logo

HAUSA

Kasar Sin ta tsara shirin raya ci gaban tattalin arziki bisa dora muhimmanci kan inganta bukatun cikin gida

2020-08-07 11:37:56 cri

A wajen taron ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin da aka shirya a kwanan baya, an nuna cewa, ya kamata kasar Sin ta gaggauta samar da sabon tsarin ci gaba, wanda ke maida hankali kan inganta bukatun cikin gida, tare da hada kai da cinikayyar waje. Masana da kwararru suna ganin cewa, wannan zai taimaka wa kasar Sin wajen tinkarar sabon kalubalen da take fuskanta, da kuma samun sabon ci gaba.

A yayin wannan taron na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, an nazarci yanayin tattalin arziki da ake ciki, da ayyukan tattalin arziki da za a yi a karshen rabin shekarar bana. Taron ya nuna cewa, yanzu haka tattalin arzikin kasar Sin na cikin wani yanayi mai tsanani, na rashin tabbas da zaman karko, wasu matsalolin da yake fuskanta za su kasance cikin dogon lokaci, dole ne a kara fahimtarsu. Baya ga haka, taron ya gabatar da cewa, za a gaggauta tsara wani sabon tsarin dake dora muhimmanci kan inganta bukatun cikin gida, tare kuma da hada kai da cinikayyar waje. Game da batun na inganta bukatun cikin gida, shehu malami na kwalejin kudi na jami'ar tattalin arziki da hada-hadar kudi ta kasar Sin Zhang Liqing ya bayyana cewa,

"A gani na, ma'anar ita ce, bisa amfanin tsarin kasuwanci, ana tabbatar da daidaito tsakanin samarwa da bukatar kayayyaki ne ta hanyar kasuwar cikin gida. A waje guda kuma, game da shigar da kasuwar kasa da kasa kuma, idan an yi amfani da tsarin sana'o'i da cinikayya na duniya, to zai inganta tabbatar da daidaito. Wato a cikin wannan yunkurin, bukatun cikin gida zasu bada muhimmin jagoranci. Wannan kwaskwarima ne bisa manyan tsare-tsare da hukumomin tsara manufofi suka yi bisa tushen tattara fasahohin da aka samu wajen samun ci gaba a cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, kuma bisa yanayin tattalin arziki da ake ciki a cikin gida da na waje. Lallai yana da ma'ana kwarai."

A hakika dai, tun daga lokacin da ake tinkarar matsalar kudi ta Asiya a shekarar 1998, kasar Sin ta soma mayar da hankali kan kara habaka bukatun cikin gida, tana ta yin hakan ne tun shekaru 20 da wani abu da suka gabata.

A shekarar da muke ciki, sakamakon yaduwar annobar numfashi ta COVID-19 a daukacin duniya, tattalin arzkin duniya na samun koma baya, har ma wasu kasashe sun soma bada kariyar tattalin arziki da cinikayya, ta yadda mai yiwuwa ne za a daidaita tsarin sana'o'i da na samar da kayayyaki na duniya baki daya.

A ganin Zhang Liqing, kwanan nan, sau da yawa kwamitin tsakiya ya ambaci kalmar sabon tsarin ci gaba, inda aka ba da alamar cewa, yanzu ana kokarin gaggauta mayar da hankali kan inganta bukatun cikin gida maimakon dora muhimmanci kan fitar da kaya da aka yi a da. Zhang Liqing ya ce,

"Idan an ce, yanayin annobar COVID-19 tana kawo matsala ne cikin gajeren lokaci, to mai yiwuwa sake shirya tsarin sana'o'in da ke sabawa dunkulewar tattalin arzikin duniya zai kasance a cikin dogon lokaci. A yayin da ake tinkarar wadannan kalubaloli na gajeren lokaci da na dogon lokaci, a gani na, tabbatar da sabon tsarin na dora muhimmanci kan inganta bukatun cikin gida, tare da hada kai da cinikayyar waje, wannan ba kawai ya amince da daidaituwar da aka yi a cikin shekaru 10 da suka gabata ba ne, har ma zai amfana wajen tinkarar sabon kalubale. Mayar da hankali kan inganta bukatun cikin gida, ba kawai zai taimaka wajen fuskantar matsalolin da ake fuskanta a yanzu ba ne, a sa'i guda har ma zai taimaka wajen samun sabon halin musamman na tattalin arziki wanda zai bullo bayan tattalin arziki ya bunkasa zuwa wani mataki."

Ko sabon tsarin dora muhimmanci kan inganta bukatun cikin gida da hada kai da cinikayyar waje na nufin cewa, kasar Sin zata rufe kofa wajen samun ci gaban tattalin arzikinta ne? Zhang Liqing ya bayyana cewa, ba haka batun yake ba.

"Tabbatar da daidaito tsakanin samarwa da bukatar kayayyaki ta hanyar kasuwar cikin gida kawai, wannan ba zai isa ba. Nazarin da aka yi kan manufofi da fasahohin da aka samu masu yawan gaske sun nuna cewa, bunkasuwar tattalin arziki dake dogara ga fitar da kayayyaki zuwa waje zai kara ingancin tattalin arziki. Don haka, bisa yanayin da ake ciki, la'akari da makomar bunkasuwa ta nan gaba, akwai bukatar a jaddada dora muhimmanci kan inganta bukatun cikin gida. Wato a yayin da ake amfani da karfin kasuwar cikin gida, a waje guda kuma, a bunkasa cinikayyar shigi da fici yadda ya kamata, hakan zai bada gudummawa wajen inganta bukatun cikin gida."(Bilkisu)