logo

HAUSA

Aliyu Ibrahim Usman: Ina son amfani da ilimin noma da na samu domin bautawa kasa ta Najeriya

2020-08-04 13:24:03 CRI

Aliyu Ibrahim Usman: Ina son amfani da ilimin noma da na samu domin bautawa kasa ta Najeriya

Aliyu Ibrahim Usman, dan asalin birnin Maidugurin jihar Borno daga arewa maso gabashin tarayyar Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a jami'ar koyon ilimin noma ta kasar Sin dake nan birnin Beijing. A zantawarsa da wakilin sashin Hausa na rediyon kasar Sin Murtala Zhang, malam Aliyu ya ce, Sin babbar kasa ce a fannin noma a duniya, kuma yana son amfani da ilimin da ya samu a wannan fanni domin bautawa kasar sa wato Najeriya.

Aliyu Ibrahim Usman: Ina son amfani da ilimin noma da na samu domin bautawa kasa ta Najeriya

Aliyu ya kuma kara da cewa, duk da cewa bai jima a kasar ta Sin ba, amma ya ziyarci wuraren shakatawa da na tarihi da dama, musamman a birnin Beijing, ciki har da babbar ganuwar kasar Sin, wato Great Wall a turance, da kuma lambun shan iska na sarakunan gargajiya na kasar, wato Summer Palace a turance, wadanda suka burge shi kwarai da gaske.(Murtala Zhang)