganin ta cimma burinta. Ta kammala dukkan kwasa-kwasan da ta dauka a jami'a cikin shekaru uku kacal, hakan ya sa ta zama ita daya kacal da ta kammala karatu a jami'arsu a wannan shekara. Daga baya kuma, sai ta koma garinsu dake jihar Xinjiang don shiga rundunar soja. Bayan shekaru biyu kuma, ta zama jami'a mata ta farko, a matsayinta na fittaciyar soja daliba, kuma an tura ta zuwa makarantar horar da jami'an sojoji. Bayan kammala karatunta a makarantar, ta kara zaben komawa jihar Xinjiang, inda ta shiga rundunar soja mai kula da motoci masu sulke.

A yayin da ta soma aiki a rundunar kula da motoci masu sulke, ta gabatar da rokonta na zama mai ba da shawarwari ga sojoji a sashe tankunan yaki. Amma, a karon farko da ta shiga sashen dake hade da sojoji maza, ba ta da kyakkyawan fata game da makomar aikinta ba.

 

Mahepali: 'Yar kabilar Kazakh wadda ke jagorantar bangaren tankunan yaki na bataliyar soja dake jihar Xinjiang

 

A kokarin ganin ta saba da yanayin aiki a wannan sashe, Mahepali ta kan yi hira da sojoji don kara yin mu'ammala da su, a fannin horo kuma ta soma koyon abubuwa game da tankunan yaki, don tinkarar sabbin kalubale da za su iya kunno kai Maheoali ta ce, "A kullum, sojojinmu ba su cewa kome game da ni, amma na san cewa, dukkansu suna kula da aikin da nake yi. Idan har ban iya gudanar da ayyuka yadda ya kamata ba, to ba za su amince da ni ba." A yayin da ake tuka tankar yaki, tana girgiza sosai, motsinta kan saka ni jiri har ma da amai. Don haka, kafin ta shiga cikin motar, Mahepali ta kan tanadi leda koda za ta yi aman, duk da haka, ta mayar da hankali wajen samun horo, a karshe har ta iya sarrafa tankar yaki mai nauyin ton 38.

Mahepali: 'Yar kabilar Kazakh wadda ke jagorantar bangaren tankunan yaki na bataliyar soja dake jihar Xinjiang

 

Wani soji na kamfanin Liu Quannong ya ce,

"Duk da kasancewar mu maza, amma jami'ar da take ba mu shawarwari, ta fi mu hakuri da kokari, a wasu lokuta kuma muna ganin cewa, ta kware a wannan fanni, amma ta kan ce, a'a, ba ta kware ba, da sauran dabaru da ya kamata ta koya. Gaskiya ina girmamata sosai."

Bayan watanni biyu, ba kawai Mahepali ta ci jarrabawar tuka tankar yaki ba, har ma ta ci jarrabawar sadarwa da harbi yadda ya kamata, hakan ya sa ta zama mace ta farko da ta kware a fannin tuka tankar yaki a bataliyarsu. A bisa jagorancinta, dukkan sojoji da jami'an wannan sashe, sun ji dadin horon da suka samu sosai, har ma sojoji masu yawan haske sun samu lambobin yabo a gasannin da aka shirya.

 

A farkon shekarar da muke ciki, bangarensu ya kafa wani sashen sarrafa tankunan yaki na sojoji mata a bataliyarsu a hukunce, a yayin da ake shirin zaben wanda zai kula da sashen, nan da nan sai aka tuna da Mahepali.

Domin gyara kuskuren da sojojin dake wannan sashe suka aikata, Mahepali ta yi ba su misali, ban da wannan kuma, ta tsara shirye-shiryen musamman na samun horo ga ko wannensu bisa halayensu na musamman Wata soja ta bangaren Shi Xiuli ta ce, "Hakika koyon sarrafa tankar yaki ta soja yana da wahala, jami'ar dake ba mu shawarwari ta kan yi mana jagora da ba mu kwarin gwiwa, dukkanmu mun yi imanin cewa, idan har jami'ar dake ba mu shawarwari za ta iya, to mu ma za mu iya."

 

A cikin watanni uku kawai da aka kafa wannan sashe na tuka tankar yaki na sojoji mata, sojojin dake wannan sashe sun samu sakamako mai kyau a jarrabawar koyon harbi da aka shirya.

A ganin Mahepali, sashenta yana karfi da kwarewa sosai, ana iya cewa, ita jagora ce da ta kware. Yanzu, ana sake daidaitawa da kyautata al'amura a wannan sashe, za kuma a jibge wasu sabbin makamai da damka musu sabbin ayyuka. Game da wannan, Mahepali ta ce, abin da ta sanya a gaba yanzu shi ne, ba wai duba nasarori da yabo da ta samu ba, maimakon haka, tana son kara kokarin jagorantar sojojinsu wajen cimma sabon burin da suka sanya a gaba.

"Jama'a da dama na ganin cewa, mata ba su dace da aikin jagorantar sojoji masu sarrafa tankunan yaki ba. Idan har na kawar da wannan bahagun tunani, to, dole ne na kara kokarin sauran mutane, domin ta hakikanin abubuwan da na aikata, na nuna musu cewa, sun yi kuskure."