Muhammad Rilwan: Ci gaban kimiyya da fasahar zamani na kasar Sin ya burge ni
2020-08-11 08:27:59 CRI
Muhammad Rilwan, wani dan jihar Kanon tarayyar Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na farko a fannin kirkirar manhajojin na'ura mai kwakwalwa wato software engineering a turance a jami'ar Wenzhou dake lardin Zhejiang na kasar Sin.
A zantawarsa da Murtala Zhang, Muhammad Rilwan, wanda ya yi shekaru kusan uku yana karatu a kasar Sin, ya ce karatun jami'a kasar ya bambanta sosai da na Najeriya, saboda jami'o'in kasar Sin suna aiwatar da dabarun koyar da ilimi ta hanyoyi na zahiri maimakon karatun littattafai kadai, wato ana gwada abubuwan da aka koya a aikace sabanin karanta takardu kawai.
Malam Rilwan ya kara da cewa, ya taba ziyartar wurare da dama a lardin Zhejiang da lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, kuma yadda aka tsara biranen ya burge shi kwarai da gaske.(Murtala Zhang)