Matakin Amurka kan Tik Tok ya saba doka
2020-08-12 19:29:25 CRI
A kwanakin baya ne gwamnatin kasar Amurka ta sanar da cewa, za ta dauki mataki kan manhajar Tik Tok mallakin kamfanin ByteDance na kasar Sin da ake amfani da ita a ketare, lamarin da ya jawo hankali da ma suka daga al'ummun kasa da kasa.
Shugaban Amurka har ma ya yi kashedin cewa, "Dole ne a sayar da manhajar Tik Tok ga kamfanin Microsoft na kasar ta Amurka kafin ranar 15 ga watan Satumban dake tafe, in ba haka ba dole ne a daina yin amfani da ita", kana ya kara da cewa, dole ne a gabatar da wasu kudin da aka sayar da manhajar ga gwamnatin kasar Amurka.
Tsokacinsa dake nuna fin karfi ya gamu da suka da shakku daga jama'a a cikin gida da wajen Amurka da sauran kasashen duniya. A watan Satumban shekarar 2016 ne, kamfanin ByteDance ya kaddamar da manhajar Tik Tok a kasar Sin bisa sunan A.me da farko, kafin a canja sunan zuwa Douyin a watan Disamban shekarar 2016.
Bayanai na nuna cewa, a cikin shekara guda, akwai mutane miliyan 100 dake amfani da manhajar, inda aka kalli hotunan bidiyo sama da biliyan 1 a cikin kwana guda, kana a kasar Amurka, ana saukar da manhajar sau sama da miliyan 80.
Amurka ta dauki wannan mataki ne ganin yadda wannan manhajar ta fi kamfanonin Amurka samun karbuwa a wajen masu amfani da yanar gizo na kasashen yamma, a don haka, matakin Amurka ya sabawa ka'idar adalci ba tare da rufa rufa ba ta hukumar cinikayya ta duniya. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)